Babaji

5704 Posts

Yanzu-yanzu: Masu zaɓen ɗan takara na Jigawa sun hargitsa zaman haɗakar Atiku da Obi

Daga BELLO A. BABAJI Wani zama na musamman da ya haɗa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Peter Obi na jam'iyyar LP da Rotimi Amaechi da sauransu ya samu tsaiko a lokacin da wasu deliget daga Jihar Jigawa suka hargitsa shi. Ana gudanar da taron haɗakar ne a Otal ɗin Abuja Continenta Hotel dake Birnin Tarayya, wanda ƙungiyar mashawarta kan harkar siyasa ta ƙasa reshen Arewa ta shirya. An samu matsala ne a lokacin da aka kasa cimma matsaya game da batun wakilci daga Jihar Jigawa a lokacin da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal ya umarci wani da…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Alonso ya gaji Ancelotti a matsayin kocin Real Madrid

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta tabbatar da Xabi Alonso a matsayin sabon kociyanta. Tsohon ɗan wasan na Sifaniya da Real Madrid ya dawo Saniago Bernabéu ne a matsayin babban mai horarwa bisa yarjejeniyar kwantaragin shekara uku. A ranar 1 ga watan Yuni, 2025 ne wa'adin kwantaragin zai fara aiki, inda zai ƙare ranar 30 ga Yunin 2028. Naďin Alonso zai fara aiki ne a nan take inda zai fara da jagorantar ƙungiyar a wasannin ƙungiyoyin ƙasashen duniya, wato Club World Cup, wanda za a fara a ranar 14 ga watan Yuni a Amurka. Alonso,…
Read More

Ku kula da ƴan damfara, har yanzu ba a fara sayar da gidajen da aka ƙwace a hannun Emefiele ba – Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI Ma'aikatar Gine-gine da Raya Birane ta ce ba ta fara sayar da kowane sashi na rukunin gidaje guda 753 da aka ƙwace ba, wanda aka alaƙanta shi da tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele. A sanarwar da Daraktan yaɗa labaranta, Badamasi Haiba ya fitar, Ma'aikatar ta ce kaɗai abinda ta yi shi ne karɓar iko da shi daga hannun hukumar EFCC a ƙarƙashin umarnin Shugaba Bola Tinubu. Hakan ya biyo bayan samun labarin waɗansu ɓata-gari ne da ke karɓar kuɗi a hannu mutane da sunan sayar da wasu ɓangarori na rukunin gidajen. Ya ce,…
Read More

Za mu haɗu a kotu domin tabbatar da gaskiya – lauyoyin Natasha ga Gwamnati

Daga BELLO A. BABAJI Lauyoyin Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan sun tabbatar da samun bayanan ƙarar da Gwamnatin Tarayya ta shigar akanta bisa rikicin rikicinta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, inda suka ce za su gabatar da hujjojinsu a lokacin da ya dace. A sanarwar da Dakta Ehiogie West - Idahosa, SAN ya fitar a ranar Asabar, lauyoyin kuma sun nemi al'umma da su sanya su acikin addu'o'insu gami da na su goyon baya. Ya ce, tawagar alķalan waɗanda suke karewa za ta shirya dukkan wata hujja da ake buƙata domin kare ababen da ake tuhumar wadda suke…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: JAMB ta fitar da sakamakon ɗaliban da suka sake rubuta jarrabawa

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Haɗaka ta bada Gurbin Karatu ga Ɗalibai (JAMB) ta fitar da sakamakon jarrabawa ga ďaliban da suka sake rubutawa bayan tsaikon da aka samu a karon farko. A wata sanarwa daga jami'in hulďa da jama'arta, Fabian Benjamin, ranar Lahadi, hukumar ta kuma bankaɗo wasu ayyukan satar jarrabawar daga ďalibai da wasu cibiyoyin jarrabawa. Ya kuma ce, daga cikin ďalibai 336,845 da aka sake shirya musu jarrabawar, guda 21,082 ba su je rubutawa ba. A watan da ya gabata ne aka rubuta jarrabawar ta zangon 2025, inda aka samu tsaiko daga ɓangaren sadarwa musamman a yankin…
Read More

Tinubu ya bai wa Nnamani, Anyim, Shema, Barkiya da wasu 18 muƙamai

Daga BELLO A. BABAJI A ƙoƙarinsa na ƙarfafawa da inganta ayyuka, Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗa mutane 22 a wasu manyan muƙamai a Hukumomin Tarayya. Daga cikinsu akwai sanannun jiga-jigan ƴan Jam'iyyar APC da suka haɗa da tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Ken Nnamani; tsohon Sakataren gwamnati (SGF), Anyim Pius Anyim da tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema. An naɗa Nnamani ne a matsayin Shugaban Cibiyar Nazarin Tsare-tsare ta Ƙasa (NIPSS), yayin da aka naɗa Shema a matsayin Shugaban Hukumar Ci-gaban Birni, FCDA. Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Edo, Philip Shaibu kuwa, zai riƙe Darakta-Janar na Cibiyar Harkokin Wasanni,…
Read More

Tawagar matan Arsenal ta lashe Champions League makonni biyu da cire mazansu a irin gasar

Daga BELLO A. BABAJI Biyo bayan doke mai riƙe da kofin, Barcelona da ci 1 da 0, tawagar mata ta ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta lashe kofin gwarazan Nahiyar Turai, wato UEFA Women's Champions League a karo na biyu. An buga wasan na ƙarshe ne a Filin Estádio José Alvalade dake Birnin Lisbon a ƙasar Portugal 🇵🇹. Ƴar wasa Stina Blackstenius ce wadda ta zura ƙwallon a minti na 74, lamarin da ya bai wa Arsenal nasarar lashe kofin tun bayan da ta lashe a shekarar 2007 lokacin da ake kiran sa da UEFA Women's Cup. Ƙungiyar Barcelona ce…
Read More

Su Shekarau na son a yi kama-kama a sauke Tinubu a 2027

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar ƴan demokraďiyya ta Arewacin Nijeriya, wato The League of Northern Democrats (LND) ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ta yanke shawarar goyon bayan haɗakar ƴan ɓangaren adawa domin sauke Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027. Ƙungiyar ta ƙunshi sanannun jagororin ƴan siyasa, malamai da ƴan kasuwa daga Arewacin Nijeriya, wadda ta bayyana matsayarta a yayin wani zama da ta gudanar, ranar Alhamis. A sanarwar da fitar, kamar yadda ɗaya daga cikin mambobinta, Umar Ardo ya karanto, LND ta ce aƙalla mutane 147 ne suka halarci taron cimma matsayar goyon bayan haɗakar a ƙarƙashin…
Read More

Kurkukun Abuja: An sallami ƴan Shi’a 56, an kama 33 da laifi – Hukuma

Daga BELLO A. BABAJI Mai shari'a Husseini Baba Yusuf na Babbar Kotun Tarayya ya sallami fursunoni guda 56 daga gidajen yari biyu a ƙarƙashin Hukumar kula da Gidajen Yari ta ƙasa (NCoS) reshen Birnin Tarayya Abuja. Kakakin NCos na Abuja, Samson Duza ya bayyana hakan a wata takarda, ranar Alhamis, inda ya ce 30 daga ciki an tsare su ne a kurkukun Kuje yayin da aka tsare sauran a kurkukun Suleja. A yayin wani hukunci kuma, Alkali Belgore ya jagoranci sauraron ƙarar wasu mambobin ƙungiyar Shi'a (IMN) guda 58 da aka tsare da gidan yarin Kuje, inda aka sallami 25…
Read More

2027: Ba ni da burin tsaya wa takarar shugaban ƙasa, inji Yahaya Bello

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a ne tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ba zai tsaya takarar shugaban ƙasa ba a babban zaɓe na 2027 saboda ba shi da burin hakan. A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Daraktan yaɗa labaransa, Michael Ohiare, Yahaya Bello ya ce ya yi mamakin ganin wani bidiyo na gangaminsa dacke yawo wand tun a shekarar 2022 aka yi, inda ake yaɗa shi da sunan zai yi takara a matsayin abokin karawar Shugaba Bola Tinubu. Ya kuma ce, duk da kalubalen da ake fuskanta a duniya, Shugaban ƙasar da ƴan…
Read More