01
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen na hannun dama ga Ministan Abuja Nyesom Wike kuam tsohon Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP na Ƙasa reshen Kudu maso Kudu, Cif Dan Orbih ya rasu. Marigayi Orbih ya rasu ne a ranar Litinin, 31 ga Agusta, 2026, a cewar wata sanarwa da iyalansa suka fitar. Iyalan sun sanar da haka ne a sanarwar da ke ɗauke da sanya hannun Francis Udukhomoi Orbih a madadinsu, inda suka bayyana al'amarin a matsayin babban rashin da ya jefa su cikin jimami. "Cikin alhini da ƙunci da yardar da ikon Ubangiji Maɗaukaki, iyalan Chief M.C.K. Orbih na…
