18
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su kasance wayayyu yayin nazari kan siyan hannayen jarin kamfanin Matatar Ɗangote na IPOs, yana mai gargaɗin su da kada su siyar da gidajensu ko amfani da kuɗaɗen karatun 'ya'yansu wajen siyan hannun jari. Mai Martabar ya yi wannan kira ne a taron wayar da kan jama'a kan hannun jarin FZE IPO na Kamfanin Matatar Ɗangote da dangogin fetur a Jihar Kano, wanda ya tara masu zuba jari, abokan hulɗa, wakilan bankuna, jagororin masana'antu, sarakunan gargajiya da sababbin masu zuba jari.…
