15
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Nijeriya bayan wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron jagororin ƙasashen BRICS da aka gudanar a birnin New Delhi na ƙasar Indiya. A yayin ziyarar, Shettima ya shiga sahun tattaunawa da wakilan ƙasashe daban-daban kan muhimman batutuwan da suka shafi ci-gaba da nufin faɗaɗa damarmakin ci-gaban tattalin arziƙin Nijeriya da janyo ra’ayoyin ƙasashe a harkar difulomasiyya. Kakakin mataimakin shugaban ƙasar, Stanley Nkwocha ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. Ya ce, daga cikin hada-hadar da aka dama da Shettima akwai ganawarsa…
