Babaji

5684 Posts

2027: NDC za ta ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen Obi da Kwankwaso ranar 20 ga Oktoba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar adawa ta NDC ta sanar da shirinta na ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓenta na shugaban ƙasa domin babban zaɓen 2027, yayin da jam'iyyar ke cigaba da nazari kan bayar da manyan muƙamai. Peter Obi, wanda tsohon Gwamnan Jihar Anambara ne, shi ne kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar tare da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso a matsayin abokin tafiyarsa. Da yake ganawa da 'yan jarida a Abuja ranar Asabar, Shugaban NDC na ƙasa, Cleopas Zuwoghe, ya ce jam'iyyar ta shirya tsarin kwamitin yaƙin neman zaɓen, amma tana yin shawara…
Read More

Rundunar ‘yan sanda ta tsare sufeto da wasu biyu kan tatsar direbobi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamishinan 'yan sandan Jihar Imo, Audu Bosso, ya umarci a kama tare da tsare wata sufeto da wasu jami'ai biyu na kare fararen hula na jihar ƙarƙashin Imo State Civil Guard Corps (IMSCGC) bisa zargin su da laifin tatsar masu ababen hawa. Kakakin rundunar, Henry Okoye a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, ya ce kwamishinan 'yan sandan ya kuma umarci a gudanar da bincike akan al'amarin. DSP Okoye ya bayyana cewa al'amarin ya faru ne a ranar Alhamis kuma jami'an sun yi iƙirarin cewa sun samu masu ababen hawan ne da…
Read More

Kotu ta tasa ƙeyar ɗan Nijar kurkukun Abuja kan zargin hannu a safarar makamai ga ‘yan ta’adda

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Juma'a Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta tura wani ɗan Nijar mai suna Muhammad Ibrahim gidan yari bisa zargin sa da laifin safarar alburusai guda 170 na bindigar AK-47 domin ayyukan 'yan ta'adda a Jihar Katsina. Alƙali Salim Ibrahim ne ya umarci a ajiye shi a kurkukun Kuje da ke Abuja bayan ya musanta hannu a laifuka huɗu da ake tuhumarsa a kai ciki har da ta'addanci da mallakar katin shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) ta ɓarauniyar hanya. Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) ne suka kama wanda ake zargin, inda…
Read More

Kotu ta ba Abba Kyari damar ƙarshe ya zayyano shaidu a shari’ar dillancin hodar ibilis

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Juma'a Mai Shari'a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya ya ba wa dakataccen jami'i, Abba Kyari da wasu 'yan sanda guda huɗu da suke fuskantar tuhumar hannu a dillancin hodar ibilis dama ta ƙarshe domin su shigar da jaddawalin sunayen shaidunsu a shari'ar da ake yi akansu. Alƙalin ya yi gargaɗin cewa rashin biyayya ga hakan ga iya sa a rufe musu bayar da kariyarsu don haka wajiban ne su gaggauta cika umarnin domin kawo ƙarshen hukuncin shari'ar. Ya bayar da wannan gargaɗi ne yayin da yake bayyana takaicinsa kan rashin biyayya…
Read More

Sojoji sun fara farautar baƙin akwatin jirgin da ya yi hatsari a Ondo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) ta ce ta fara ƙoƙarin gano baƙin akwati da na'urar ɗaukar murya jirgin ATR-42 da ya yi hatsari a Igbokoda da ke Ƙaramar Hukumar Ilaje ta Jihar Ondo a makon day a gabata. Jami'i SSE Ebimobo Ebiowe, wanda mataimakin air vice marshal ne ya bayyana haka ga 'yan jarida a wajen da hatsarin ya faru a ranar Juma'a. Al'amarin ya auku ne a lokacin da jami'an NAF suka taso daga Benin City na jihar Edo suka nufi Legas, a kusa da sansanin FOB na NAF a ranar Litinin, wanda…
Read More

Tinubu zai buɗe yaƙin neman zaɓe a Kaduna ranar 24 ga Oktoba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Asabar 24 ga Oktoba, 2026 ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai fara yawon neman zaɓensa na shugaban ƙasa domin babban zaɓen 2027 da ke tafe a Jihar Kaduna. Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar na jam'iyyar APC, Abdulaziz Yari ne ya bayyana haka a ranar Juma'a jim-kaɗan bayan ganawa da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja Yayin hira da wakilan fadar. Ya ce, Shugaban ƙasa ya amince da jaddawalin yaƙin neman zaɓen da suka gabatar masa, inda ya ƙara da cewa daga nan zai zarce zuwa Maiduguri, Jihar…
Read More

Mayar da hannun agogo baya ne dawo da tallafin fetur – APC ga ‘yan adawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar APC ta yi watsi da batun dawo da tallafin fetur, inda ta ƙalubalanci 'yan takarar shugaban ƙasa na tsagin adawa da su yi bayanin yadda za su samar da kuɗaɗen tsarin ba tare da tauye kuɗaɗen shigar da gwamnati take samu ba da kuma sauke wajiban suke kanta na kuɗi. Sakataren Jam'iyyar na Ƙasa, Sueajudeen Ajibola Basiru ne ya faɗi haka a ranar Juma'a, inda ya bayyana cire tallafin fetur a matsayin abin da ba zai yiwu ba, sannan ya yi gargaɗin cewa muddin aka dawo da shi, Nijeriya za ta koma gidan…
Read More

‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da manyan jami’an cibiyar bincike a Oyo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni daga Kudu maso Yammacin Nijeriya sun bayyana cewa, wasu 'yan bindiga sun afka wa cibiyar bincike ta Cocoa Research Institute of Nigeria (CRIN) da ke Jihar Oyo, sannan suka sace manyan jami'ai guda uku yayin da suke tsaka sa binciken tsirrai a wata gona da ke farfajiyar cibiyar. Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar al'amarin a ranar Juma'a, 9 ga Oktoba, 2026, inda ta tabbatar wa al'umma cewa an fara ƙoƙarin ceto mutanen cikin aminci da kama masu hannu a laifin. Kakakin rundunar 'yan sandan, Olayinka Ayanlade ne ya tabbatar da…
Read More

Sojoji sun ƙwato babura 17 da makamai bayan daƙile harin Lakurawa a sansanin Kebbi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun Rundunar Sojin Nijeriya sun yi nasarar daƙile wani harin sanyin safiya daga wasu mutane da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne a sansaninsu na Forward Operating Base da ke yankin Maiyama a Jihar Kebbi, inda suka ƙwato babur guda 17 bayan maharan sun janye farmakin nasu, kamar yadda mahukuntan soji suka faɗa. Al'amarin ya auku ne a ranar Laraba, 7 ga Oktoba, 2026 a lokacin da wani dandazon 'yan ta'adda da ya ƙunshi sama da babura 100 ya afkwa wa yankin sansanin tare da buɗe wuta, a cewar sashen Atisayen FANSAR YAMMA. Rundunar Sojin…
Read More

Gwamnatin Tarayya na ƙoƙarin saukar da hauhawar farashi, inji Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ce tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta sauke hauhawar farashin kayayyaki zuwa ƙaramin mataki ga 'yan Nijeriya, kamar yadda Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya bayyana. Onanuga ya faɗi haka ne yayin da yake sanar da matakan da gwamnatin ta samar domin tallafa wa 'yan ƙasa a daidai lokacin da ake fuskantar tsadar farashin fetur a matakin duniya. Farashin fetur dai ya yi tashin gwauron-zabi ne a sakamakon rufe mashigar Hormuz da ke yankin Gabas ta Tsakiya bisa rikicin Amurka da Iran. Da fari, a ranar Alhamis ne Ministan Kuɗi…
Read More