Babaji

5684 Posts

FIFA ta yi watsi da ƙorafin Nijeriya kan aike wa imel ɗin da ba ta amince da shi ba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa-da-ƙasa FIFA, ta yi watsi da ƙorafin Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF) akan rikicin wasanta da DR Kongo na neman gurbi, saboda NFF ɗin ta yi kuskuren tura wa wani adireshin Imel da ba shi ta amince wa ba. A madadin amfani da shafin shari'ar FIFA na yanar gizo, NFF ta tura ƙorafin nata ne ta wani adireshin Imel da ake amfani da shi a ofishin Babban Sakataren hukumar ƙwallon ƙasa-da-ƙasar. Wannan kure da ya haifar da jinkirin isarwa da kuma watsi da ƙorafin daga bisani akan rashin cika…
Read More

Kotu ta kori ƙorafin El-Rufa’i na neman haramta wa EFCC da ICPC kama kadarorinsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta yi watsi da ƙorafin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya shigar a gabanta na neman ta katange Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da wasu hukumomin kula da biyayya ga doka daga sanya wa asusun bankunansa takunkumi ko ƙwace kadarorinsa. Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ce ta yi hukuncin a ranar Alhamis bayan ta ce ƙorafin cin fuska ne ga matakan kotu. El-Rufa'i dai ya shigar da ƙorafin ne akan ICPC, EFCC, DSS da Antoni Janar na Ƙasa (AGF) a matsayin waɗanda ake ƙara…
Read More

Tsohon sakataren gwamnati, Yayale Ahmed ya jinjina wa Ambasada Isma’il Abba kan nasarorin NAHCON

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Alhaji Yayale Ahmed, yaba wa Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Ambasada Isma'il Abba Yusuf kan nasarorin da hukumar ta samu a ƙarƙashin jagorancinsa, inda ya ce ana samun kyawawan sakamako a harkokin jigilar alhazan Nijeriya. Yayale Ahmed, wanda kuma shi ne Ajiyan Katagum, ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara a babban ofishin NAHCON da ke Abuja. A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'ar hukumar, Shafi'i Sani Mohammed ya fitar, ya ce a yayin ziyarar, tsohon sakataren gwamnatin ya kuma bayar da shawarwari na…
Read More

Amurka ta gurfanar da Nicolás Maduro da matarsa kan makircin cin zarafi da wasu laifuka

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Amurka ta sanar da gurfanar da tsohon Shugaban ƙasar Venezuela Nicolás Maduro da matarsa, Cilia Flores bisa zargin su da hannu a makircin aikata cin zarafi, wanda ke nuna an samu ƙarin sabon zargin aikata babban laifi ga tuhume-tuhumen safarar ƙwayoyi da suke fuskanta. A bayanan da aka fitar a birnin New York daga baya a ranar Alhamis, 8 ga Oktoba, 2026, ana zargin Maduro da Flores da umarta da sanya ido akan wani salon cin zarafi, tserewa ba bisa doka ba da rikici akan abokan hamayyar siyasa yayin shekaru 13 na mulkinsu.…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta sanar da rangwamen farashin fetur na kwana 30

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa 'yan Nijeriya za su fara siyan fetur a farashi mai rahusa a gidajen man NNPCL har na tsawon wata guda. Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattali, Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis. Ya ce, za a samu ragi a kowace lita daga ainihin yadda aka saba siya. A cewarsa gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne da nufin samar da sauƙi ga al'umma musamman bisa la'akari da masu harkar sufuri na 'yan kasuwa. Sannan, ya ce gwamnatin tarayyar za ta…
Read More

Sojoji sun mayar da filin tsohon Oyo National Park cibiyar horo bayan garkuwar Oriire

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Kwamandan Sojojin Nijeriya na Shiyya ta 2, Manjo-Janar Auwalu Mahmuda ya bayyana cewa rundunar ta karɓe iko tare da mayar da filin shaƙatawa na Old Oyo National Park cibiyar bayar da horo bayan garkuwa da ceto ɗalibai 40 da malamansu a Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo. Mahmuda ya faɗi haka ne a ranar Laraba yayin karɓar baƙuncin wakilan ƙungiyar 'yan jarida ta Chapel of the Nigerian Union of Journalist reshen Jihar Oyo, a hedikwatar shiyyar da ke yankin Odogbo a Ƙaramar Hukumar Akinyele ta jihar. Ya ce, Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya, Laftanal…
Read More

Kwana biyu bayan hatsarin jirgin Ondo, wani jirgin NAF ya karci ƙasa a Benuwai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani jirgi mai tashin angulu na Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) ya karci ƙasa a Jihar Benuwai a yayin sauka a ranar Laraba a lokacin da yake ƙoƙarin kai wa sojoji agaji a lokacin da suke ƙaddamar da wani atisayen fatattakar 'yan bindiga, kamar yadda wata majiya ta shaida wa manema labarai. Da take tabbatar da aukuwar lamarin ta sahihin shafinta, NAF ta bayyana al'amarin a matsayin "saukar kiyayewa", inda ta ce matuƙin ya yi amfani da ƙwarewarsa ta aiki ne wajen sauka daga nisan mil 10 a sararin samaniya bayan nasarar kammala atisayen.…
Read More

‘Yan hidimar ƙasa 20 da aka sace a Imo sun shaƙi iskar ‘yanci bayan mako guda

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'Yan hidimar ƙasa (NYSC) guda ashirin da aka yi awon-gaba da su a lokacin da suke kan hanyar tafiya daga Jihar Oyo zuwa sansanoninsu a Jihar Abia sun kuɓuta bayan shafe kwana bakwai a hannun 'yan bindiga. An yi garkuwa da yayayyun ɗaliban ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata akan hanyar Owerri zuwa Onitsha da ke yankin Umunoha a Jihar Imo, bayan wasu 'yan bindiga sun farmaki motocin bos biyu da ke ɗauke da su daga Ibadan, inda suka tasa ƙeyarsu su 20 zuwa daji. Wannan al'amari ya haifar da damuwa acikin…
Read More

NAHCON ta karɓi baƙuncin Babban Kwamandan Sibil Difens don ƙarfafa alaƙar aiki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba, 7 ga Oktoba, 2026 Babban Kwamandan Hukumar Tsaron Fararen Hula ra Ƙasa (NSCDC) da aka sani da Sibil Difens, Dakta Ahmed Abubakar Audi, ya kai ziyarar girmamawa ga Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Ambasada Isma'il Abba Yusuf a ofishinsa da ke hedikwatar hukumar ta Hajj House a Abuja. Wannan ziyara ta taimaka wajen samar da damar tattauna muhimman al'amuran da suka shafi ƙarfafa alaƙar aiki tsakanin NAHCON da NSCDC musamman a lamuran da suka shafi tsaro, gudanar da dandazon jama'a da amincin alhazai da kuma samar da ingantaccen yanayi na…
Read More

Kotun Maiduguri ta bada belin mutum biyar da aka tsare kan rigar TMG

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Kotun Shari'a a Maidugurin Jihar Borno ta bayar da belin wasu mutane biyar da aka kama su bisa sanya riguna masu ɗauke da rubutun #TinubuMustGo (TMG). An kama mutanen ne a ranar 25 ga Satumba, 2026 a cikin garin Maiduguri, lamarin da ya tayar da ƙura musamman a kafafen sada zumunta kan 'yancin bayyana ra'ayi da mutunta tafiyar siyasa a jihar. Saidai rundunar 'yan sandan jihar Borno, ta yi iƙirarin cewa ta kama waɗanda ake zargin ne da wasu laifuka akan ra'ayin siyasa ds wasu ke zargi, wannan ci-gaba ya haifar da cece-kuce…
Read More