Babaji

5702 Posts

NEMA ta yi aiken jami’an ko-ta-kwana a Katsina da wasu jihohi 14 da ke fuskantar barazanar ambaliya

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta rarraba jami'anta a jihohi guda 15 da suke fuskantar barazanar aukuwar ambaliya, da nufin wayar da kan al'umma da kuma ƙaura daga wuraren da ake fargabar samun ta. Ta ce, waɗanda iftila'in ambaliyar Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja ta afka wa, ba su yi aune ba a lokacin al'amarin ya zo musu duk da gargaɗi na musamman da hukumomi suka aika musu. Babban jami'in hulďa da jama'a na NEMA, Manzo Ezekiel ya ce Jihohin sun haɗa da; Kogi, Imo, Enugu, Adamawa, Taraba, Borno, Zamfara, Katsina da Abuja.…
Read More

Kashe-kashe: Shugaban Sojoji ya tare a Benue

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban Sojojin Nijeriya (COAS), Laftanal Janar Olufemi Oluyede ya yi ƙaura zuwa Makurďi, Babban Birnin Jihar Benue a sakamakon aukuwar yawan kashe-kashen ƴan ƙauye da makiyaya da ƴan bindiga suke yi a jihar. Lamarin ya yi sanadin rasa rayuka da dama da raunata wasu gami da ƙone gidaje, wanda hakan ya ɗaiɗaita mutane da dama. A safiyar ranar Talata ne Laftanal Janar Oluyede ya bar Abuja tare da wasu manyan jami'ai (PSOs) daga ofishinsa da wasu daga Hedikwatar Tsaro zuwa jihar da nufin ganin halin da ake ciki game da al'amarin. Babban jami'in zai gana ne…
Read More

Haƙiƙanin dalilin farfaɗowar Boko Haram – Ministan Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI Ministam Tsaro, Badaru Abubakar, ya alaƙanta sake samuwar hare-haren mayaƙan Boko Haram akai-akai da babban shirin ƙungiyar na ganin ta hana zaman lafiya a yankin Sahel, lamarin da ya shafi Nijeriya, Mali, Burkina Faso da Nijar. Badaru ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a Kaduna, ranar Talata, a lokacin da ya kai ziyarar aiki ta kwana biyu a manyan cibiyoyin sojoji dake jihar ciki har da kwalejin NDA da cibiyar fasaha ta sojojin sama da sauransu. Ya ce, suna aiki tuƙuru wajen ganin sun daƙile ayyukan ƴan ta'addar, inda a sati biyu…
Read More

Gwamnati ta fara biyan tsofaffin ƴan hidimar ƙasa ragowar alawus ɗinsu na N44,000

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta fara biyan ragowar alawus ɗin N44,000 na mafi ƙarancin albashi ga tsofaffin ƴan hidimar ƙasa NYSC. Hakan cika alķawari ne da gwamnatin ta yi, wanda ya dace da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi, lamarin da ya haura da alawus ɗinsu daga N33,000 zuwa N77,000. Ana biyan kuɗin ne kaɗai ga waɗanda suka kammala hidimarsu gabannin fara aiwatar da biya da sabon tsarin albashi. Tuni dai wasu daga cikin tsoffin ƴan hidimar suka fara tabbatar da samun ragowar kuɗaɗen nasu a asusun bankunansu ta kafafen sada zumunta musamman ta kafar X. Da dama daga…
Read More

2027: APC ta musanta bai wa ƴan majalisa tikitin takara kai-tsaye

Daga BELLO A. BABAJI Jam'iyyar APC ta musanta rahoton da ya karaďe kafafen sadarwa da ke cewa ta bada tikitin takara na damar sake tsayawa takara ga sanatoci da ƴan Majalisar Wakilai ba tare da yin zaɓen fidda gwani ba. A sanarwar da Sakataren na yaɗa labaranta na ƙasa, Felix Morka ya fitar a ranar Talata, jam'iyyar ta yi kira ga al'umma da su yi watsi da rahoton, yana mai bayyana shi a matsayin ƙarya da aka jingina wa APC. Ya ce, lallai labarin ba gaskiya bane domin ba daga jam'iyyar ya fito ba, inda ya ce an ƙirƙire shi…
Read More

Zamfara: Farmakin sojoji ya hallaka ƴan bindiga 20 da ƴan bijilante biyar

Daga BELLO A. BABAJI Dakarun sojoji sun yi nasarar hallaka sama da ƴan bindiga guda 20 a wani hari ta sama da suka kai a yankin Ƙauyukan Maraya da Wabi na Ƙaramar Hukumar Maru a Jihar Zamfara. Lamarin ya auku ne a ranar Asabar, inda kuma wasu ƴan bijilante biyar suka rasa rayukansu a sakamakon rashin janyewa a lokacin da aka buƙaci su yi hakan. Ƙwararren mai sharhi kan harkokin daƙile ayyukan ta'addanci a yankinTafkinChadi, Zagazola Makama, ya ce farmakin ya gudana ne a ƙarƙashin atisayen tawagar 'Fansan Yamma' da aka yi a ranar 1 ga watan Yuni. Ya ce,…
Read More

Majalisar Wakilai ta titsiye jagororin WAEC bisa matsalolin jarrabawa

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Litinin ne Kwamitin Majalisar Wakilai akan Ilimin matakin farko da Hukumomin jarrabawa ya yi wa hukumar gudanarwa ta Majalisar kula da Jarrabawa a Yammacin Afirka (WAEC) titsiye bisa gazawa na matsalolin da ake samu a yayin rubuta jarrabawar SSCE ta bana. A yayin zaman bincike a majalisa, ƴan majalisar sun titse Shugaban WAEC, Dakota Amos Dangut akan abinda suka kira da gazawar cika aiki, wanda hakan abu ne da zai daƙile yardar al'umma game da hanyoyin jarrabawa a Nijeriya. WAEC ta samu suka daga ɓangarori da dama a sakamakon rahotannin rashin bin dokoki da…
Read More

Yadda ziyarar Tinubu a Legas ta fallasa ɓoyayyen rikici tsakaninsa da gwamnan jihar

Daga BELLO A. BABAJI Masu-ruwa-da-tsaki na jam'iyya mai mulki (APC) sun koka game da tsamin alaƙa da ke tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu duba da cewa babu alamar sulhu a tsakanin su. Duk da cewa, babu wanda ya bayyana hakan ga al'umma a tsakanin mutanen biyu, muryoyi daga APC a matakin ƙasa da jihar sun tabbatar da samun rashin jituwa da ya raba tsakanin Shugaba Tinubu da gwamnan. Ziyarar da Tinubu ya kai wa jihar a kwanan nan ta ƙara buɗe al'amarin tun daga saukarsa a Filin jiragen sama na Murtala Muhammed, inda aka fahimci…
Read More

Zafin rana: NAHCON ta shawarci mahajjata su riƙa zama a masauƙinsu daga 10 na safe zuwa 4 na yamma

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta shawarci mahajjata da su riƙa zama a masauƙinsu daga ƙarfe 10 na safe zuwa 4 na yamma a yayin aikin hajji duba da halin tsananin zafin rana da ake ciki a ƙasa mai sarki. Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh ya faɗi hakan a yayin ganawa da manema labarai a Makkah, ranar Lahadi. Kamfanin dillancin labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa, Saudiyya ta ofishin Cibiyar Kula da Yanayi (NCM) ta bada gargaɗi game da matakin zafi a ƙasar ga mahajjata, inda ta yi kira a gare su da su kula…
Read More

Ambaliyar Mokwa: Mutanen da iftila’in ya rutsa da su sun koka da ƙarancin abinci da rashin kyan sansani

Daga BELLO A. BABAJI Kwanaki uku da aukuwar iftila'in ambaliyar ruwan sama a ƙauyuka da dama na Ƙaramar Hukumar Mokwa a Jihar Neja, mutanen da lamarin ya shafa sun koka game da halin da suka tsinci kawunansu a ciki a sansanonin da aka ware musu. Sun bayyana cewa, ba su da wadatattun abinci da kuma ingancin wajen zama a wuraren da aka ba su mafaka. Da dama daga cikin waɗanda iftila'in ya ɗaiɗaita sun ce, duk da cewa hukumomi sun ɗauki hotunansu a lokacin da su ke tare da kayan abinci, hakan bai sa an ba su ba. Ɗaya daga…
Read More