Babaji

5704 Posts

NiMET ta yi hasashen mamakon ruwan sama na kwana uku a Abuja, Kaduna da wasu jihohi 12

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Kula da Yanayi (NiMET) ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a jihohi guda 14 a Nijeriya har na tsawon kwana uku. Jihohin sune Bayelsa, Ribas, Delta, Ondo, Edo, Akwa-Ibom, Kuros-Riba, Imo, Abia, Abuja, Kaduna, Nasarawa, Kogi da Neja. Ranakun sune daga Laraba, 28 zuwa Juma'a, 30 ga watan Mayu. Ta kuma ce, akwai yiwuwar a samu iska a yayin ruwan saman gami da ambaliya a wasu yankunan. Haka kuma ta shawarci jama'a da kada su yi zirga-zirga a yankunan da ruwa ke taruwa, waɗanda akwai yiwuwar su haddasa ambaliya ko cinkoson ababen hawa.
Read More

Kotu ta umarci El-Rufa’i biyan diyyar miliyan N900 kan tsare manyan Adara ba bisa doka ba

Daga BELLO A. BABAJI Wata Babbar Kotun Tarayya a Kaduna ta umarci tsohon gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufa'i da wasu mutane biyar da su biya Naira miliyan 900 a matsayin kuɗin diyya na tsare wasu jagororin Adara a shekarar 2019 ba bisa ƙa'ida ba, wanda hakan tauye musu ƴancin ɗan-adam ne. Alƙali Hauwa'u Buhari ta gabatar da hukuncin a yayin shari'ar da wani Awemi Dio Maisamari da wasu mutane takwas na ƙabilar Adara daga Kudancin Kaduna suka shigar, ranar Talata. Kotun ta ce, El-Rufa'i ya kama su ne bisa wani shiri na raɗin kansa, don haka zai biya diyyar miliyan…
Read More

An ga watan Dhul Hijjah, za yi babbar sallah ranar 6 ga Yuni

Daga BELLO A. BABAJI Hukumomin Saudiyya sun tabbatar da ganin watan 12 a kalandar musulunci, wato Dhul Hijjah. Hakan ya nuna cewa za a yi salla babba a ranar 6 ga watan Yuni yayin da za a yi hawan arfa a ranar 5 ga wata. Kotun Koli, ta sanar da hakan a ranar Talata, kamar yadda aka ruwaito a labaran Arab News. Al'ummar musulmi da ke aikin hajji a wannan shekarar za su yi sallar Eid-el-Kabir a ranar 6 ga wata. Haka kuma masarauta Saudiyya ta bada hutu ga ma'aikatan gwamnati da na ma'aikatu masu zaman kansu.
Read More

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’ar FRSC a Filato

Daga BELLO A. BABAJI Rahotanni daga Jos, Babban Birnin Filato, sun bayyana cewa wata jami'ar Hukumar Kiyaye Haɗurra (FRSC) mai suna Kate Jonathan Akpabio ta shiga hannun ƴan bindiga a Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu dake jihar. A wata sanarwa da mai sharhi kan harkar tsaro, Zagazola Makama ya wallafa ta kafar X, ranar Talata, ya ce lamarin ya auku ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 5:30 na safe, a lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai farmaki gidanta dake yankin Rantya, inda suka tafi da ita. Daga lokacin ne aka kira jami'an tsaro domin sanar da su faruwar…
Read More

Tinubu ya amince da sauya Federal Polytechnic Kabo zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kabo

Daga BELLO A. BABAJI Sanata Barau ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa amincewa da ƙudirinsa na mayar da makarantar Federal Polytechnic Kabo, dake Kano zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kabo. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bayyana godiyarsa ga Shugaba Tinubu, bisa amincewarsa da ƙudirin da ya gabatar a Majalisa na sauya Federal Polytechnic Kabo zuwa Federal University of Science and Technology, Kabo a Jihar Kano. Amincewar ta zo ne cikin wata wasika da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya aikewa Majalisar Dattawa a safiyar yau, wadda shugaban Majalisar Godswill Obot Akpabio ya karanta…
Read More

Ekiti: An yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai bisa lalata da ƴar matarsa

Daga BELLO A. BABAJI Wata Babbar Kotu a Ado Ekiti ta yanke wa wani Jayeoba Oluwafemi hukuncin ɗaurin rai-da-rai bisa lalata da wata ƴar shekara 14, wadda ƴar matar da ya ke aure ne. Mutumin, mai shekaru 56, an gurfanar da shi ne a ranar 4 ga watan Disambar 2020 bisa tuhumar sa da aikata lalata da ƴar shekara 14 wanda yin hakan saɓa wa sashe na 31 ga dokar kare ƴancin ƴaƴa ta jihar ta 2012. Yarinyar, wadda ƴar aji shida ce a makarantar firamare, a yayin bada ba'asi a kotun, ta ce mutum bayan ya auri matafiyarta, ya…
Read More

Babu ƙaramar hukumar da za ta sake shiga hannun Boko Haram, inji Zulum

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi ikirarin cewa babu wata ƙaramar hukuma a jihar da za a sake bari ta faɗa hannun mayaƙan Boko Haram ko ISWAP duk da sake farfaďowar barazanar tsaro a shiyyar Arewa maso Gabas. Zulum ya faɗi hakan ne a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai jim-kaďan bayan zama da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja. Ya bayyana cewa, duba da haďin-gwiwa da ake samu a tsakanin sojoji da hukumomin al'umma da ƙauyuka a jihar, hakan zai taimaka wajen magance ayyukan mayaƙan. "In Allah ya yarda…
Read More

Abuja: Sojoji sun tabbatar da tarwatsewar abin fashewa a Barikin Mogadishu

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar Sojojin ƙasa ta tabbatar da rahoton tarwatsewar wani abin fashewa a barikin sojoji na Mogadishu dake birnin tarayya Abuja. A sanarwar da ta fitar ta kafar X, ta ce lamarin ya auku ne a wajen tsayawar motoci dake daura da barikin. Ta kuma ce, tuni aka ɗauki matakan da suka dace. Rundunar ta ƙara da cewa, za ta fitar da sauran bayanai da zarar an kammala bincike.
Read More

Saudiyya ta koro Sheikh Gumi bayan hana shi yin aikin hajjin bana

Daga BELLO A. BABAJI Sanannen malamin addinin Musulunci a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa, hukumomin Saudiyya sun hana shi gudanar da aikin hajji duk da cewa yana da biza. A wani saƙo daga shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, babban malamin ya ce yana ganin ra'ayoyinsa akan harkokin siyasar duniya sun taimaka wa hukumomin ɗaukar matakin akansa. Ya ce, ya yi abinda ya ke wajibi akansa ta hanyar da aka shar'anta kuma tuni ya dawo gida Nijeriya, yana mai kafa hujja da ayar Al'ƙu'rani. Sheikh Gumi ya kuma yaba wa hukumomin Nijeriya, waɗanda ya ce sun shiga tsakani…
Read More

Ƙungiyar furodusoshin Nijeriya ta jajenta rasuwar Shugaban MOPPAN, Maikuɗi Cashman

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Furodusoshin Nijeriya (AMP) ta yi jimamin rasuwar Umar Maikuďi, Shugaban Ƙungiyar masu shirya fina-finai ta ƙasa (MOPPAN). AMP ta ce, rashin jagoran ƙungiyar babban giɓi ne ga ci-gaban harkar fina-finai a Nijeriya duba da irirn gudumawar da ya bayar a lokacin da ya ke raye. A sanarwar da Shugabar ƙungiyar, Dakta Queen Blessing Ebigieson ta fitar a ranar Litinin, ƙungiyar ta miƙa saƙon ta'aziyyarta ga iyalai da ƴan uwa da abokan arziƙi gami da mambobin MOPPAN bisa babban rashin. Ta kuma yi addu'ar Allah Ya yafe masa kurakuransa gami da sanya shi a Aljannar Firdausi.…
Read More