30
May
Daga MUHAMMAD AL'AMIN a Damaturu A daidai lokacin da ya ke cika Shekaru shidda a karagar mulkin Jihar Yobe, Gwamna Mai Mala Buni, a ranar Alhamis ya gudanar da taron ji kai tsaye daga bakin al'ummar jihar, domin amsa tambayoyi da tsokacin jama'a dangane da ayyuka da manufofin gwamnatinsa. Gwamnan ya ɗauki awanni yana amsa tambayoyi tare da tsokaci dangane da nasarorin da ya samu a cikin wannan tsakani, a fannonin harkokin ilimi, kiwon lafiya, abubuwan more rayuwa, tare da uwa uba, wato harkar tsaro. Taron ya gudana a babban dakin taro na gidan gwamnatin jihar (Banquet Hall) dake Damaturu,…
