Babaji

5684 Posts

APC ta lashe zaɓen cike gurbin majalisar dokokin Kano bayan ƙauracewar manyan jam’iyyun adawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da Hussain Yusuf Datti na Jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbin mazaɓar Dawakin Kudu ta Jihar Kano. Bature zaɓen, Farfesa Ibrahim Tajo-Suraj ne ya bayyana haka a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu. Ya ce, Yuzuf Datti ya yi nasarar ne sakamakon samun ƙuri'a 22,890, wanda ya ba shi damar doke Habib Hamisu na Peoples Redemption Party (PRP) da ya samu ƙuri'a 270. Haka kuma, ya ce Abdullahi Adamu na Peoples Democratic Party (PDP), ya samu ƙuri'a 108, yayin da Bala Mohammed-Sani…
Read More

Tinubu ya umarci Shettima ya wakilci Nijeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima umarnin jagorantar tawagar Nijeriya domin wakiltar sa a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da za a gudanar a New York, ƙasar Amurka. Kakakin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi. A cewarsa, Shettima zai jagoranci tawagar ne, wadda ta haɗa da Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara; Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal; ministoci da wasu manyan jami'an gwamnati. Za a gudanar da taron a ranakun 22 zuwa 28 ga…
Read More

Mutuwar matasan Neja: ‘Yan sanda sun rufe sabuwar hedikwatar Sibil Difens yayin da sabon kwamanda ya kama aiki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan sanda a Jihar Neja ta sanar da rufe sabon ofishin Hukumar Sibil Difens (NSCDC) na Jihar Neja domin fara bincike kan abin alhinin mutuwar masu haƙar ma'adinai a ofishin a ranar 17 ga Satumba, 2026. Kakakin rundunar, SP Wasiu Abiodun ne ya tabbatar da haka a wata sanrwa da ya aike wa Blueprint.ng a ranar Lahadi, inda ya ce hakan wani ɓangare ne na biyayya ga umarnin Sufeto-Janar na rundunar, Olatunji Rilwan Disu. Ya ce, an aiwatar da hukuncin ne a lokacin da Kwamishinan 'yan sandan, Adamu Abdullahi Elleman, ya umarci a…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Ibrahim Idris ya rasu a Birtaniya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris, ya rasu bayan shafe shekaru 77 a duniya. Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi, 20 ga Satumba, 2026 a wani asibitin Birtaniya, kamar yadda Blueprint.ng ta ruwaito. Saidai ba a samu cikakken bayani ba kan yadda al'amarin ya kasance, duk da wasu majiyoyin iyalansa sun ya yi fama jinya mai tsanani gabanin rasuwarsa. Gwamna Usman Ododo na jihar mai ci a yanzu ya miƙa saƙonsa na ta'aziyya ga iyalan tsohon gwamnan. Ya bayyana shi a matsayin ɗan siyasar da ya bayar da gudummawa masu amfani a…
Read More

Sanata Barau ya sallami mataimaki kan wallafa “Abba Must Go” yayin da APC da Kwankwaso ke fafutukar nasara a Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya kori mai taimaka masa na musamman kan harkokin majalisa, Umar Alhassan da aka fi sani da King Indara sakamakon wallafe-wallafe akan Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano. Wannan mataki ya fara aiki ne a ranar Juma'a, 18 ga Satumba, 2026, a cewar wata sanarwa da jami'in yaɗa labaran Sanata Barau, Shitu Madaki Ƙunchi ya fitar. Sanatan ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bisa abin da ya kira da "rashin girmamawa" daga mataimakinsa a Soshiyal Mediya. Musamman sanarwar ta kawo misali da wallafar Indara ta…
Read More

NDC ta yi watsi da mutum 59 ta OK Movement, ta gargaɗi ƙungiyoyin goyon bayanta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar NDC ta nesanta kanta daga kwamitin yaƙin neman zaɓenta mai mambobi 59 da Tafiyar Obi-Kwankwaso da aka fi sani da OK Movement ta sanar da kafawa yayin tunkarar zaɓen 2027. NDC ta yi gargaɗin cewa babu wani mutum, ɗan takara ko ƙungiyar goyon baya da ta amince wa kafa wata tawagar yaƙin neman zaɓe ko amfani da sunanta ba tare da sahalewar Kwamitin Gudanarwarta ta Ƙasa (NWC) ba. Shugaban jam'iyyar na Ƙasa, Sanata Moses Cleopas ne ya bayyana haka a wata takarda a ranar Asabar, bayan Darakta-Janar na tafiyar, John Ughulu ya gabatar…
Read More

Wasan neman shiga AFCON: Osimhen ba zai samu buga wa Super Eagles ba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan wasan gaba na Super Eagles Victor Osimhen ba zai samu damar wakiltar Nijeriya ba a wani ɓangare na wasannin neman gurbin shiga gasar Kofin Ƙasashen Afirka (AFCON) na 2027 sakamakon fama da raunin ƙwanji. Sashen yaɗa labaran Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF) ne ya tabbatar da wannan labari a ranar Asabar cikin wata sanarwa, inda ya ce ɗan wasan na ƙungiyar Galatasaray na fama da jinkirin warkewa, inda hakan ke nufin ba zai kasance cikin tawagar Nijeriyar ba. Da fari an sanya sunan ɗan wasan cikin jerin 'yan wasan da za su…
Read More

Uku sun rasu yayin da 5 suka jikkata a sabon harin kasuwar Filato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mutane uku aka halaka da raunata wasu biyar bayan wasu 'yan bindiga sun buɗe wa jama'a wuta a kasuwar 'Yan Gwari da ke Ƙaramar Hukumar Mangu a Jihar Filato. Al'amarin, wanda ya auku a ranar Juma'a, ya haifar da fargaba kan halin tsaro a Mangu da wasu sassan Jihar Filato, inda aka samu munanan hare-hare a makonnin da suka gabata. Waɗanda suka rasu a harin sune Nanker Andrew, Delshak Jacob da kuma Jessica Thomas. Sun rasa rayukansu ne a wajen da al'amarin ya faru. Sai kuma Polina Colis, Gloria Fwanshak, Sekyen Lonkat da Bamrat…
Read More

Direba ya kuɓuta bayan biyan miliyan N2 yayin da ‘yan bindiga suka buƙaci fansar N30m ga limaman Zamfara shida

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'Yan bindigar da suka yi awon-gaba da malamai guda shida a Jihar Zamfara sun buƙaci a biya su Naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa domin sako su. Rahotanni sun bayyana cewa, wani mai suna Malam Muhammad Ibrahim a ƙauyen Dakka na Ƙaramar Hukumar Bakura, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust wannan ci-gaba ta wayar tarho. Saidai ya ce direban da aka sace tare da limaman ya shaƙi iskar 'yanci bayan biyan 'yan bindigar Naira miliyan 2. Ya ce, "Yan bindigar sun sace jimillar mutum takwas ne - limamai biyar, direbansu da wasu mutane…
Read More

An zargi wata mata da halaka mijinta kan shirin ƙara aure a Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An kama wata mata, Bilkisu Sani a Ƙaramar Hukumar Rogo da ke Jihar Kano kan zargin ta da halaka mijinta mai suna Hafizu Gausu, wanda aka ce yana shirin ƙara aure. Auwal Kazagi, wanda mazaunin yankin ne, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa al'amarin ya auku ne a ranar Juma'a da misalin ƙarfe 7 na yamma a unguwar Katsalle na cikin garin Rogo. Ya ce, mazauna sun hanzarta zuwa gurin domin gane da idanunsu bayan jiyo kuka daga matar Gausu, wadda ta yi iƙirarin cewa an yanka mijinta. "A lokacin da muka isa…
Read More