Babaji

5684 Posts

Gwamnan Adamawa ya ayyana makokin kwana uku kan rasuwar Bamanga Tukur

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa, ya ayyana makokin kwanaki uku a jihar bayan rasuwar Alhaji Bamanga Tukur, wato ɗaya daga cikin manyan ƙasa kuma ɗan asalin Jihar Adamawa. Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar, 12 ga Satumba, 2026 bayan fama da wani rashin lafiya na tsawon lokaci. Gwamnan ya yi wannan sanarwa ne a wata takarda da Sakataren yaɗa labaransa. Humwashi Wonosikou ya sanya wa hannu a Yola, babban birnin jihar. Fintiri ya kuma miƙa gaisuwar ta'aziyyarsa ga iyalan, abokan siyasa, abokan arziƙi, masu fatan alheri da ɗaukacin al'ummar Adamawa a madadin…
Read More

Nasarawa: Ma’aikatar noma ta buƙaci Sasakawa Africa ta inganta bincike don wadatar abinci

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Ma’aikatar Noma da Tsaron abinci ta Jihar Nasarawa ta tarbi tawagar Ƙangiyar Sasakawa Africa Association (SAA) yayin ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Lafia babban birnin jihar inda aka tattauna kan yadda za a hanzarta sauya tsarin abinci a jihar da qasa bakidaya. Dayake jawabi a madadin darakta na SAA a Najeriya Dr. Godwin Atser mai kula da harkokin tsarin noma da kuma wanda ke kula da fannin juriya ga canjin yanayi da Abinci wato Mista Nathaniel Otene sun yi kira ga gwamnati da ta kara zuba jari a fannonin binciken noma da fadakarwa…
Read More

Zamfara: Rundunar sojoji ta musanta sace malamai a gidan Yari

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar Sojojin Nijeriya ta yi watsi da rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da wani ayarin malamai a gidan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara da ke jihar. Saidai, ta tabbatar da rahoton awon-gaba da wasu mutane da ke tafiya daga yankin dajin Sububu a Ƙaramar Hukumar Bakura zuwa Talata Mafara. A wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na riƙo na Sashi na 2 na dakarun Atisayen FANSAR YAMMA, Laftanal Kanal Olaniyi Osoba ya fitar a ranar Lahadi, rundunar ta bayyana rahotannin da ake danganta…
Read More

INEC ta tabbatar da Dakta Nafi’u Sankara a matsayin ɗan takarar sanatan Kano ta Tsakiya a PDP

Jam’iyyar PDP Reshen Jihar Kano, ta sanar da cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da sunan Dakta Nafi’u Sankara a matsayin ɗan takarar da jam’iyyar ta tsayar na kujerar sanata mai wakiltar Mazaɓar Kano ta Tsakiya. A sanarwar da Sakataren yaɗa labaranta ya fitar a ranar Asabar, ya ce an sunansa cikin jerin sunayen ’yan takara na ƙarshe da INEC ta wallafa a hukumance, wanda hakan ya sake tabbatar da matsayinsa a matsayin ɗan takarar Jam’iyyar PDP na Kano ta Tsakiya a zaɓen da ke tafe. Reshen Jam’iyyar PDP na Jihar Kano na maraba da…
Read More

Gwamnatin Filato ta umarci a buɗe makarantu a gobe Litinin duk da fargabar annobar mashaƙo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Filato ta umarci a sake buɗe baki ɗaya makarantun firamare da sakandare na gwamnati a sassan jihar daga Litinin, 14 ga Satumba, 2026, bayan aiwatar da matakan kariya na daƙile cigaba da yaɗuwar cutar mashaƙo da ta ɓarke a wasu ƙananan hukumomin jihar. Ta ce, hakan na da nufin daidaita buƙatar bayar da kariya ga ɗalibai, malamai da sauran ma'aikatan makarantu tare da buƙatar tabbatar da cigaba da gudanar da harkokin karatu. Hakan na zuwa ne bayan rufe makarantun na wucin-gadi a 'yan kwanakin da suka gabata domin samun damar daƙile yaɗuwar…
Read More

Kakaki Abbas ya buƙaci a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki kan masu safarar ƙwayoyi da kulawa da ‘yan ƙwaya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, ya yi kira da a riƙa ɗaukar matakai masu tsauri akan masu safarar miyagun ƙwayoyi da ƙara matakin bayar da tallafi ga waɗanda suke fama da matsalolin shaye-shaye, yana mai cewa yawan amfani da miyagun ƙwayoyi na barazana ga zaman lafiyar al'umma. Wajibi ne mu hukunta waɗanda suke ribata daga ƙwayoyi. Wajibi ne mu yi magani ga waɗanda suka zama 'yan ƙwaya. Dilan yana buƙatar doka. Wanda ya dogara kuma yana buƙatar kulawa," inji Abbas. Ya kuma ce, yayin da akwai gwamnati, dole a samu doka tana aiki tare…
Read More

Gwamnonin Arewa sun yi jimamin rasuwar Bamanga Tukur

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewacin Nijeriya (NNGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, CON, ya bayyana kaɗuwarsa kan rasuwar ɗaya daga cikin manyan ƙasa, tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola kuma tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP, Alhaji Bamanga Tukur (Tafidan Adamawa). Marigayi Bamanga Tukur ya rasu ne a Abuja a ranar Asabar, 12 ga Satumba, 2026, kamar yadda rahotanni suka bayyana. A wani saƙon ta'aziyya da ya fitar a madadin takwarorinsa na NNGF, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana rasuwar tsohon dattijon ƙasar a matsayin babban rashi ga arewacin Nijeriya da ma ƙasar baki ɗaya. Ya ce, Nijeriya…
Read More

JADDAWALI: INEC ta tantance Tinubu, Atiku, Obi, Sowore da wasu 14 a matsayin ‘yan takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta wallafa cikakken jaddawalin ƙarshe na 'yan takarar shugaban ƙasa da abokan tafiyarsu domin shiga babban zaɓen 2027. Manhaja ta ruwaito cewa, jaddawalin ya ƙunshi 'yan takarar shugaban ƙasa guda 18 da kuma abokan tafiyarsi daga jam'iyyun siyasa da dama, wadda Sakatariyar INEC Rose Oriaran Anthony ta sanya wa hannu. A cikin jaddawalin akwai Shugaba Bola Ahmed Tinubu na All Progressives Congress (APC), tsohon Maitaimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar na African Democratic Congress (ADC), tsohon Gwamnan Jihar Anambara Peter Obi na Nigeria Democratic Congress (NDC), Gwamnan…
Read More

Sojoji sun fara bincike bayan zargin babban jami’i da cin zarafin kurma maras galihu a Taraba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An zargi wani babban jami'in soja mai suna Kyaftin Etim Essien da cin zarafin wata maras galihu a Jihar Taraba, inda rundunar soji ta ƙaddamar da bincike kan al'amarin. Yarinyar mai shekaru 13, wadda kurma ce da ba ta magana, an zargi jami'in da yin lalata da ita a lokuta da dama a lokacin da take ƙarƙashin kulawar iyalansa. Akan haka ne Ma'aikatar kula da Harkokin Mata da Ci-gaban Yara da Hukumar kula da 'Yancin Ɗan-adam ta Ƙasa (NHRC) suka fara bincike, inda suka buƙaci Rundunar Sojin Nijeriya ta ɗauki ladabtarwa akan jami'in. A…
Read More

Ƙyamar baƙi: An halaka ƙarin ‘yan Nijeriya biyu a Afirka ta Kudu yayin da Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An halaka 'yan Nijeriya biyu, Bishop Michael Taiwo Fakunle da James Uchechukwu Nwankwo a wurare mabambanta a ƙasar Afirka ta Kudu yayin sabunta hare-haren ƙyamar baƙi da ake zargin jami'an tilasta biyayya ga doka ne suke assasawa akan 'yan Nijeriya da 'yan wasu ƙasashen Afirka a ƙasar. Gwamnatin Tarayya ta Ma'aikatar Harkokin Waje, ta yi tir da waɗannan mace-mace na kwanan nan da kira ga mahukuntan Afirka ta Kudu da su gudanar da bincike mai zurfi da tabbatar da adalci wajen gano waɗanda suke da hannu a ciki da tabbatar da cewa sun fuskanci…
Read More