06
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun Sojoji a Jihar Borno, sun yi nasara ceto wata yarinya mai kimanin shekaru 11 da aka yi zargin 'yan ta'adda sun yi garkuwa da ita zuwa jihar da nufin samar da bayanai kan sojoji. Sojojin Shiyya ta 82 ta Task Force Battalion ne suka samo yarinyar mai suna Aisha Mustapha yayin wani sintiri a yankin Armuda General da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza. Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:41 na daren ranar 4 ga Satumba, 2026. Sun yi zargin cewa, Aisha tana ɗaya daga…
