Babaji

5684 Posts

El-Rufa’i: Kotu ta za ta yi hukuncin shari’ar zargin naɗar hirar Ribaɗu a 26 ga Oktoba

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta ayyana ranar 26 ga Oktoba, 2026 domin yanke hukunci kan buƙatar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ta cewa babu wata hujjar da za ta sa a ci gaba da shari’ar da ake yi masa. El-Rufa'i yana fuskantar shari’a ne kan zargin kutse da naɗar kiran wayar Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro (NSA), da Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS ta shigar da shi a kansu. A zaman kotun da aka yi ranar Talata, lauyoyin gwamnati da na El-Rufai sun gabatar da hujjoji kan buƙatar a sallami tsohon gwamnan…
Read More

Harin masallacin Neja: masallata uku aka halaka bayan sace 63, inji Bago

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya warware batun garkuwar kwanan nan da ta auku a wani masallacin Juma'a da ke yankin Dakera, inda ya ce mutane 63 ne 'yan bindiga suka sace yayin al'amarin. Bago ya kuma yi watsi da batun cewa mutane 500 ne aka yi awon-gaba da su, yana mai bayyana adadin a matsayin iƙirarin da aka kambama da ke yawo a Soshiyal Mediya. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da tsohon gwamnan jihar kuma Sanata mai wakiltar mazaɓar Neja ta Arewa, Abubakar Sani Bello ya ziyarce shi a Gidan…
Read More

Mutuwar ‘yan Neja 37: Zainab Okino ta Blueprint ta samu gurbi yayin da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da kwamitin bincike

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin bincike mai zaman kansa na mutum goma domin gaggauta gudanar da bincike akan ainihin dalilan da suka sabbaba mutuwar mutane 37 da ake zargin masu haƙar ma'adinai ne ba bisa doka ba a Jihar Neja. Da yake ƙaddamar da kwamitin a Abuja, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce gwamnatin tarayyar ta duƙufa wajen ganin an yi wa mamatan adalci, waɗanda suka rasu a ofishin Hukumar Sibil Difens (NSCDC) reshen Jihar Neja. An bai wa kwamitin, wanda tsohon Mataimakin Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS), Jonathan…
Read More

Kashe-kashen Filato: Gwamnatin jihar ta sanya dokar kulle a ƙananan hukumomi uku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Filato ta sanar da sanya dokar hana fita da dare a sassan ƙananan hukumomin Barikin Ladi, Ɓokkos da Mangu a sakamakon matsalolin tsaro da suka shafi wasu ƙauyukansu. Dokar, wadda ta fara daga ranar Litinin, 21 ga Satumba, 2026 ta umarci mazauna ƙananan hukumomin da su zauna a gidajensu daga tsakanin ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe har illa ma sha Allahu. Kwamishinar Yaɗa Labaran jihar, Joyce Lohya Ramnap ce ta sanar da haka a wata sanarwa, inda ta ce an ɗauki matakin ne domin bai wa jami'an tsaro damar…
Read More

Gwamna Uba Sani ya amince da biyan biliyan N3.659 ga ‘yan fansho a Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da biyan Naira biliyan 3.659 ga 'yan fansho, da sauran haƙƙoƙin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya, da kuma iyalan ma’aikatan da suka rasu a jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Malam Ahmed Maiyaƙi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce kudaden mutane 1,339 da suka cancanta a karkashin tsarin (CPS) ne Zasu amfana. Ya ce, wannan sabon kaso ya kawo adadin kudaden fanshon da gwamnatin Uba Sani ta biya tun bayan hawanta mulki a watan Mayun 2023 zuwa Naira biliyan 21.455, wadanda suka mutane 9,683 suka…
Read More

‘Yan sanda a Kano sun kama wanda ake zargi da garkuwa da satar dabbobi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan Sanda a Jihar Kano ta ce ta kama wani ɗan shekara 35 da ake zargin mai garkuwa da mutane kuma ɓarawon dabbobi ne mai suna Habibu Bello, a yayin wani atisaye a yankin iyakar Kano da Kaduna. Rahotanni sun bayyana cewa, Bello, wanda ɗan garin Kunkumi ne na Ƙaramar Hukumar Maƙarfi ta Jihar Kaduna, an kama shi ne a ranar 14 ga Satumba bayan samun wasu bayanan sirri daga tawagar yaƙi da garkuwa ta rundunar. Kakakin 'yan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da haka a wata takarda, inda…
Read More

‘Za mu garzaya Villa’, Iyayen yara 80 na Borno da ke hannun Boko Haram sun ba wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana shida ta ceto su

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Iyaye da al'ummar yankunan Mussa da Lassa na Ƙaramar Hukumar Askira-Uba ta Jihar Borno sun yi barazanar zuwa Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja nan da kwana shida muddin ba a ceto yaransu ba da suke hannun ƙungiyar Boko Haram a Arewa maso Gabas. Iyalan, waɗanda ke halin ƙunci na rashin ganin 'ya'yansu a tsawon sama da kwanaki 130, sun fitar da wannan wa'adin gargaɗi ne a ranar Litinin yayin wata zanga-zanga akan abin da suka kira da halin ko-in-kula daga ɓangaren gwamnati a Askira-Uba. An yi garkuwa da yaran ne a wani babban…
Read More

Zamfara: A Oktoba za a fara jigilar fasinjoji daga Gusau zuwa Abuja a sabon filin jiragen saman jihar – Gwamnati

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanya hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa da kamfanin XEJet Limited domin fara zirga-zirgar jiragen fasinja kai tsaye tsakanin Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau da Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. Yarjejeniyar Fahimtar Juna, wato MoU da aka sanya wa hannu ranar Litinin ta zama wani muhimmin mataki wajen inganta zirga-zirgar jama’a da kuma sauƙaƙa harkokin kasuwanci, zuba jari, yawon buɗe ido da bunƙasar tattalin arzikin Jihar Zamfara. Wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa…
Read More

‘Yan sanda sun fara bincike bayan karɓe iko da ofishin NSCDC da masu haƙar ma’adinai 37 suka rasu a ciki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan sanda a Jihar Neja, ta karɓe iko da gurin da masu gargajiyar haƙar ma’adinai suka rasu a ofishin Hukumar Sibil Difens NSCDC da kuma fara bincike akan al'amarin. Wannan ya biyo bayan umarnin Sufeto-Janar na rundunar, Olatunji Disu na ta bankaɗo ainihin dalilan da suka sabbaba mutuwarsu da tabbatar da gaskiya da adalci tare da martaba 'yancin dokar ƙasa ga mamatan. A wata sanarwa da rundunar 'yan sandan Neja ta fitar a ranar Litinin, Kwamishinanta, CP Adamu Elleman ya umarci tawagogin sintiri na Operation Flush da su killace tare da kula da…
Read More

Tinubu zai dawo Nijeriya a ƙarshen mako bayan tsawaita hutunsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai dawo Nijeriya a ƙarshen makon nan bayan ƙarin wa'adin hutunsa da 'yan kwanaki. A ranar 30 ga watan Agusta ne Tinubu ya bar Nijeriya zuwa Landon domin fara hutunsa na shekara, inda daga bisani ya garzaya Paris a ƙasar Faransa ya cigaba da harkokinsa yayin da kuma yake shiga lamuran gida Nijeriya daga can. Kakakinsa Bayo Onanuga ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 21 ga Satumba, 2026. Bayan shafe mako guda a Landon, Tinubu ya je Paris inda ya gana da…
Read More