Babaji

5684 Posts

2027: Idris ya gargaɗi editoci kan labaran bogi na fasahar AI

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Mohammed Idris Malagi, ya yi kira ga editocin Nijeriya da su mayar da aikin tantancewa a matsayin jigo kuma al'ada a ɗakin yaɗa labarai, yayin da ƙasar ke fuskantar zaɓen 2027, yana mai gargaɗin cewa fasahar AI ta zama hanyar mayar da ƙarya ta zama gaskiya acikin al'umma. Mohammed Idris ya bayyana haka ne yayin jawabi a babban taron editoci na All Editors Conference (ANEC 2026) da aka gudanar a Enugu mai taken "The Ballot, the Media and Task of Keeping Democracy Alive" da kuma ƙaramin…
Read More

Ku riƙa biyan ‘yan jarida da kyau ko darajar dimukraɗiyya ta zube da labaran bogi – Shugaban INEC ga kafafen labarai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan (SAN), ya yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar darajar dimukraɗiyyar Nijeriya ta rushe muddin aka cigaba da barin labaran bogi da masu ruɗarwa ta fasahar AI suna yaɗuwa acikin al'umma, yana mai cewa wajibi ne masu kafafen yaɗa labarai su fifita walwalar 'yan jarida a harkar gudanarwa. Amupitan ya yi wannan gargaɗi ne a ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026 a taron All Nigeria Editors Conference (ANEC 2026), wanda aka gudanar a Enugu. Da yake jawabi a gaban editoci sama da guda 500, mawallafa da jagororin…
Read More

Shugaban ƙaramar hukumar Zamfara ya shaƙi iskar ‘yanci bayan kwana 61 a hannun ‘yan bindiga

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Nura Abdullahi, wanda shi ne Shugaban Ƙaramar Hukumar Bunguɗu a Jihar Zamfara, ya yi nasarar kuɓuta daga hannun 'yan bindiga bayan shafe kwanaki 61 a hannunsu. Wata majiya daga iyalansa ta ce Hon. Abdullahi ya shaƙi iskar 'yanci ne tare da wasu da aka yi garkuwa da su yayin harin. A ranar 25 ga Yuli ne aka ya awon-gaba da Abdullahi a lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai farmake shi a gidansa da ke garin Bunguɗu. An sako shi ne tare da wasu mutane, duk da cewa ba a bayyana ainihin yadda al'amarin…
Read More

Yanzu-yanzu: Kotu a Gombe ta umarci a sake zaɓen fidda gwanin PDP bayan soke takarar Pantami

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya a Jihar Gombe, ta umarci jam'iyyar PDP da ta sake gudanar da sabon zaɓen fidda gwanin ɗan takararta na gwamna a jihar. Wannan umarni ya biyo ƙorafin da Usman Aliyu Garry ya shigar wa kotun na ƙalubalantar zaman Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar a zaɓen 2027 da ke tafe. Mai Shari'a Amina Aliyu Mohammed, wadda ta yi hukuncin, ta umarci PDP ta sake shirya sabon zaɓen fidda gwani bisa sharuɗɗa da dokokin jam'iyyar. Garry ya ƙalubalanci zaman Pantami a matsayin ne bayan…
Read More

EFCC ta ayyana tsohon Shugaban fansho, Abdulrasheed Maina a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, ta ayyana tsohon shugaban tsohon Kwamitin Gyaran Fansho, Abdulrasheed Maina a matsayin wanda take nema ruwa-a-jallo bisa ragin sa da hannu a karɓar wata kadarar sata. Hakan na zuwa ne bayan shekaru da Babbar Kotun Tarayya ta same shi da laifin almundahanar kuɗaɗen da sauya akalar kuɗaɗen fansho. Saƙon EFCCn na kwanan nan ya karkata ne kan zargin karɓar wasu kadarorin sata. Jami'in hulɗa da jama'ar hukumar Dele Oyewale ya fitar da sanarwar a ranar Laraba. A ranar 25 ga Oktoba, 2019 ne aka gurfar…
Read More

Mutum huɗu sun rasu yayin da ƙasar wajen haƙo ma’adinai ta rufta a Filato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Masu aikin haƙar ma'adinai guda huɗu sun gamu da ajalinsu a lokacin da ƙasar wani wurin haƙar ma'adinai ta rufta akansu a yankin Baban Rafi da ke Ƙaramar Hukumar Ɓokkos a Jihar Filato. Al'amarin ya auku ne a ranar Talata yayin da mutanen suke tsaka da aiki a wajen. Shugaban Matasan Ɓokkos, Daniel Tula ne ya ya tabbatar da wannan labari ga gidan Talabijin na Channels a wata hirar tarho, inda ya ce mamatan sun haɗa da maza da mata biyu-biyu. A cewarsa, mutanen sun rasu ne sakamakon ruftawar wani sashe na ƙasar ramin…
Read More

Fitacciyar ‘yar jarida, Medina Dauda ta zama kakakin ABER

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An naɗa daɗaɗɗiyar ‘yar jarida, Hajiya Medina Dauda Nadabo a matsayin Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Shirin Ci-gaban Tattalin Arziƙin Albarkatun Ruwa na Afirka (ABER), wato Africa Blue Economy Roundtable. Hakan na ƙunshe ne a wata takarda mai kwanan wata 15 ga Satumba, 2026, wadda Shugaban ABER kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na Shirin Ci-gaban Harkokin Walwala (BTPDI) na BRACED, Dakta Piriye Kiyaramo ya sanya wa hannu. A cewar wasiƙar, naɗin ya ya yaba da hidimar Medina Nadabo ne a matsayinta na wadda ta shafe sama da shekaru 40 tana da ƙwarewa…
Read More

Fitacciyar ‘yar jarida, Medina Dauda ta zama kakakin ABER

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An naɗa daɗaɗɗiyar 'yar jarida, Hajiya Madina Dauda Nadabo a matsayin Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Shirin Ci-gaban Tattalin Arziƙin Albarkatun Ruwa na Afirka (ABER), wato Africa Blue Economy Roundtable. Hakan na ƙunshe ne a wata takarda mai kwanan wata 15 ga Satumba, 2026, wadda Shugaban ABER kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na Shirin Ci-gaban Harkokin Walwala (BTPDI) na BRACED, Dakta Piriye Kiyaramo ya sanya wa hannu. A cewar wasiƙar, naɗin ya ya yaba da hidimar Madina Nadabo ne a matsayinta na wadda ta shafe sama da shekaru 40 tana da ƙwarewa…
Read More

‘Ni ba shugaban riƙo ba ne’, Har yanzu Shugaba Tinubu ke mulki daga waje, inji Akpabio

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, ya bayyana cewa babu wani gurbi a Fadar Shugaban Ƙasa, inda ya tirje kan cewa har yanzu Shugaba Bola Tinubu ne yake mulkar Nijeriya duk da cewa ba ya cikin ƙasar. Akpabio ya yi wannan furuci ne a ranar Talata a Jihar Akwa-Ibom a yayin da ya yi watsi da cigaba da nuna damuwa daga wasu kan cigaba da zaman Tinubu a Turai da tafiyar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima taron Majalisar Ɗinkin Duniya. Ya ce, Shugaba Tinubu na cigaba da aiki a matsayin shugaban Nijeriya duk cewa yana…
Read More

Ma’aikatan lantarki sun yi barazanar tsunduma yajin aiki kan cin zarafi daga sojoji

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Ma'aikatan Lantarki ta Ƙasa (NUEE) a Jihar Bauchi, ta yi barazanar dakatar da ayyukan raba wutar lantarki a Nijeriya bisa zargin cin zarafin wasu mambobinta daga ɓangaren jami'an Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF). Mataimakin Shugaban NUEE, Rilwanu Shehu ne ya bayyana haka yayin wata zanga-zangar lumana da ma'aikatan suka gudanar a Bauchi, ranar Litinin, 21 ga Satumba, 2026. Ya ce, sun ɗauki matakin ne domin nuna adawarsu ga kutse da cin zarafin mambobinsu da jami'an NAF suka yi. Shehu ya bayyana cewa, a ranar 18 ga Satumba ne wasu sojoji suka afka wa…
Read More