19
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An samu gawar wata malamar jami'a mai suna Ayodele Odularu, wadda ke karantarwa a Jami'ar Fort Hare da ke Afirka ta Kudu a gidanta na Estern Cape Province a ƙasar. Rahotanni sun bayyana cewa, Odularu ta rasu ne a ranar 16 ga Agusta bayan shafe shekaru 51 a duniya, kamar yadda ɗan uwanta Gbadebo Odularu ya shaida wa manema labarai a ranar Asabar. Ya ce, suna tunanin mutuwarta tana da alaƙa da wani ɓoyayyen al'amarin, musamman ganin yadda ba su gano ainihin yadda ajalin nata ya riske ta ba. Akan haka ne iyalanta suke…
