Babaji

5684 Posts

Kakakin hukumar kashe gobarar Kano, Saminu Abdullahi ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta yi rashin mai magana da yawunta, Saminu Yusuf Abdullahi, wanda ya rasu a safiyar yau Laraba bayan fama da wani gajeren rashin lafiya. An tabbatar da mutuwarsa ne a wata takarda da aka aike wa manema labarai a Kano daga Shugaban ofishin hukumar na Ƙaramar Hukumar Ɗambatta, PFS2 Muhammad Ibrahim Nasiru. A cewar sanarwar, an gudanar da jana'izar marigayin ne da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar Laraba. Marigayin ya kasance kakakin hukumar a jihar Kano, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen harkokin sadarwa da ayyukan bayar da…
Read More

Iyalai sun koka kan shirun mahukunta mako guda bayan turmutsutsin gidan gwamnatin Neja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Bayan sati ɗaya da turmutsutsin gidan gwamnatin Jihar Neja da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku da raunata wasu da dama, gwamnatin jihar da rundunar 'yan sanda sun cigaba da kasancewa a halin abin da iyalai suka kira da "halin ko-in-kula" kan al'amarin. Sun bayyana damuwa kan yadda babu wani saƙo ko ta'aziyya a hukumance daga bangarorin biyu kan waɗanda suka rasu a iftila'in ko kuma samar da wani tallafi ga iyalan mamatan. Manhaja ta ruwaito cewa, Gwamnatin Jihar Neja zuwa yanzu ba ta fitar da wani bayani ba a hukumance game da aukuwar…
Read More

‘Na bar ku lafiya’, Messi cikin ƙawa-zuci ya zura ƙwallo a wasansa na Ajantina na ƙarshe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Bayan shafe sama da shekaru 20 yana wakiltar Ajantina, zakaran ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya Lionel Andres Messi Cuccittini, ya kammala wakiltar ƙasar da zura ƙwallo ɗaya da bayar da biyu da aka ci a wasansu da Jamhuriyar Benin a birnin Buenos Aires na ƙasar kudancin Amurka. Messi, mai shekaru 39 ya buga wasansa na 208 a matakin ƙasa-da-ƙasa kuma na ƙarshe, inda ya zura ƙwallon 126 a rigar Ajantina a bugun fenareti. Da fari, ya taimaka Nicolas Otamendi da Nico Paz sun zura ƙwallo guda kowannensu a wasan ƙawancen da aka tashi…
Read More

Ronaldo ya bayyana cikakken labarin dalilin barinsa tawagar Portugal

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Zakaran ɗan ƙwallon ƙafa na duniya Cristiano Ronaldo, ya fitar da wata sanarwa da a ciki yake zargin kociyan Portugal, Jorge Jesus da cin amana a lokuta mabambanta, inda ya bayyana hakan a matsayin rikicin da ya sabbaba masa barin tawagar 'yan wasan ƙasar. Kyaftin ɗin tawagar mai shekaru 41 ya bayyana cewa, da fari ya ƙudiri aniyar yin ritaya bayan kammala gasar Kofin Duniya na 2026, amma daga bisani shugaban hukumar ƙwallon ƙafan Portugal ya shawarce shi da ya cigaba da wakiltar ƙasar kuma ya amince da hakan. Da farko, Ronaldo ya goyi…
Read More

Hatsarin Ondo: Bayan shekaru 20 da rasuwar mahaifinta a irin hatsarin, ta rasa mijinta mako biyu da ɗaura aurensu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shekaru ashirin da suka gabata da rasa mahaifinta a hatsarin jirgin sojojin sama, Flight Lieutenant Damilola Adekunle ta sake haɗuwa da wata jarrabawa a wannan karon na rasa mijinta, wanda aka ɗaura musu aure ƙasa da makonni uku da suka gabata a makamancin hatsarin. Mahaifin Adekunle, wato Wing Commander E.O. Adekunle yana ɗaya daga cikin jami'an rundunar Sojojin Sama na Nijeriya (NAF) da wani hatsarin jirgi ya rutsa da su a Jihar Benuwai a ranar 17 ga Satumbar 2006. Al'amarin ya auku ne a yankin Oko da ke Ƙaramar Hukumar Vandeikya a lokacin da…
Read More

Gwamanan Zamfara ya shiga tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Habasha don tattaunawar jagoranci

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu gurbi a tawagar manyan jami’an Nijeriya da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da aikewa birnin Addis Ababa na Habasha, domin gudanar da shirin musayar ƙwarewa da dabarun shugabanci tsakanin Nijeriya da Habasha. Tawagar Gwamnatin Tarayya za ta kasance ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, tare da haɗin-gwiwar Gwamna Dauda Lawal na Zamfara da wasu gwamnoni. Ana sa ran tawagar za ta tashi daga Nijeriya ranar Talata, domin halartar taron musayar ƙwarewar shugabanci tsakanin Nijeriya da Habasha, wanda za a gudanar daga ranar 7 zuwa 9 ga Oktoba, 2026. Sauran gwamnoni da…
Read More

Tinubu ya yi jimamin rasuwar Babban Sakataren Majalisar Ƙolin Shari’a, Nafi’u Baba-Ahmed

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya bayyana jimaminsa bisa rasuwarsa Babban Sakataren Majalisar Ƙolin Shari'a a Nijeriya (SCSN), Malam Nafi’u Baba-Ahmed. Malam Baba-Ahmed, wanda jami'in gudanarwa kuma jagoran addini da ake mutuntawa, ya rasu ne a safiyar ranar Talata bayan tsawon lokaci yana hidimta wa Musulunci da Nijeriya. Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jagora mai tasiri da ya gudanar da harkokin SCSN bisa hikima, hangen nesa da ƙoƙarin samar da haɗin kai, adalci da zaman lafiya acikin al'umma. Tinubu ya tunatar da alaƙarsa ta tsawon lokaci da shi musamman a lokacin shirye-shiryen zaɓen 2011…
Read More

Legas ta yi fintinkau yayin da INEC ta fitar da jerin rijistar masu zaɓe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da ake cigaba da tunkarar babban zaɓen 2027, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta fitar bayyana jihohi masu mafiya yawan adadin rajistar masu zaɓe, inda Legas Kano da Kaduna suke kan gaba. Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ne ya bayyana adadin a ranar Talata a Abuja a lokacin da yake jawabi kan shirye-shiryen hukumar ga zaɓukan na 2027 da ke cigaba da ƙaratowa. A cewarsa, Legas ce take jagorantar jaddawalin da jimillar rajistar masu zaɓe guda 7,488,633, sai Kano mai 6,570,276 da kuma Kaduna mai guda 4,662,640. Katsina ita ce jiha ta huɗu…
Read More

NAF ta fitar da sunayen mutane 25 da suka rasu a hatsarin jirgin sojoji a Ondo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar Sojin Saman Nijeriya NAF, ta fitar da sunayen mutane 25 da suka rasu a hatsarin jirgin rundunar (ATR 42) da ya auku a yankin Igbokoda da ke Jihar Ondo a ranar Litinin. Rahotanni sun nuna cewa al'amarin ya faru ne a lokacin da jirgin na NAF 931 ke ɗauke da jami'an jirgi biyar da fasinjoji 20 yayin da yake kan hanyar zuwa Legas daga Benin. A wata sanarwa da Kakakin NAF, Air Komodo Ehimen Ejodame ya fitar, ya ce babu wanda ya tsira daga iftila'in, wanda ya sanya hukumomin hanzarta gudanar da aikin…
Read More

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ɗage hukuncin neman belin El-Rufa’i

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin, 5 ga Oktoba, Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zaune a Kaduna ta ɗage zaman sauraron ƙorafin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i ya shigar mata na ƙalubalantar hukuncin Babbar Kotun Jihar Kaduna da ya yi watsi da buƙatarsa ta neman beli. El-Rufa'i, wanda Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gurfanar da shi, ya tunkari Kotun Ɗaukaka Ƙarar ne domin neman ta soke hukuncin Babbar Kotun da bayar da belin nasa daga kotun ta ƙi amincewa da shi. Da yake ganawa da 'yan jarida jim-kaɗan bayan…
Read More