Babaji

5684 Posts

Babu ɗan bindigar da zan ba wa sisin kwabo a matsayin fansa, inji Gwamnan Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jadda da matakinsa na ƙin goyon bayan dukkan wata tattaunawa da 'yan bindigar da suke sace mazauna da haddasa firgici a jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne a wata hira da 'yan jarida a ranar Litinin, inda ya ce bai wa 'yan bindiga kuɗi abu ne da ke ƙara musu ƙarfi. Ya kuma ce, tattaunawar sulhu da aka yi da su a baya ba su bayar da kyawawan sakamako ba. "Kun san akwai wasu matakai masu tsauri da suka dace ka ɗauka a matsayinka na jagoran gida…kuma na…
Read More

Tinubu ya ayyana makokin kwana uku kan hatsarin jirgin sojoji a Ondo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana makokin kwana uku ga jami'an Rundunar Sojin Saman Nijeriya da suka rasu a hatsarin jirgin sojoji na ranar Litinin. Haka kuma, Shugaban ya umarci a sauke tutoci zuwa tsakiyar sanduna domin karrama jami’an da suka rasa rayukansu a sanadiyyar aukuwar lamarin. Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ne ya sanar da wannan umarni a wata sanarwa da ya fitar a ranar 5 ga Oktoba, 2026. Da fari Shugaban ya bayyana kaɗuwarsa kan hatsarin jirgin mai tashin angulu na Nigeria Air Force ATR-42 jet, wanda ya yi ajalin mutane da…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya dawo Abuja bayan shafe kwana shida a Legas

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shirya barin Legas zuwa Abuja a yammacin ranar Litinin bayan shafe kwanaki shida a tsohuwar babbar birnin tarayyar. A ranar 29 ga Satumba ne Tinubu ya isa Legas bayan kammala hutunsa na shekara a Landon da Paris. Yayin zamansa a Legas, Shugaban ya gabatar wa 'yan Nijeriya jawabi a ranar 1 ga Oktoba, wato lokacin bikin cikar Nijeriya shekeru 66 da samun 'yancin kai. Bayan haka a ranar, Shugaban ya kuma halarci taron karrama marigayi MKO Abiola musamman akan gwagwarmayarsa ta siyasa da kuma tarihin "June 12" bayan gwagwarmayar…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da hatsarin jirgin sojoji ya rusa da mutum 32 a Ondo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci-gaban Sararin Samaniyar Nijeriya, Festus Keyamo (SAN), ya tabbatar da labarin hatsarin wani jirgin sojoji da ke ɗauke da mutane 32 a yankin Igbokoda na Jihar Ondo a Kudu maso Yammacin Nijeriya. Rahotanni sun nuna cewa, jirgin, mai lamba 931, yana tafiya ne daga Benin zuwa Legas a lokacin da aka neme shi aka rasa da misalin ƙarfe 9:13 na safiyar yau Litinin, lamarin da ya sanya jami'an kula da zirga-zirgar jirage shiga gudanar da bincike. Keyamo a wata sanarwa, ya ce yunƙuri da dama na ji ta bakin…
Read More

NRS ta ankarar da al’umma kan shafin ɗaukar aiki na bogi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (NRS) da aka sani da FIRS, ta yi watsi da wani saƙon ɗaukar aiki da ke yawo a kafafen sada zumunta da sunan Federal Inland Revenue Service (FIRS), inda ta bayyana shi a matsayin "damfara". A wani saƙo da ta fitar wa al'umma mai taken "Fraudulent Recruitment Notice" da ta wallafa a sahihin shafinta na X.com a ranar Litinin, NRS ta ce ta samu labarin saƙon bogi da ake yaɗawa a kafafen Soshiyal Mediya mai taken "Federal Inland Revenue Service - Replacement". A cewarta, saƙon yana tallata batun damarmakin…
Read More

Dakarun tsaro sun halaka babban Kwamandan ISWAP, Abdussamad Ohida a Ondo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani atisayen leƙen asiri da haɗakar jami'an Rundunar Sojojin Nijeriya, Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) da na Western Nigeria Security Network da aka sani da Amotekun, ya yi sanadiyyar halaka wani babban kwamandan kungiyar ISWAP mai suna Abdussamad Ohida, wanda aka ƙaddamar a Dajin Owo da ke Jihar Ondo. Rahotanni sun nuna cewa, Ohida, wanda aka sani da Anwar da ke shirin ƙaddamar da wasu munanan hare-haren ta'addanci a wasu jihohin kudancin Nijeriya, an halaka shi ne tare da wasu gungun 'yan ƙungiyar ta'addancin bayan jami'an tsaron sun kai farmaki a maɓoyarsu a…
Read More

‘Yan bindiga sun buɗe wa jama’a wuta yayin dawowa daga kasuwa a Filato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan sanda a Jihar Filato ta tabbatar da cewa mutum bakwai sun jikkata a sakamakon wani harbe-harbe da aka ƙaddamar a yankin babban titin Ɓukuru da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu. Rahotanni sun ce wannan al'amari ya rutsa da wasu ƙananan 'yan kasuwa da ke koma wa gidajensu daga kasuwa, inda aka yi zargin wasu 'yan bindiga ne suka buɗe wa motarsu wuta a garin Ɓukuru da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu. A wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, rundunar ta yi tir da wannan hari, inda ta ce…
Read More

INEC za ta bayyana wa duniya shirye-shiryen zaɓen 2027 yayin da ya rage saura kwana 100

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta ce za ta gudanar da babban taron 'yan jarida da masu ruwa da tsaki da duniya a ranar Talata, 6 ga Oktoba, 2026 yayin da ya rage saura kwanaki 100 a gudanar da babban zaɓen 2027 a Nijeriya. A yayin taron, INEC za ta bayar da ba'asi akan shirye-shiryen zaɓen, ciki har da rajistar masu zaɓe, fitar da sunayen 'yan takarar, halin mallakar kayayyakin zaɓe da wasu muhimman matakai domin tabbatar da sahihancin zaɓen. Adedayo Oketola, wato Sakataren yaɗa labaran Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ne ya bayyana…
Read More

WAEC ta ƙara ba wani ɗan Nijeriya babban muƙami

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Shirya Jarrabawa a Yammacin Afirka (WAEC) ta naɗa Mista Suleiman Ɗanlami Kum a matsayin sabon Shugaban Reshenta na Nijeriya, inda ya maye gurbin Dakta Amos Josiah Dangut. Kum, wanda ƙwararren jami'in gudanar da harkokin jarrabawa ne, ya fara aiki da WAEC ne tun a shekarar 1998 a matsayin Mataimakin Rajistara na II. An haife shi a ranar 16 ga watan Oktoban 1970, kuma ainihinsa ɗan Ƙaramar Hukumar Langtang ta Arewa ne daga Jihar Filato. Ya yi digirinsa na farko a Tsangayar Noma a Fannin Kiwon Dabbobi na Jami'ar Noma da ke Makurɗi a…
Read More

‘Yan bindiga sun rage fansar ‘yan hidimar ƙasa daga miliyan N50 zuwa N5m kowanne

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'Yan bindigar da suka sace 'yan hidimar ƙasa na NYSC su guda 20 a kudancin Nijeriya sun sanar da rage adadin kuɗin fansar da suka buƙaci a biya da fari domin sako su, daga Naira miliyan 50 zuwa Naira miliyan 5 ga kowannensu, lamarin da ya dawo da ainihin kuɗin zuwa miliyan N100. Tun a ranar Juma'a ne dai masu garkuwar suka bayar da wa'adin kwana guda domin a biya miliyan N50 ɗin da suka buƙata da fari ga kowane ɗaya daga cikin 'yan hidimar, inda ake tsammanin wa'adin ya ƙare a yau Lahadi.…
Read More