Babaji

5704 Posts

Mutane uku sun rasu bayan cin abinci mai guba a Katsina

Daga BELLO A. BABAJI Mutane uku sun rasu yayin da aka garzaya da ɗaya zuwa asibiti a lokacin da suka ci wani abinci mai ɗauke da guba a garin Magama dake Ƙaramar Hukumar Jibia a Jihar Katsina. Ƙwararre mai sharhi kan daƙile ayyukan ta'addanci, Zagazola Makama ya faɗi hakan a wani sako ta kafar X, ranar Alhamis. Ya ce, mamatan sune Hussaina Ayuba, Ahmed Ayuba, and Nana Ayuba. An garzaya da su Babban Asibitin Jibiya ne a lokacin da suka ci taliya, inda suak rasu jim-kaďan bayan hakan. Ya kuma ce, Hafsat Ayuba mai shekaru 12 tana karɓar magani a…
Read More

Gwamnatin Amurka ta haramta ɗaukar ƴan Nijeriya da wasu ƙasashe a Jami’ar Harvard

Daga BELLO A. BABAJI Gwmanatin Amurka ƙarƙashin jagorancin Shugaba Donald Trump ta dakatar da daukar ƴaƴan Nijeriya da na wasu ƙasashe a Jami'ar Harvard. A ranar Alhamis ne Ofishin harkokin tsaro na cikin gida ya ce an janye bai wa daliban ƙasashen waje guraben karatu a Jami'ar. Haka kuma daliban da suke karatu an ba su zaɓin neman barin makarantar ko kuma a tilasta musu ficewa. Rahotanni sun bayyana cewa, jami'ar ta gaza cika ķa'idar samar da kuɗi na gwamnatin Trump a sakamakon ƙin bada haďin-kai ga buƙatun Shugaban ƙasar. Daga cikin ababen da jami'ar ta ƙi yi akwai rashin…
Read More

Bayan shekaru tara, DSS ta biya diyyar harbin ɗan kasuwa bisa kure a Jos

Daga BELLO A. BABAJI A ƙoƙarinta na cika alķawarin bada magani kyauta ga basakkwacen ɗan kasuwa da aka harba bisa kuskure shekaru tara da suka gabata yayin atisayen jami'an DSS, hukumar ta gayyaci mutumin zuwa asibitinta dake Abuja. A tsakiyar watan Maris ne Darakta-Janar na DSS, Tosin Ajayi ya amince da biyan Naira miliyan 10 a matsayin kuɗin dameji ga ɗan kasuwar bisa umarnin wata kotu shekaru shida da suka gabata. Haka kuma daraktan ya ƙara wa mutumin miliyan N10 na jinkiri da aka samu, wanda ya mayar da jimillar kuɗin zuwa miliyan N20. Ya kuma umarci asibitin da ta…
Read More

INEC ta kafa ɓangaren fasahar AI don inganta zaɓen 2027

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da samar da ofishin fasahar zamani ta AI, wato 'Artificial Intelligence' a ķarķashin ɓangaren kula da bayanan na'ura (ICT). INEC ta sanar da haka ne a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Kwamishinanta na ƙasa kuma Shugaban kwamitin yaɗa labarai da ilimantar da masu zaɓe, Sam Olumekun, ranar Alhamis. Ya ce, an yi hakan ne da nufin amfani da ci-gaban da AI ta kawo domin da magance munanan tasirin fasaha a yayin zaɓuka musamman a na shekarar 2027. Olumekun ya ce, ofishin zai taimaka wa hukumar wajen…
Read More

Tsaro: Abinda mu ke yi wajen ceto Nijeriya – Ribaɗu

Daga BELLO A. BABAJI Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribaɗu, ya ce Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro sun yi nasarar daƙile kaso mai girma na ayyukan ta'addancin da gwamnatin Bola Tinubu ta gada. Ya bayyana cewa, an samu nasarar kawo ƙarshen kisan kiyashi da ɗaiɗaita dukiyoyi da harin ƴan ta'adda akan kadarorin gwamnati ta hanyar haɗaka tsakanin hukumomin tsaro. A lokacin da ya ke magana a taron ƙasa na jiga-jigan Jam'iyyar APC a Abuja, yayin cikar Shugaba Tinubu shekaru biyu akan mulki, Ribaɗu ya ce gwamnatin ta gaji manyan rikici guda biyar a…
Read More

Babu wanda ke juya Tinubu, inji Ministan Labarai

Daga BELLO A. BABAJI Ministan Labarai da Wayar kan Al'umma, Mohammed Idris ya ce, babu wanda ke juya Shugaba Bola Tinubu a yayin gudanar da harkokin mulkinsa. A madadin haka Shugaban ƙasar ya kan yi maraba da shawarwari da dama, sannan sai ya yanke hukunci daidai da maslahar Nijeriya. A sanarwar da mai taimaka masa kan harkar labarai, Rabi'u Ibrahim ya fitar, Ministan ya bayyana hakan ne a Abuja, yayin gabatar da jawabinsa a taron ƙasa na ƴaƴan Jam'iyyar APC da aka yi wa take da 'Renewed Hope Agenda', ranar Alhamis. Ya ce, "Akwai buƙatar ku nazarci Shugaban ƙasar. Za…
Read More

Mutane uku sun rasu yayin da jirgi ya kutsa hanyar gidaje a Amurka

Daga BELLO A. BABAJI Mutane da dama sun rasa rayukansu a lokacin da wani ƙaramin jirgin sama samfurin jet ya yi hatsari a wata hanyar gidaje dake Birnin California tare da lalata gidaje da ƙonewar motoci. Kimanin gidaje goma ne suka ƙone da motoci da dama a yankin, wanda ake kira da San Diego. Hukumar kashe gobara a yankin ta ce suna bincike game da gano adadin mutanen da ke cikin jirgin gami da hakikanin waɗanda suka rasu. Ta kuma ce, a lokacin da hatsarin ya faru, tankin man jirgin ya fashe tare da tarwatsewa zuwa wurare da dama, lamarin…
Read More

2027: Gwamnonin APC 22 sun amince da tsayawar takarar Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI Yayin da ake cigaba da shirye-shiryen fara yaƙin neman zaɓen 2027, gwamnonin APC sun sanar da amincewarsu ga Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar da zai tsaya wa jam'iyyar a zaɓen Shugaban Ƙasa. Sun bayyana hakan ne a yayin taron ƴaƴan jam'iyyar na ƙasa da ya gudana a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja, ranar Alhamis. Shugaban ķungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya tabbatar da hakan a lokacin da ya gabatar da buķatar, inda Uba Sani na jihar Kaduna ya mara masa baya. Lamarin da ya nuna ƙarfin haɗin kan da ke tsaka…
Read More

Hukumar Fina-finai ta Ƙasa ta jajenta rasuwar Shugaban MOPPAN, Umar Maikuďi

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Kula da Fina-finan Nijeriya (NFC), ta bayyana alhininta bisa rashin Alhaji Umar Maikuďi, wanda ɗaya ne daga cikin jiga-jigan harkar fina-finai a Nijeriya. A sanarwar da ta fitar a Jos, hukumar ta koka game da rashin shugaban na ķungiyar masu shirya fina-finai ta ƙasa MOPPAN, duba da gudumawarsa ga ci-gaban harkar fim a Nijeriya musamman ga masana'antar Kannywood. A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Daraktan hulďa da jama'ar hukumar, Brian Etuk, Darakta-Manaja na NFC kuma babban jarumin Kannywood, Dakta Ali Nuhu ya bayyana kaďuwarsa game da rashin, wanda ya ce ya haifar…
Read More

Gwamnan Kaduna ya yi garambawul ga gwamnatinsa da dawo da Ma’aikatar Labarai da El-Rufa’i ya rushe

Daga BELLO A. BABAJI Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya dawo da Ma'aikatar Labarai da aka rushe a lokacin gwamnatin Malam Nasiru El-Rufa'i a jihar. Haka kuma, ya sauya wa Kwamishinan Ilimi, Farfesa Mohammed Sani Bello wajen aiki, inda ya naɗa shi matsayin wanda zai jagoranci ma'aikatar. Gwamnan, ya nada tsohon darakta-janar na Hukumar Makamashi ta Ƙasa kuma tsohon mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara akan makamashi, Farfesa Abubakar Sani Sambo a matsayin Kwamishinan Ilimi. A sanarwar da Sakataren yaɗa labaran gwamnatin jihar, Ibraheem Musa ya fitar, ya ce gwamnan ya kuma naɗa Gloria Ibrahim a mukamin Kwamishinar Ci-gaban…
Read More