04
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta musanta bayar da goyon baya ga yunƙurin kifar da gwamnatin soji ta Jamhuriyar Nijar, tana mai watsi da iƙirarin cewa hakan ya samu goyon bayan Ƙungiyar Ƙasashe Afirka ta Yamma masu Ƙarfin Tattalin Arziƙi (ECOWAS) kuma musamman yadda aka danganta da Nijeriya. Ƙaramin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Sola Enikanolaiye ne ya bayyana haka a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannunsa a ranar Alhamis, inda ya bayyana iƙirarin, wanda ake yaɗawa a kafafen Soshiyal Mediya a matsayin ƙoƙarin ruɗar da jama'a da ɓata wa Nijeriya suna. Enikanolaiye ya ce an…
