03
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ke cika shekaru 60 a duniya, an bayyana shi a matsayin mutum mai ban mamaki wanda haƙuri, kiyaye amana da kuma ƙaunarsa ga shugabancin ƙasarsa suka bayar da gudummawa wajen ci-gaban Ajandar Sabon Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ingantacciyar Nijeriya. Alhaji Musa Illiyasu Kwankwaso, Darakta Zartarwa na Harkokin Kuɗi na Hukumar kula da Kogunan Haɗejia da Jama'are ne ya bayyana haka yayin taya Mataimakin Shugaban Ƙasar murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Ya ce: "A yau Najeriya ta fi samun ƙarfafa alaƙa tsakanin ƙabilu daban-daban, saboda…
