Babaji

5703 Posts

Yadda Akpabio ya nemi na karɓo masa cin hanci daga ministoci – Natasha

Daga BELLO A. BABAJI Sanatar da aka dakatar daga Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi zargin cewa Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya buƙaci da ta razana ministoci da jagororin hukumomi da nufin ya samu cin-hanci da wasu alfarma domin amfanin kansa. A yayin hira da wata ƴar jarida kuma ƴar Nijeriya da ke zaune a Amurka, Adeola Fayehun, Natasha ta ce lallai akwai salon tursasawa a majalisar, tana bada misali da kasancewar ta shugabar kwamitin albarkatun cikin gida wanda aka yi yunƙurin amfani da shi wajen tatsar ma'aikatu da hukumomi ciki har da ministan man fetur da Gas da kuma…
Read More

An ƙara Yoruba cikin jaddawalin yarukan da za a fassara huɗubar Arafa da su

Daga BELLO A. BABAJI Hukumomin Saudiyya sun sanya yaren Yarbanci acikin jaddawalin yaruka 34 da za a fassara huɗubar ranar Arfa da su a yayin aikin hajjin 2025/1446. Haka ma akwai yaren Fullanci (Fula) da Hausa, waɗanda manyan yaruka ne da ake amfani da su a Nijeriya. Ma'aikatar harkokin addinin a Makkah da Madina ta sanar da hakan a wata takarda a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar Harkokin Addini, Dakta Abdulrahman Al-Sudais, ranar Alhamis. Ya ce, an yi hakan ne da nufin isar da saƙon huɗubar zuwa ga mutane aƙalla miliyan biyar a faɗin duniya. Ya kuma ce, fadar shugabancin ƙasar…
Read More

Cikar shekaru biyu: Tinubu ya ƙaddamar da zangon farko na babban titin Legas zuwa Kalaba da wasu ayyuka

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta cigaba da inganta al'amuran ƙasa da amfani da fasahar zamani gami da inganta al'umma a yayin da ya ƙaddamar da zangon farkon na aikin babban titin 'Lagos-Calabar' da wasu muhimman ayyukan tituna a ƙasar. A yayin taron ƙaddamarwar a Legas ranar Asabar ne Shugaba Tinubu ya umarci Ministan Ayyuka, Dave Umahi da wasu ministoci da su sanya ido akan ayyukan tituna a faɗin ƙasar don tabbatar da an bi dokoki da tsare-tsaren aikin. Ya ce, gwamnatin ba za ta sake biyan diyya ga kamfanonin gine-ginen tituna da ba…
Read More

Super Eagles ta lashe Unity Cup na 2025

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles ta yi nasarar doke Reggae boys na ƙasar Jamaica, inda ta lashe kofin gasar Unity Cup da aka yi a Ingila, ranar Asabar. Moses Simon na Nijeriya shi ya fara zura ƙwallo a minti na 9, a yayin da Dixon na Jamaica ya farke a minti na 12. Daga bisani Samuel Chukwueze a minti na 53 ya ƙara ƙwallo a raga, inda minti goma bayan haka ne sai Russell ya farke wa Jamaica a karo na biyu. Bayan tashi a haka ne sai aka yi bugun fenareti, wanda ya bai…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: PSG ta lashe Champions League

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint Germain ta yi nasarar lashe kofin gasar zakarun Nahiyar Turai, wato UEFA Champions League na kakar 2024/2025. Hakan ya biyo bayan lallasa Inter Milan ta ƙasar Italiya da ta yi da ci 5 da 0 a wasan ƙarshe. Wannan shi ne karo na farko da PSG ta taɓa lashe gasar tun bayan kafuwarta a watan Agustan shekarar 1970.
Read More

Tinubu ya ƙarfafa sojoji da kayan aiki don bunƙasa tsaro a ruwa

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da jiragen ruwa guda uku na sojojin ruwa, wato NNS SHERE, NNS FARO da NNS IKOGOSI, sai kuma helikwafta uku ƙirar AW109 Trekker masu lambobi kamar haka; 501, 502 da 503. A lokacin da ya ke magana yayin ƙaddamarwar a Legas, ranar Asabar, Tinubu ya ce sun ƙara jiragen sintirin ne domin tabbatar da bai wa yankunan ruwan Nijeriya tsaro yadda ya dace. Tinubu, wanda Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya wakilce shi, ya ce yankunan tekunan Nijeriya ginshiƙi ne na nasarori ga harkokin tattali. Sannan, ya bayyana cewa sama da…
Read More

Abinda ya sa na ƙi zaɓar Tinubu da yi masa aiki – Amaechi

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon Gwamnan jihar Ribas kuma Ministan Sufuri sau biyu, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa ya ƙi zaɓe ko aiki wa Shugaba Bola Tinubu ne saboda ya gamsu cewa ba zai jagoranci Nijeriya ba. Amaechi ya bayyana hakan ne a yayin lakcar bikin cikarsa shekaru 60 a duniya, wanda aka yi a Abuja inda ya ce ya haɗu Tibubu a Yola, sai ya ce masa "ba zan yi ma ka aiki ba kuma ba zan zaɓe ka ba." Ya ce, mutane suna cewa bai yi wa jam'iyyar APC ko PDP aiki ba, wanda ya ce hakan ya…
Read More

Wani shugaban ƙasa ya tsallake rijiya da baya bayan jirginsa ya karci ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI Kamfanonin Jiragen Sama da dama sun dakatar da tafiyar shiga Laberiya biyo bayan tsaikon da wani jirgin mai tashin angulu da ke ɗauke da Shugaba Joseph Nyuma ya samu, inda ya kusa kartar ƙasa a filin jiragen sama na Roberts (RIA), ranar Alhamis. Kamfanonin Kenyan Airways, Air Peace da wasu da suka shirya sauka a Monrovia a ranar, sun dakatar da ayyuka a yayin da hukumomi ke ƙoƙarin shawo kan matsalar. Muryoyi daga filin jirgin sun ce, jirgin ya samu tsaiko ne a lokacin da ɗaya daga cikin tayoyinsa ya fashe a yayin da ya ke…
Read More

Yadda rashin tsaro ya shafi ƴan Nijeriya miliyan 150 – Ribaɗu

Daga BELLO A. BABAJI Kimanin ƴan Nijeriya miliyan 120 zuwa 150 ne al'amarin taɓarɓarewar tsaro ya shafa a ƙasar, kamar yadda Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu ya bayyana a ranar Juma'a. Ya faɗi haka ne a Abuja, yayin sanya hannu a yarjejeniyar MoU tsakaninsu Cibiyar Daƙile Ayyukan Ta'addanci ta Ƙasa da Cibiyar Kula da Harkokin Noma a Yankuna masu Sahara ta Ķasa-da-ƙasa. An ƙulla yarjejeniyar ne da nufin raya kasuwancin harkokin noma da inganta rayukan al'ummar da ke rayuwa a yankunan da ke fama da matsanancin rashin tsaro. Ribaɗu ya ce, ta'addanci abu…
Read More

An kashe kwamandan Boko Haram, Abu Fatima da aka sanya ladar miliyan N10 akansa

Daga BELLO A. BABAJI Dakarun sojoji sun yi nasarar kashe kwamandan mayaƙan Boko Haram da ISWAP, wato Ami Abu Fatima, wanda akwai ladar Naira miliyan 10 akansa. An hallaka shi ne a yayin wani atisayen jami'an a yankin Kukawa na Jihar Borno, kamar yadda rundunar sojoji ta wallafa a shafinta na X. A ranar Alhamis ne aka gudanar da atisayen a ƙarƙashin tawagar 'Operation HAƊIN KAI' bayan samun bayanan sirri game da zirga-zirgar ƴan ta'adda a yankin. A yayin haka ne rundunar ta ce, jami'anta na musamman suka hallaka Abu Fatima da mataimakinsa gami da wasu gomman ƙwararrun mayaƙan ƴan…
Read More