Babaji

5684 Posts

An ɗage ƙarar El-Rufa’i ta diyyar biliyan N1 zuwa 27 ga Oktoba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin Babbar Kotun Tarayya ta ɗaga sauraron ƙarar neman biyan diyyar Naira biliyan 1 da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya shigar akan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da wasu zuwa ranar 27 ga Oktoba. Sauran waɗanda tsohon gwamnan ya shigar ƙara tare da ICPC sune Sufeto-Janar na Rundunar 'Yan sanda (IGP) da Antoni-Janar na Ƙasa (AGF) a matsayin ɓangare na biyu da na uku. Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ce ta ɗage shari’ar domin bai wa lauyan da ke kare tsohon gwamnan, Akinyemi Aremu damar bayar da amsa…
Read More

Abin da ya sa Shettima ke wakiltar Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81 – Ministan Labarai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Mohammed Idris Malagi, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilce shi ne a taron Majalisar Ɗinkin Duniya saboda yana halin hutun shekara. Mohammed Idris ya ce, Shettima ya ɗauki cikakken umarnin Shugaban da Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya wajen wakiltar ƙasar a babban taron karo na 81, yana mai watsi da batun cewa rashin ganin shugaban ƙasar a taron ka iya rage ƙarfin martabar Nijeriya a harkokin difulomasiyya. Wannan bayani na zuwa ne bayan da Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar…
Read More

Ladanin Masallacin haramin Makkah, Ibrahim Al-Madani ya rasu a shekara 51

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sheikh Ibrahim bin Adel Al Madani, ladani a Masallacin Haramin Makkah ya rasu a safiyar ranar Litinin bayan shafe shekaru 51 a duniya. Tashar Al-Ekhbariya ta Saudiyya ce ta tabbatar da labarin, wanda ya janyo alhini da miƙa saƙon ta'aziyya a kafafen sada zumunta. Al Madani ɗaya ne daga cikin manyan ladanan babban masallacin na Makkah guda 24. Guda shida daga cikinsu na aikin kiran salla a kowace rana yayin sallolin farilla biyar. Marigayin ya shahara ne da kiran sallar asubahi da kuma rera kabbarbarin Idi. Haka kuma, aikinsa ya haɗa da tabligh, wato…
Read More

Gwamnatin Zamfara ta amince da ƙarin kaso 95 na albashin ma’aikatan lafiya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da ƙarin kashi 95 na albashin ma'aikatan lafiya a sassan jihar, inda aka tsara sabon matakin ya fara aiki daga ranar 7 ga Satumba, 2026. Gwamnatin ta ce, wannan sabon tsarin ya yi daidai da amincewar Gwamnatin Tarayya akan tsare-tsaren albashin fannin lafiya, musamman kan Tsarin Ƙarfafa Albashin Fannin Lafiya (CONHESS). Shugaban Ma'aikatan jihar, Shehu Baraya ne ya sanar da haka a wata wasiƙa mai ɗauke kwanan wata 10 ga Satumba, 2026. An gabatar da ita ne kai-tsaye ga manyan jami'an gwamnati, ciki har da Sakataren Gwamnatin jihar, masu…
Read More

NiMet ta yi hasashen mamakon ruwa daga Litinin zuwa Laraba a sassan Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da Yanayi ta Ƙasa NiMet, ta fitar da hasashen samun mamakon ruwan sama da tsawa a sassa da dama na faɗin Nijeriya daga Litinin zuwa Laraba, tana mai gargaɗin samun iska mai ƙarfi gabanin tsawa a wasu yankuna. NiMet ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi a Abuja, inda ta shawarci mazauna yankunan da ta zayyano da su ɗauki matakan kariya yayin da ake tsammanin matakai daban-daban na ruwan sama a sassan ƙasar. A ranar Litinin, hukumar ta ce akwai yiwuwar samun tsawa da matsakaicin ruwan…
Read More

Shettima ya isa New York don halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya isa birnin New York ta ƙasar Amurka domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu da jagorantar tawagar Nijeriyar a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 UNGA. An bayyana haka ne a wata sanarwa da aka fitar a yau Litinin, inda mataimakin shugaban ƙasar yake cewa hada-hadar Nijeriya a taron za su fi karkata ne ga maslahar ƙasar, ƙoƙarin warware muhimman batutuwan difulomasiyya, da kuma kiran Shugaba Tinubu na a samar da gyare-gyare ga cibiyoyin duniya domin dacewa da halin tattalin arziƙi da yanayin ƙasashe. Shettima ya jagoranci tawagar ne,…
Read More

Bago ya buƙaci gwamnati ta kafa dokar haramta haƙar ma’adinai a wurare masu haɗari yayin da NSCDC ta gurfanar da jami’ai kan mutuwar mutane 37

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago ya yi kira da a samar da doka daga Fadar Shugaban Ƙasa ko Ma'aikatar Ci-gaban Albarkatun Ƙasa ta Tarayya da za ta haramta ayyukan haƙar ma'adinai a yankunan da ake da damuwa akansu a jihar, yayin da a ranar Lahadi Hukumar Sibil Difens (NSCDC) ta gurfanar da dakataccen daraktanta na Neja, Suberu Aniviye da sauran jami’an da suke da alaƙa da mutuwar waɗanda ake zargi da ayyukan haƙar ma'adinai ba bisa doka ba su 37 a ofishin NSCDC. Bago ya yi wannan kira ne a wata hira da gidan…
Read More

An kama mai POS, dilan kayan babur da wasu biyu kan zargin alaƙar kuɗi da jagoran ‘yan bindiga a Katsina

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani mai sana'ar POS da dillalin kayan babur mai suna Isiyaku Nasiru a Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina sun shiga hannun hukuma bisa zargin su da hannu a taimaka wa jagoran 'yan bindiga, Kachalla Muhammadu wajen hada-hadar miliyoyin nairori. Hukumar Tsaro ta Katsina State Watch Corps ne ta kama Nasiru tare da wasu mutane uku: Abubakar Sayaya, Nura Baka Sati da Ubale Mai Cange. An kama su a wurare mabambanta a jihar a tsakanin ranakun Alhamis da Asabar. Shugaban ƙaramar hukumar Matazu, Shamsuddeen Muhammad Sayaya, wanda ya tabbatar wa manema labarai kamen, ya…
Read More

JADDAWALI: Sunayen masu haƙo ma’adinai ba bisa doka ba 37 da suka rasu a ofishin Sibil Difens na Neja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An bayyana sunayen masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba guda 37 da suka rasu a ofishin Hukumar Sibil Difens (NSCDC) na Jihar Neja a makon da ya gabata. Mamatan suna daga cikin waɗanda aka kama a wani atisaye da jami'an NSCDC na jihar suka ƙaddamar a ranakun 15 da 16 ga Satumba a yankin Rukunin Gidajen Laftanal Janar Mohammed Inuwa Wushishi da ke Minna, babban birnin Neja. Dakataccen Kwamandan NSCDC a jihar, Suberu Aniviye a wata sanarwa, ya ce an samu da dama daga cikin waɗanda kama sun rasu a safiyar ranar Alhamis…
Read More

Ba gaskiya ba ne cewa ni ne mamallakin wajen haƙar ma’adinan matasan Neja 37, inji IBB

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon shugaban mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida ya musanta iƙirarin cewa ya mallaka ko yana da hannu a wani gurin haƙar ma'adinai a Jihar Neja, inda aka kama wasu matasa 37 da ake zargin su da yin aikin haƙo ma'adinai ba bisa doka ba da daga bisani suka rasu a komar hukumar Sibil Difens (NSCDC). Babangida, wanda aka fi sani da IBB, ya bayyana wannan zargin a matsayin ƙarya mara asali da ba shi da makama, kamar yadda wakilinsa, Dakta Ɗanladi Umar Abdulhameed ya bayyana. Wannan na zuwa ne bayan iƙirarin da wani wanda…
Read More