Babaji

5703 Posts

Ambaliyar Mokwa: Mutanen da iftila’in ya rutsa da su sun koka da ƙarancin abinci da rashin kyan sansani

Daga BELLO A. BABAJI Kwanaki uku da aukuwar iftila'in ambaliyar ruwan sama a ƙauyuka da dama na Ƙaramar Hukumar Mokwa a Jihar Neja, mutanen da lamarin ya shafa sun koka game da halin da suka tsinci kawunansu a ciki a sansanonin da aka ware musu. Sun bayyana cewa, ba su da wadatattun abinci da kuma ingancin wajen zama a wuraren da aka ba su mafaka. Da dama daga cikin waɗanda iftila'in ya ɗaiɗaita sun ce, duk da cewa hukumomi sun ɗauki hotunansu a lokacin da su ke tare da kayan abinci, hakan bai sa an ba su ba. Ɗaya daga…
Read More

Yunwarka ta mulki ce ba abinci ba – Wike ga Amaechi

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Litinin ne Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bada amsa ga kalamai akan yunwa na tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi. A wata hira da manema labarai a Abuja, Wike ya ce Amaechi ba zai iya zama ba mulki ba, sannan kalamansa na yunwa rainin hankali ne ga ƴan Nijeriya. Ya ce, duk da cewa ya riƙe muƙamai da dama na tsawon sama da shekaru 20, hakan bai sa ya ji shakkar furta cewa yana jin yunwar abinci ba shekara biyu rak ba tare da wani muƙami ba. Wike da Amaechi ƴan siyasa ne da suka…
Read More

MOPPAN ta karrama Gwamnan Kebbi bisa bai wa ƴan Kannywood muƙamai

Daga BELLO A. BABAJI Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya Fina-finai ta Ƙasa (MOPPAN) tare da haɗin-gwiwar reshenta na Jihar Kebbi, ta Karrama Gwamnan jihar, Dakta Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) kan bai wa mawaƙa da wasu ƴan harkar masana'antar fina-finai guda 100 muƙaman masu taimaka masa, wato SA's. Kakakinta, Ibrahim Amarawa a wata sanarwa ya ce lambar yabon da aka bai wa gwamnan wani ɓangare ne na ƙoƙarin shugabancin MOPPAN wanda zai ƙara ɗaukaka martabar ƙungiyar a idon shugabanni da al’umma. Haka kuma ya ce, taron karramawar ya yi nasarar samun halartar jagororin MOPPAN daga jihar. Sannan, hakan ya nuna cewa ƙungiyar…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnati ta ayyana 6 da 9 ga Yuni a matsayin lokacin hutun Babbar Salla

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun 6 da 9 ga watan Yuni, 2025 a matsayin lokutan hutu domin gudanar da hidimar Eid-ul-Adha, wato babbar Salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana hakan a madadinta, inda ya kuma taya ɗaukacin al'ummar musulmi a gida da waje murnar zagayowar lokacin. A sanarwar da Babbar Sakatariyar Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, Dakta Magdalene Ajani ta fitar, Ministan ya yi kira ga al'ummar musulmi da su cigaba da bin karantarwar addinin wajen sadaukarwa da tsayuwa akan imani musamman a koyi da Annabi Ibrahim (AS) da kuma amfani da lokacin…
Read More

Hukumomin Saudiyya sun gabatar da sabbin matakan kariya bayan matakin zafi ya haura digiri 50

Muslim pilgrims join one of the hajj rituals on Mount Arafat near Mecca early on Sunday. Daga BELLO A. BABAJI Ma'aikatar Hajji ta Saudiyya fitar da sababbin matakan kariya ga masu aikin hajji, inda ta yi kira a gare su da su kiyaye halin da ake ciki duba da tsananin zafi da ake fama da shi. Hakan na zuwa ne a yayin da matakin zafi a ƙasar ya haura digiri 50 domin tabbatar da kammala aikin hajjin cikin lumana. Akan haka ne hukumomin suka nemi mahajjatan da kada su fito daga masaukinsu daga ƙarfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na…
Read More

Benue: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji tara a Bus

Daga BELLO A. BABAJI Ƴan bindiga a Jihar Benue sun yi garkuwa da fasinjoji guda tara har da direban motar kamfanin sufuri na jihar a hanyar Owukpa zuwa Orokam dake Ƙaramar Hukumar Ogbadibo. Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar Asabar a yayin da fasinjojin ke dawowa daga kasuwar Orba ta Jihar Enugu zuwa Owukpa. Wata ƴar Owukpa mai suna Grace Ogwuche ta shaida wa manema labarai cewa ƴan bindigar sun harbi direban da kuma ɗaya daga cikin fasinjojin a yayin harin. Haka kuma wani fasinja da ya samu raunuka a sakamakon harbin da maharan suka…
Read More

Tsare-tsaren Tinubu za su kawo sauƙin rayuwa nan ba da jimawa ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI Babban Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya ce nan ba da jimawa ba ƴan Nijeriya za su ga sauƙin al'amura a yayin da gyare-gyare a harkar tattalin ke fara aiki a ƙasar. Onanuga a yayin ganawa da manema labarai a Legas, ranar Lahadi, ya ce kwanan nan tsare-tsaren Tinubu za su fara aiki a kowane fanni a Nijeriya. Ya ce, ba kaɗai gabatar da sauye-sauye na ci-gaba Shugaba Tinubu ya yi ba, har ma da magance ƙalubalen da gwamnatocin baya suka ƙaurace wa, waɗanda suke hana ruwa gudu a yayin…
Read More

Fashewar bom ya halaka mutum tara a tashar Borno

Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Maiduguri Rahotanni sun bayyana yadda fashewar bom ya kashe kimanin mutum tara a tashar mota a Ƙauyen Mairari da ke Ƙaramar Hukumar Guzamala, Jihar Borno. Bayanan da MANHAJA ta tattaro sun nuna cewa al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau Lahadi, yayin da kuma tashin bom ɗin ya raunata ƙarin wasu jama'a da dama a tashar. Sa'ilin da yake tofa albarkacin bakinsa dangane da harin; Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Hon. Abdulkarim Lawan, ya tabbatar faruwar lamarin, inda ya ce tashin bom ɗin ya rutsa da fasinjoji dake jiran mota. Ya kara da…
Read More

Gwamnatin Kano ta bada hutun kwana ɗaya domin jimamin rasuwar ƴan wasa 22 a hatsari

Daga BELLO A. BABAJI Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya ayyana ranar Litinin a matsayin lokacin hutu ga ma'aikata domin taya jimami ga iyalan ƴan wasa 22 da suka rasu a wani hatsarin mota a lokacin da suke koma wa Kano daga Jihar Ogun. Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa a wata takarda, ya ce gwamnati ta zaɓi ranar Litinin ne domin bai wa al'umma damar yin addu'o'i ga mamatan tare da iyalansu. Daga cikin waɗanda suka rasu akwai ƴan wasan guje-guje da tsalle-tsalle da koca-kocai da kuma jami'an wasanni, waɗanda suke wakiltar jihar a wasanni da dama…
Read More

Wasanni: Tawagar Shettima ta je jajen Kanawan da suka rasu a hatsarin mota

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ne ya jagoranci ayarin don isar da saƙon jajen Shugaba Bola Ahmad Tinubu bisa hatsarin mota da ya rutsa da ƴan tawagar jihar Kano a kan hanyar Kaduna zuwa Kano. Lamarin ya auku ne a lokacin da ƴan wasan suke kan hanyar dawowa daga gasar wasannin motsa jiki da aka gudanar a jihar Ogun. Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma jajenta wa iyalai da al’ummomin da bala’in ambaliyar ruwan sama ya shafa a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta jihar Neja da kuma waɗanda suka rasa rayukansu a yayin iftila'in.
Read More