Babaji

5704 Posts

Da Ɗumi-Ɗumi: Jami’an FCTA sun rufe Hedikwatar PDP

Daga BELLO A. BABAJI Da misalin ƙarfe 2:05 na ranar Litinin ne jami'an Hukumar Kula da Birnin Tarayya (FCTA) suka rufe Hedikwatar babbar jam'iyyar adawa, PDP dake yankin Wuse a Abuja. A ranar Juma'a ne rahotanni suka bayyana cewa, FCTA a ƙarƙashin umarnin Ministan Abuja, Nyesom Wike za ta fara ƙwace filaye daga ranar Litinin, wato yau, a sakamakon rashin biyan kuɗaɗen hayar ƙasa na shekaru tsakanin 10 da 43. Filin Hedikwatar PDP yana ɗaya daga cikin wuraren da aka zayyano, wanda a watan Maris, 2025 ne aka ƙwace shi saboda rashin biyan kuɗin hayar ƙasa. A yayin ganawa da…
Read More

Yanzu-yanzu: An yanke wa wanda ya cinna wa masallaci wuta a Kano hukuncin rataya

Daga BELLO A. BABAJI Wata Babbar Kotun Shari'a a Kano ta yanke wa Shafi'u Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa cinna wa masallata wuta a wani masallaci dake Ƙauyen Gadan a Ƙaramar Hukumar Gezawa ta jihar. Lamarin ya auku ne a lokacin da wasu mutane ke tsaka da yin sallar Asuba a ranar 15 ga watan Mayu, 2024. Kimanin mutane 11 ne suka rasa rayukansu a yayin karɓar magani a Asibitin Murtala Muhammed. Alƙali Halhatu Huza'i Zakariya, a lokacin da aka gurfanar da Abubakar, ya yanke masa hukuncin ne, bayan samun sa da laifuka huɗu da ake tuhumar sa…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Wakilai ta janye ƙudirin neman wajabta zaɓe bayan al’umma ta koka

Daga BELLO A. BABAJI Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya janye ƙudirin da ke neman a wajabta wa al'umma kaɗa kuri'a a lokutan zaɓe. Kakakin majalisar da ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Bassa/Jos (Filato), Daniel Ago ne suka ɗauki nauyin ƙudirin. Saidai, a yayin zaman majalisar na ranar Litinin, bayan samun ƙorafe-ƙorafen al'umma game da kaďuwa da suka nuna a kai, majalisar ta yanke hukuncin janye ƙudirin. A sanarwar da mai taimaka wa Kakakin akan harkar labarai, Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Abbas ya ce an gabatar da ƙudirin ne da nufin faɗaɗa adadin masu zaɓe duba da ƙarancinsa…
Read More

PDP ta ɗage zaman majalisar zartarwarta bisa rashin tabbas akan Atiku da Wike

Daga BELLO A. BABAJI Babbar Jam’iyyar adawa (PDP) ta sanar da ɗage taron majalisar zartarwarta karo na 99 duba da yiwuwar ofishin yanke hukunci zai ɗauki mataki akan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Ministan Abuja, Nyesom Wike. Da farko, an shirya gudanar zaman ne a gobe Talata, kana daga bisani aka ɗage shi domin bai wa kwamitin sulhu ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki damar yin aikinsa. A saƙon da Sakataren jam'iyyar na Ƙasa, Samuel Anyanwu ya fitar, ya ce za a sanar da sanya wata ranar taron daga baya kamar yadda dokar jam'iyyar ta tanadar.…
Read More

Abuja: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da dama yayin hari a wani rukunin gadaje

Daga BELLO A. BABAJI Wasu gungun ƴan bindiga sun kai farmaki a Rukunin Gidaje na Grow Homes Estate dake yankin Chikakore a Kubwa, Abuja, inda suka tsare mazauna na sama da sa'a guda. Wani mazaunin yankin ya ce, lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 12:00 zuwa 1:30 na daren Litinin. Ɗaya daga cikin ƴan unguwar ya bayyana cewa ya shaidi lokacin da ƴan bindigar suka yi garkuwa da wani mutum da wata mata. Saidai, bayan gari ya waye an samu matar a rukunin gidajen bayan sako ta da ƴan bindigar suka yi ba tare da sanin dalilin yin hakan…
Read More

Sojojin sama sun tarwatsa haramtattun wuraren tace mai sama da 100 a wata biyar

Daga BELLO A. BABAJI A wani yunƙuri na yaƙi da satar ɗanyen mai da lalata muhalli, Rundunar Sojojin Sama (NAF) ta tarwatsa haramtattun wuraren tace ɗanyen mai guda 100 a yankin Neja-Delta cikin watanni biyar da suka gabata. A yayin atisayen sojojin sama ƙarƙashin dakarun 'Operation DELTA SAFE' (OPDS) aka samu nasarar daƙile manyan laifukan domin kare albarkatun mai daga shiga hannun ɓata-gari gami da tseratar da ƙashin bayan tattalin arziƙin Nijeriya daga faɗawa cikin mawuyacin hali. Daraktan yaɗa labaran NAF, Ehimen Ejodame a wata takarda, ya bayyana cewa jami'an '115 Special Operations Group' ne suka gudanar da atisayen, wanda…
Read More

NCC ta umarci kamfanonin kiran waya su biya kwastomomi diyya bisa ɗaukewar sabis na sama da kwana ɗaya

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, NCC, ta yi aiken sabon umarni ga kamfanonin telekom da su riƙa biyan kwastomomi diyya a duk lokacin da aka samu ɗaukewar sabis na sama da sa'o'i 24. A ranar Lahadi hukumar ta bayyana hakan a wata takarda, inda ta ce wajibi ne a biya diyya ga dukkan kwastomomin da irin hakan ya shafa gami da faɗaɗa wa'adin sabis bisa la'akari da kiyaye dokar bai wa kwastomomi kariya. Sabuwar dokar ta shafi masu gudanar da harkokin sabis na wayoyin kira, masu samar da sabis na yanar gizo da kuma sauran masu isar…
Read More

Ba biza, ba shiga: Gwamnatin Tarayya ta haramta wa ƴan ƙasashe takwas shigowa ba tare da sahihan takardu ba

Daga BELLO A. BABAJI Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya ce Gwamnatin Tarayya ta haramta wa ƙasashe takwas shigowa Nijeriya a makon da ya gabata sakamakon samun su da bizozin da suka tashi daga aiki. Dakta Tunji-Ojo ya bayyana hakan ne a yayin hira da tashar TVC a daren ranar Lahad inda ya ce ma'aikatar ba za ta sake amincewa da shigowar ƴan ƙasashen waje ba ba tare da cika ƙa'ida ba. Ya kuma ce, ya gana da wakilan kamfanonin jiragen sama a ranar Juma'a, inda ya tattauna da su akan sababbin matakai da aka bijiro da su…
Read More

Haƙar Ma’adanai: Gwamnatin Tinubu ta samu sama da Dala miliyan 800 na hannun-jari daga waje – Minista

Daga BELLO A. BABAJI A ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ɓangaren haƙar ma’adinai a Nijeriya ya samu gagarumar nasara, wanda Ministan Raya Ma’adinai, Dakta Dele Alake, ya bayyana a matsayin “ci-gaba mafi girma da aka taɓa samu a tarihin Najeriya” a fannin. A cewar Ministan, kuɗaɗen shiga daga harkar ma’adinai sun ƙaru daga Naira biliyan 6 a baya zuwa biliyan N38 a shekarar 2024, hakan ya kai ninki shida cikin shekara guda. Ci-gaban ya biyo bayan sabbin matakai ne da aka kafa, waɗanda suka haɗa da tsauraran sharuddan bayar da lasisi da kuma wajabcin sarrafa ma’adanai a cikin gida…
Read More

Rikicin PDP ya yi ƙamari bayan Wike ya janye daga sulhu

Daga BELLO A. BABAJI Rikicin jam'iyyar PDP ya ɗumi a ranar Lahadi a yayin da Ministan Abuja, Nyesom Wike ya fice daga yarjejeniyar sulhun da aka cimma a tsakanin ƴaƴanta. Wike ya zargi Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde kan zama sababi na matsalolin da suka dabaibaye jam'iyyar, inda ya ce gwamnan ba ya bin ka'idodin yarjejeniyar da aka gindaya. A sanarwar da ya fitar, Wike ya zargi jagororin jam'iyyar waɗanda suka haɗa da Gwamnan Enugu, Peter Mbah da butulci da rashin gaskiya gami da karya ka'idodin sulhu. Ministan na Abuja, wanda tsohon gwamnan Ribas ne kuma ɗaya daga cikin ƙungiyar…
Read More