12
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon shugaban jam'iyyar PDP na Ƙasa kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a Jamhuriya ta Uku, Bamanga Tukur ya rasu bayan shafe shekaru 90 a duniya. Majiyoyin iyalansa ne suka tabbatar da rasuwarsa a ranar Asabar, duk cewa ba a bayar da cikakken bayanin kan al'amarin ba a nan take ga al'umma. Marigayin, wanda aka haife shi a ranar 15 ga Satumban 1935, ɗan siyasa ne kuma jami'in gudanarwa wanda ya riƙe muƙamin gwamna a tsohuwar Jihar Gongola, wato wadda ta haɗa jihohin Adamawa da Taraba a yau, a lokacin Jamhuriyar Nijeriya ta Biyu.…
