Babaji

5684 Posts

Ba mu kai ƙara ba, ‘yan takarar APC da PDP sun musanta ƙalubalantar nasarar Gwamnan Osun a kotu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tawagar shari'a ta jam'iyyar APC a Jihar Osun da ɗan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP, Adebayo Adedamola a zaɓen gwamna na 15 ga Agusta, sun yi watsi da iƙirarin cewa sun shigar da wani ƙorafi da ke ƙalubalantar nasarar Gwamna Ademola Adeleke a kotu. Wannan na zuwa ne bayan da aka wallafa wasu takardu a ranar Litinin a allon sanarwar kotun ƙorafin zaɓen gwamnan jihar da ke cewa na ƙorafe-ƙorafen APC da PDP ne. Rahotanni sun bayyana cewa wannan ci-gaba ya haifar da ruɗani game da ainihin inda aka samo ƙorafe-ƙorafen, inda kotun…
Read More

Abin da ya sa ba za a kama Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya ba – Jakadan MƊD

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wakilin Nijeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Ambasada Jimoh Ibrahim, ya yi watsi da iƙirarin cewa akwai yiwuwar a kama Shugaba Bola Ahmed Tinubu ko kuma a sanya masa takunkumin zirga-zirga a Amurka yayin da ya halarci babban taron majalisar ɗinkin duniya. Ibrahim ya ce, ofishin jakadancin Nijeriya ga MƊD bai samu wani saƙo daga gwamnatin Amurka ba da ke nuna cewa Tinubu ka iya fuskantar wani takunkumi a taron an UNGA, yana mai cewa shugaban Nijeriyar da iyalansa za su kasance cikin walwala a hedikwatar gunduma ta MƊD. Rahotanni sun bayyana cewa wannan bayani…
Read More

Ginin Abuja ya rushe bayan FCTA ta rufe shi, ‘yan sanda da jami’an kashe gobara sun fara ceto

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani gini ya rushe a yankin Wuse Zone 4 da ke Babban BirninTarayya Abuja, inda tuni aka fara aikin ceto yayin da jami'an bayar da agajin gaggawa suka shiga bincike domin gano ko akwai waɗanda al'amarin ya rutsa da su. Rahotanni sun nuna cewa, jami'an hukumar kashe gobara ta Abuja suna wajen domin aikin ceto, kuma an jibge motocin agajin gaggawa a yankin. Rundunar 'yan sandan Abuja ta ce ta samu kiran gaggawa kan al'amarin da misalin ƙarfe 7:45 na yammacin ranar Litinin, 7 ga Satumba 2026. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ce ta…
Read More

‘Ka kawo hujja ko ka janye kalamanka’, iyalan El-Rufa’i sun ba Ministan Tsaro kwana 7 kan zarginsa da hannu a rikicin kudancin Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya bayar da wa'adin kwana bakwai ga Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa Gwabin (mai ritaya), da ya gabatar da wata hujja kan zarginsa ga tsohon gwamnan cewa ya shirya kashe-kashe a kudancin Kaduna ko kuma ya fito ya janye iƙirarin nasa. Janar Musa dai ya zargi tsohon gwamnan ne na ɗaukar matakan da suka ƙarfafa rarrabuwar kai da taimaka wa matsalolin rashin tsaro a Jihar Kaduna a lokacin da yake gwamna daga shekarar 2015 zuwa 2023, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Ministan ya yi…
Read More

RUƊANI: Peter Obi ya ziyarci taron buɗe ofishin ɗan takarar shugaban ƙasa na APM a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi ya halarci taron ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen Seyi Makinde, wanda shi ne jam'iyyar APM ta fitar a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa na babban zaɓen 2027 da ke tafe. An gudanar da taron ne a Babban Birnin Tarayya Abuja, inda aka ga Obi da wasu sanannun 'yan siyasa na APM ciki har da jagoranta na ƙasa kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed. A wasu bidiyoyi da aka yaɗa a kafafen sada zumunta, an ga tsohon gwamnan na Jihar Anambara…
Read More

Mijin Shugabar Tanzaniya, Samia Suluhu ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin mijin Shugaba Samia Suluhu Hassan ta ƙasar Tanzaniya, Hafidh Ameir ya rasu yayin da yake karɓar magani a wani asibiti da ke Birnin Zanzibar. BBC ta ruwaito cewa, Mataimakin Shugaban ƙasar, Deogratius Ndejembi ne ya sanar da rasuwa Ameir, inda ya ce ya kasance yana fama da wata cuta da ta shafi zuciya. Ndejembi ya ce, Ameir ya rasu ne da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Litinin a Asibitin Emilio Mzena Memorial da ke Zanzibar. Ya ƙara da cewa, ana shirin gudanar da jana'izarsa a ƙauyen Kizimkazi da ke wani yankin…
Read More

Kotun zaɓen Osun ta wallafa koken APC da PDP na ƙalubalantar nasarar Gwamna Adeleke

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kotun zaɓen gwamnan jihar Osun ta wallafa ƙorafe-ƙorafe biyu da jam'iyyun APC da PDP suka shigar mata, waɗanda suke ƙalubalantar nasarar da Gwamna Ademola Adeleke ya sake samu. Rahotanni sun nuna cewa kotu ta wallafa ƙorafe-ƙorafen ne a allonta na sanarwa a sakatariyarta da ke Osogbo a ranar Litinin, wanda ke nuna ɗaukar matakin shari'a kan zaɓen, wanda aka gudanar a ranar 15 ga Agusta. An samu haka ne bayan Sakataren kotun, Pefe Belemore ya tabbatar da cewa an shigar da ƙorafe-ƙorafen a gaban kotun nasu kuma za su wallafa su ga al'umma. Hakan…
Read More

Gwamna Namadi ya amince da Lawan Ahmed Muhammad a matsayin Sarkin Gumel na 17

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Jigawa, Malam (Dr.) Umar A. Namadi, FCA, ya amince da naɗin Dakta Lawan Ahmed Muhammad Sani a matsayin Sarkin Masarautar Gumel na 17. Wannan naɗi ya biyo bayan shawarwari daga majalisar masu zaɓen sarki da majalisar sarakunan jihar Jigawa. Dakta Lawan Ahmed Muhammad Sani ya riƙe muƙamin Ciroman Gumel kuma Hakimin Gundumar Bosuwa. Ya kuma riƙe muƙamin daraktan Tsaron Yanar Gizo a Hukumar Ci-gaban Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA). A wata sanarwa daga Sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim ya fitar, ya ce Gwamna Namadi ya bayyana godiyarsa ga majalisar masu zaɓen…
Read More

Majalisar Wakilai ta rushe baki ɗaya kwamitocin wucin-gadinta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Wakilai ta sanar da rushe baki ɗaya kwamitocin wucin-gadin da ta kafa domin gudanar da wasu bincike kan muhimman lamuran ƙasa, inda ta umarci mambobinsu da su dakatar da dukkan ayyukan da aka ɗora musu a nan take. Rahotanni sun bayyana cewa, umarnin ya biyo bayan ƙarewar wa'adin da aka bai wa kwamitocin ne na su kammala bayar da rahotannin ayyukan da aka ba su da miƙa su gare ta bisa sharuɗɗa da al'adar majalisar. Wannan mataki ya fara aiki ne a ranar Juma'a, 28 ga Agusta, 2026. Kakakin majalisar, Tajudeen Abbas ne…
Read More

Sojoji sun ceto mutum 36 bayan halaka jagororin ‘yan ta’adda a Borno da Katsina – Hedikwatar Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hedikwatar Tsaro ta ce hare-haren dakarunta ta sama sun halaka 'yan bindiga guda 70 a Jihar Neja, sannan ta musanta cewa atisayen sojoji ya yi ajalin fararen hula yayin da suka ceto mutane 36 da aka sace da kuma halaka 'yan ta'adda da dama ciki har da jagororinsu biyu a atisaye daban-daban a faɗin Nijeriya. Daraktan Yaɗa Labaran hedikwatar, Manjo-Janar Michael Onoja ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ce an ƙaddamar da atisayen ne a tsakanin ranakun 31 ga Agusta da 3 ga Satumba. A cewar sanarwar,…
Read More