31
May
Daga BELLO A. BABAJI Kwamitin Majalisar Wakilai kan Ilimi a matakin farko da hukumomin jarrabawa ya ƙi sauraron tawaga daga Majalisar Kula da jarrabawa a yammacin Afirka (WAEC), ranar Juma'a. Ƴan Majalisar sun ce shugaban WAEC na ƙasa ne kaɗai zai iya bada amsar tambayoyi game da matsalolin da ake samu a jarrabawar da ke gudana a yanzu. Kwamitin ya bai wa WAEC sa'o'i 24 na ya amsa umarninsa na ya bayyana a gabansa a ƴan kwanakin nan. Tawagar WAEC ƙarƙashin jagorancin babban mataimakin rajistira, Ambrose Okelezo ya bayyana cewa shugaban yana halin sanya ido ga harkokin jarrabawa sannan a…
