Babaji

5684 Posts

2027: Tinubu da APC sun buƙaci kotu ta yi watsi da ƙarar Atiku ta zargin takardar bogi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar APC da Shugaba Bola Tinubu sun yi kira ga Babbar Kotun Tarayya da ta yi watsi da baki ɗaya ƙorafe-ƙorafen da ƙarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya shigar akan Shugaban Ƙasar ta ƙunsa. Kamfanin Dillancin Labarai NAN, ya ruwaito cewa, Atiku ya shigar da Shugaba Tinubu, APC da Hukumar Zaɓeta ƙasa (INEC) ƙara bisa zargin shugaban da gabatar da takardar shaidar kammala hidimar ƙasa ta NYSC ta bogi. Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne, ya nemi kotu ta bayar da izinin soke cancantar Tinubu da jam'iyyar APC…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta tura ƙudirin dokar daina ɗaukar yunƙurin kisan kai a matsayin babban laifi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta fara shirin soke dokar ayyana yunƙurin kisan kai a matsayin babban laifi a Nijeriya bayan amincewar da Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta yi da matsayar Ma'aikatar Lafiya da Walwalar ta Tarayya akan al'amarin. Ƙaramin Ministan Ma'aikatar Lafiya, Dakta Iziaq Salako ne ya bayyana haka a Abuja a ranar Alhamis, yayin bikin Ranar Bayar da Kariya ga Kisan kai ta Duniya ta 2026, wadda aka yi wa taken "Changing the Narrative on Suicide". Dakta Salako ya ce yanzu an miƙa batun ga Majalisar Dokokin Ƙasa domin gudanar da aikin doka a…
Read More

AAC ta buƙaci a yi bincike bayan tir da kisan Ɗan Shagamu a Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar African Action Congress (AAC) ta yi alla-wadai da mummunan kisan da aka yi wa Ibrahim Khalil Ɗan Shagamu, wato ɗan Soshiyal Mediya kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa da gwamnati, wanda rasuwarsa ta zo ƙarshe a gidansa da ke Gaida a Ƙaramar Hukumar Kumbotso da ke Jihar Kano. Abokin tafiyar ɗan takara shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC, Haruna Garba Magashi ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis a Kano. A cewarsa, wannan al'amari abin firgitarwa ne kuma mai raɗaɗi ga makusanta da al'umma, wanda gabanin haka ya koka kan barazana…
Read More

Shettima ya wakilci Tinubu a taron ƙasashen BRICS na 18 a Indiya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya nufi zuwa birnin New Delhi da ke ƙasar Indiya domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron jagororin ƙasashen BRICS karo na 18, inda zai nemi a ƙarfafa alaƙar tattali da difulomasiyya da muhimman ƙasashe. Taron, wanda aka tsara gudanarwa a ƙarshen makon nan a Bharat Mandapam na New Delhi, zai haɗa jagororin BRICS da ƙasashe masu hulɗa da ita da kuma ɗaiɗaikun mutane masu alfarma da aka gayyata daga sassa daban-daban na duniya domin tattauna ci-gaban tattali a matakin duniya da alaƙoƙin lamuran ci-gaba. Nijeriya ta shirya…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta ba ‘yan D’Tigress kyautar Dala 100,000 kowanne bayan lashe FIBA Women Afrobasket

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta cika alƙawarin da ta yi na karrama tawagar manyan 'yan wasan kwando na mata, D'Tigress biyo bayan nasarar lashe gasar ƙwallon kwando na mata na Afirka na 2025 da Hukumar Ƙwallon Kwando ta Ƙasa-da-ƙasa FIBA ta shirya. A wata sanarwa da Hukumar Kula da Wasanni ta Ƙasa NSC, ta fitar a ranar Laraba, ta ce an bai wa kowace 'yar wasa Dala 100,000, wato kwatankwacin Naira miliyan 132.6, yayin da aka bai wa jami'an tawagar Dala 50,000 kowannensu. Hukumar ta tabbatar da cewa, an yi biyan ne a ranar 9 ga…
Read More

2027: Ka yi murabus za mu kula da kai – Kwankwaso ga Atiku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi kira ga tsohon Maitaimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar da ya haƙura da muradinsa na neman kujerar shugaban ƙasa ta 2027, inda ya ce a madadin haka ya mayar da hankali wajen hidimominsa na gargajiya. Kwankwaso, wanda shi ne abokin tafiyar ɗan takara shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, ya yi wannan kira ne a ranar Litinin, a lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin Ƙungiyar Fulani Nanoma a gidansa da ke Abuja. Tsohon gwamnan na Jihar Kano, wanda ke tafiya da Peter Obi a NDC, ya kafa hujja da shekaru…
Read More

Amurka ta sake kawo wa Nijeriya makamai kan taɓarɓarewar tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da Washington DC da Babban Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja suke cigaba da ƙarfafa haɗin-gwiwar bayar da tsaro da kariya a tsakaninsu, ƙasar Amurka ta aike wa Nijeriya ƙarin wasu makamai domin inganta ayyukan sojojin ƙasar. Wani jirgin Amurka na US Air Force C-17 Globemaster III ne ya yi jigilar makaman ƙarƙashin shirin yarjejeniyar siyar da makamai na sojojin waje tsakanin Washington da Abuja. Rahotanni sun bayyana cewa, kawo wa Nijeriya makaman ɓangare ne na wata yarjejeniya mai nufin ƙarfafa dabarun haɗaka tsakanin ƙasashen biyu da ƙarfafa wa ƙoƙarin Nijeriya wajen aiwatar da harkokin…
Read More

‘Yan sanda a Kano sun kama CSP na bogi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'yan sanda a Jihar Kano, ta ce ta kama wani ɗan shekara 35 mai suna Adamu Musa wanda ke iƙirarin shi ɗan sanda ne mai muƙamin CSP, wato Babban Sufuritandan 'Yan sanda bisa hannu a damfara da aikin sojan gona. Wanda ake zargin, wanda ɗan yankin Kureken Sani Quarters ne a Kano da ke zagayawa yana damfarar al'umma, an bayyana shi ne ga manema labarai ta ofishin Kakakin rundunar, CSP Haruna Abdullahi Kiyawa, a ranar Talata. Haruna Kiyawa ya bayyana cewa, a ranar 1 ga Satumba, 2026 ne rundunar ta samu wani kira…
Read More

Ƙungiyar ‘yan union ta goyi bayan sake zaɓar Gwamna Lawal karo na biyu a Zamfara kan inganta walwala

Ƙungiyar Direbobi ta Ƙasa (NURTW) ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa yadda take ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkokin sufuri da samar da ababen more rayuwa a jihar. Ƙungiyar ta ba Gwamna Lawal lambar yabo ta Ƙwarewa da Nagarta, wato Award of Excellence, a wani biki da aka gudanar ranar Laraba a Dome Pavilion da ke harabar Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara a Gusau. Baya ga karramawar, ƙungiyar ta kuma bayyana goyon bayanta ga Gwamna Lawal, inda ta amince da ya sake neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027. Mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala…
Read More

Champions League: Barcelona, PSG, Arsenal da Liverpool sun yi nasara a wasannin farko

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba ƙungiyoyin Barcelona, PSG, Liverpool da Arsenal suka yi nasara a wasannin farko na gasar Zakarun Nahiyar Turai (UEFA Champions League) na 2026/27 a jimillar wasanni shida da aka buga a sassan yankin. Daren buɗe gasar na biyu ya samar da ƙwallaye 19 a wasannin da ƙungiyoyi daban-daban suka fafata. Barcelona ta lallasa Feyenoord ta ƙasar Holland da ci 5 da 1, yayin da masu riƙe da kofin, Paris Saint-Germain ta fara da salo mai ban ƙaye da ci 6 da 1 akan Slovan Bratislava. Ita kuwa Liverpool mai kofin guda shida…
Read More