31
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jihar Katsina ta samu rahoton samun masu ɗauke da cutar mashaƙo guda 1,000 tun daga Junairu, 2026, inda kuma kaso 5 na waɗanda abin ya shafa suka rasu, lamarin da ya tilasta wa gwamnatin jihar hanzarta ɗaukar matakan gaggawa domin daƙile cigaba da yaɗuwar cutar. Sakatariyar riƙo ta Hukumar kula da Lafiya a Matakin Farko (PHCA) ta jihar, Shaima'u Abba ce ta bayyana haka ga manema labarai a cibiyar aikin gaggawa na hukumar da ke garin Katsina a ranar Lahadi. Ta bayyana mashaƙo (diphtheria) a matsayin cuta mafi haɗari da ake saurin kamuwa da…
