Babaji

5684 Posts

Adadin waɗanda suka rasu sakamakon gubar giya ya kai 49 yayin da aka samu 170 a Ondo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar shan wata giya da aka yi zargin an sanya wa guba a wasu ƙauyukan Jihar Ondo ya ƙaru zuwa 49 yayin da aka samu rahoton mutum 170 da al'amarin ya shafa. A ranar 5 ga Satumba, 2026 ne aka fara samun rahoton al'amarin a garin Odigbo da Araromi Obu da ke Ƙaramar Hukumar Odigbo bayan mazauna yankunan sun sha wata giyar gargajiya. An ruwaito cewa wasu daga cikin mutanen da suka sha giyar suna tsinci kansu a halin rashin sanin inda suke gabanin su rasu a…
Read More

Ofishin jakadanci ya gargaɗi mata a Afirka ta Kudu bayan mutuwar mace takwas

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ofishin jakadancin Nijeriya a birnin Johannesburg ya aike da saƙon kira ga aminci ga 'yan Nijeriya da ke zama a yankin Kempton Park da kewayen Ekurhuleni, bayan mutuwar wasu mata guda takwas da ofishin ya ce rundunar 'yan sandan Afirka ta Kudu (SAPS) tana bincike a kai. Rahotanni sun bayyana cewa, Ofishin a sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, 16 ga Satumba, 2026, ya ce mace-macen sun faru ne kusan watanni biyu da suka gabata kuma hakan ya sa aka gaggauta kafa kwamitin bincike da ya haɗa jami'an hukumomin tsaro daban-daban. A cewar…
Read More

Rundunar ‘yan sanda ta ƙarfafa matakan tsaro don ziyarar Shettima zuwa Adamawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ke shirin zuwa gaisuwar ta'aziyyar ga iyalan marigayi Bamanga Tukur, Rundunar 'Yan sanda a Jihar Adamawa ta tura jami'ai na musamman domin daƙile tarzoma da tankokin yaƙi zuwa wasu yankuna a Yola, Babban Birnin jihar. Rahotanni sun bayyana cewa rundunar ta ɗauki wannan mataki ne bisa ziyarar da mataimakin shugaban ƙasar zai kai zuwa jihar a hukumance. A wata sanarwa da SP Suleiman Nguroje, wato kakakin rundunar ya fitar a ranar Alhamis, ya ce 'yan sandan sun ɗauki matakan ne a sassan Yola da wasu wurare a…
Read More

NLC ta koka kan hauhawar farashin fetur a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa NLC, ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta amincewa da tallafin gaggawa a matsayin matakin rage raɗaɗi ga ma'aikata a faɗin Nijeriya da raba ɗanyen mai ga matatun gida a farashin naira domin daƙile tasirin hauhawar farashin dangogin fetur a ƙasar. Haka kuma, cibiyar ƙwadagon ta kuma kirayi gwamnatin da ta faɗaɗa girman rumbunan ajiya na ƙasa domin buƙatar agajin gaggawa da ƙarfafa tsaron makamashi. A wata sanarwa da Shugaban NLC, Joe Ajaero ya fitar, ya yi gargaɗin cewa hauhawar farashin fetur ka iya haifar da ƙamarin…
Read More

2027: Kotu ta umarci a aike wa Tinubu ƙarar Atiku ta neman soke cancantarsa ta shiga takara a hukumance

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci a aike wa Shugaba Bola Tinubu ƙarar da ke neman haramta masa shiga takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 acikin mako guda bisa zarge-zargen cewa ya miƙa wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC takardun shaida na bogi. Mai Shari'a Inyang Ekwo yayin wani hukunci, ya amince da isar da saƙon shari'a ga Shugaba Tinubu ta hannun jam'iyyarsa ta APC. Alƙalin ya bayar da wannan izinin ne bayan sauraren ƙarar da lauyan Atiku, Mista Olanrewaju Omotsyo-OJo ya shigar bayan wakiltar Mista Silas Onu da aka…
Read More

2027: Fadar Shugaban Ƙasa ta buƙaci Obi ya janye daga takara kan iƙirarin bashin Anambara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fadar Shugaban Ƙasa ta magantu a game da rikicin da ke gudana tsakanin tsohon gwamnan Jihar Anambara kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi da kuma gwamnatin jihar bisa bashi da wasu nauye-nauyen da ke kan jihar. Mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu, Bayo Onanuga a wani saƙo ta kafar X a ranar Laraba, ya ce Obi ya yi iƙirarin barin shugabancin jihar Anambara ba tare da wani bashi ba, amma ya yi barazanar cewa zai janye tsaya wa takarar shugaban ƙasa muddin aka tabbatar da wannan iƙirari ba haka…
Read More

Gwamnan Zamfara zai halarci babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya a New York

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal zai halarci babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya a New York, inda zai gana da shugabannin duniya, abokan hulɗa da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin jawo zuba jari zuwa Jihar Zamfara. Zaman Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 na da taken, “Maido da Amincewa, Gudanar da Sauye-sauye: Majalisar Ɗinkin Duniya Mai Aiwatar da Ayyukanta Ga Kowa.” Sanarwar ta fito ne daga Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, a ranar 16 ga Satumba, 2026. Manyan tarukan Majalisar Ɗinkin Duniya za su mayar da hankali kan Manufofin Ci Gaba Mai Ɗorewa (SDGs), yaƙi da…
Read More

Daɗaɗɗen jarumin Nollywood, Olu Jacobs ya rasu a shekara 84

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Oludotun Baiyewu Jacobs, wato daɗaɗɗen jarumin nan na masana'antar shirya finafinan Nollywood da aka fi sani da Olu Jacobs ya rasu bayan shafe shekaru 84 a duniya. Ɗansa, Olusoji Jacobs ne ya sanar da labarin a yau Laraba, 16 ga Satumba, 2026. Olusoji ya sanar rasuwar mahaifin nasa ne a wani saƙo da ya wallafa ta kafar Instagram, inda ya ce iyalansa na godiya bisa tsawon ransa da kuma roƙon al'umma da su girmama sirrinsu a wannan lokaci. Olu Jacobs dai ɗaya ne daga cikin shahararrun jaruman finafinan Nijeriya wanda ya shafe tsawon lokaci…
Read More

NNPCL ya sake ƙara farashin fetur

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL, ya sake ƙara farashin litar fetur a gidajen mansa da ke Abuja da kewayenta. Ƙarin na kwanan nan ya yi sanadiyyar komawar farashin zuwa Naira 1,430 ga kowace lita, lamarin da ya ƙara shigar da matsin kuɗi kan masu ababen hawa da sauran kwastomomi da ke cigaba da jure wa hauhawar farashin fetur. Gidajen mai da dama a Birnin Tarayya Abuja sun nuna cewa yanzu farashin litar ya koma tsakanin N1395 da N1,430. Sababbin farashin na wakiltar ƙarin N50 zuwa N80, bisa la'akari da gurin da gidan…
Read More

Ranar 30 ga Satumba za a fara horar da ‘yan rukunin C na 2026 – NYSC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da ɗalibai masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), ta sanar da ranar 30 ga watan Satumba a matsayin lokacin da za a fara horar da 'yan rukunin C na 2026. A wata takarda da Daraktar hulɗa da jama'arta, Caroline Embu ta fitar a ranar Talata, hukumar ta sanar da al'umma musamman ɗaliban rukunin C ɗibar farko cewa za a fara aikin horar da su ne a ranar 30 ga Satumba, sannan a kammala a ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026. Ta kuma ce, yayin da aka fara rajistar 'yan rukunin a ranar…
Read More