10
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alla-wadai da kisan ɗan Soshiyal Mediya kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Ibrahim Khalil da aka fi sani da Ɗan Shagamu. Haka kuma gwamnan ya bayar da umarni ga hukumomin tsaro da su gaggauta farauto masu hannu a laifin, yana mai bayyana kisan a matsayin abin firgitarwa wanda ba za a lamunta ba, sannan ya bayyana kaɗuwarsa kan abin da ya haddasa aukuwar lamarin. Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Laraba. Gwamna Abba ya…
