Babaji

5704 Posts

Ƙungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa ta jajenta rasuwar Shugaban MOPPAN

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa (AFMAN) reshen jihar Kano, ta miƙa ta'aziyyarta ga rasuwar Shugaban ƙungiyar masu shirya fina-finai ta ƙasa (MOPPAN), Alhamis Umar Maikuďi. Ta jajenwa iyalai, ƴan uwa da abokan arziƙi bisa babban rashin jajirtaccen jagoran, wanda ya bada gagarumar gudumawa ga masana'antar Kannywood da harkar fim a Nijeriya. A sanarwar da ke ɗauke da sanya hannun Sakataren AFMAN, Sharif Mustapha Anwar, ƙungiyar ta kuma yi addu'ar fatan samun rahama a gare shi da ɗaukacin al'umma baki ɗaya.
Read More

Jami’ar Harvard ta maka Trump a kotu bisa hana ta ɗaukar ƴan ƙasashen waje

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a ne Jami'ar Harvard dake Amurka ta shigar da Gwamnatin Shugaba Donald Trump ƙara a kotu, bisa hana ta ɗaukar ďalibai ƴan ƙasashen waje. A ranar Alhamis ne Sakataren harkokin tsaro na cikin gida a Amurka, Kristi Noem ya sanar da haramta wa Jami'ar ɗaukar ďaliban, lamarin da ya jefa dubunnansu shiga mawuyacin hali. Shugaba Trump ya fusata ne da Jami'ar a lokacin da ta yi buris da buƙatarsa game da sauya tsarinta na ɗaukar dalibai karatu da bada ayyukan wucin-gadi. Gwamnatin ta kuma yi barazanar ƙaƙaba wa Jami'ar biyan Dala biliyan 9 na…
Read More

Kwamitin Amitattun MOPPAN ya je ta’aziyyar rasuwar shugaban ƙungiyar

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Asabar ne mambobin kwamitin amitattu na ƙungiyar masu shirya fina-finai (MOPPAN) suka je Zaria domin gabatar da ta'aziyyar rasuwar shugaban ƙungiyar, Alhaji Umar Maikuďi. Tsohon shugaban ƙungiyar, wanda ya samu wakilcin Dakta Ahmad Sarari shi ya gabatar da addu'a a madadin mambobin kwamitin. Kwamitin ya kuma miƙa ta'aziyyar ƙungiyar ga iyalan mamacin bisa babban rashin da aka yi musu tare da fatan samun haƙurin juriyan rashin a gare su.
Read More

JAMB: ‘Yan sanda sun kama mutum 20 bisa zargin kutse a sakamakon jarrabawar UTME

Daga BELLO A. BABAJI Mutane 20 ne aka kama bisa laifin yin kutse ga na'urar jarrabawar UTME ta shekarar 2025 da Hukumar JAMB ta shirya. Jami'an DSS da na ƴan sanda ne suka kama waɗanda ake zargin a Abuja. Ana zargin mutanen suna daga cikin wata ƙungiya da ke da sama da mambobi 100, waɗanda suka ƙware wajen yin kutse ga shafukan jarrabawa da dama da suka haɗa da JAMB da NECO. Majiya daga jami'an tsaro sun ce, waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu da cewa suna da hannu a yin kutse ga ofishin sadarwar CBT domin ɗora wa JAMB…
Read More

Dakarun tsaro sun daƙile harin Boko Haram a sansanin sojoji na Gajibo

Daga BELLO A. BABAJI A daren ranar Alhamis ne jami'an Sojojin Nijeriya a ƙarƙashin atisayen HAƊIN KAI suka kare wani hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a sansanin sojoji dake Ƙauyen Gajibo na Ƙaramar Hukumar Dikwa a Jihar Borno. Mataimakin Daraktan hulďa da jama'a na sojoji shiyya ta 7, Ajemasu Yake Jingina ya bayyana hakan a wata takarda, ranar Juma'a, inda ya ce mayaƙan Boko Haram na ɓangaren Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad (JAS) da ISWAP ne suka kai farmakin da misalin ƙarfe 10:20 na dare. Lamarin da ya ankarar da dakarun sojojin tare da mayar da martani cikin gaggawa…
Read More

Napoli ta lashe kofin Serie A karo na huɗu

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli ta yi nasarar lashe kofin gasar Serie A na ƙasar Italiya bayan doke Cagliari da ci 2 da 0 a ranar Juma'a. Tsofaffin ƴan wasan Manchester United da Chelsea, Scott Mc Tominay da Rumelu Lukaku ne suka zura ķwallayen. Gabannin haka, an aka kai ruwa rana a tsakanin ķungiyar da takwararta, Inter Milan wadda ta bai wa tazara maki ɗaya, lamarin da ya kai Napoli ga nasara a makon ƙarshe na gasar. A gefe guda kuma, ita ma Inter Milan ta doke Como da ci 2 da nema. Wannan shi ne…
Read More

Abuja: Sama da ƴan bindiga 20 sun farmaki rukunin gadajen Efab

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sanda a Abuja, ta tabbatar da aukuwar wani hari da aka kai wa rukunin gadaje na Efab Global Estate da ke Idu a Industrial Area, wanda sama da ƴan bindiga 20 suka gudanar da raunata masu gadi biyar tare da yin fashi a gidaje da dama. Wani shaida ya ce, ƴan fashin sun kai harin ne da tsakiyar dare, inda suka yi ta harbe-harbe domin tsorata al'ummar yankin. Wani mazaunin unguwar ya ce, masu gadi biyar sun samu raunuka yayin da maharan suka yi fashi a gidaje shida, inda suka karɓe wayoyin hannu, kuɗaɗe,…
Read More

Rikicin jam’iyya: Saraki ya jagoranci tawagar PDP zuwa Enugu

Daga BELLO A. BABAJI A ƙoƙarinsu na ɗinke barakar da ta mamaye jam'iyyar PDP, mambobin kwamiti na musamman kan sulhu a ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki sun gana da Gwamnan Jihar Enugu kuma jagoran jam'iyyar a Kudu maso Gabas, Peter Mbah. Sauran mambobin da suka halarci ganawar, wadda aka yi ta cikin sirri a Fadar gwamnatin jihar sun haɗa da tsofaffin gwamnonin jihohin Bayelsa da Gombe, wato Sanata Seriake Dickson da Ibrahim Ɗankwambo. Bayan kammala zaman ne a yayin hira da manema labarai, Saraki ya ce sun yi zama da kwamitin sulhun ne don tabbatar da an…
Read More

Kaduna: Wata mata ta kashe jaririn kishiyarta ɗan wata uku da asid

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sanda a Jihar Kaduna, ta kama wata mata mai suna Zaliha Shu'aibu bisa zargin ta da kashe jaririn abokiyar zaman ta mai watanni uku a Ķauyen Malari dake Ƙaramar Hukumar Soba a jihar. Lamarin ya auku ne a ranar 13 ga watan Mayu, 2025 a gidansu inda ta ke tare da mijinta da kishiyar tata. Kakakin ƴan sandan, Mansir Hassan ne ya faɗi hakan a wata takarda, ranar Juma'a, inda ya ce mahaifiyar jaririn mai suna Maryam Ibrahim, ta bar jaririn ne a lokacin da ta shiga makewayi domin biyan wata buƙata. Bayan ta…
Read More

FCTA ta ƙwace filin Sakatariyar PDP da wasu filaye 4,793 a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Raya Birnin Tarayya (FCTA), ƙarƙashin umarnin Ministan Abuja, Nyesom Wike ta ce daga ranar Litinin za ta karɓe iko da filaye guda 4,794 bisa rashin biyan kuɗaɗen hayar ƙasa na shekaru tsakanin 10 da 43. Daga cikinsu akwai na Sakatariyar jam'iyyar PDP dake birnin, wanda an ƙwace shi tun a watan Maris na wannan shekarar saboda rashin biyan kuɗin haya na shekaru da dama. Mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Lere Olayinka ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai, ranar Juma'a. Ya ce, tuni FCTA ta ƙwace mallakar filayen, waɗanda ke…
Read More