Babaji

5702 Posts

Babbar Sallah: ‘Yan sanda sun jaddada hana hawan sallah a Kano

Daga BELLO A. BABAJI Yayin da al'umma ke cigaba da gudanar da shirye-shiryen sallah a Kano, rundunar ƴan sandan jihar da haɗin-gwiwar hukumomin tsaro sun nanata haramta bukukuwan hawan sallah a jihar. A sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, rundunar ta ce ta ɗauki matakan da suka dace wajen tabbatar da zaman lafiya a yayin gudanar da hidindimun sallar tare da kira ga al'umma da su kasance masu kiyaye doka da oda da kuma ƙaurace wa duk wani abinda ka iya haddasa fitina. Rundunar ta kuma tunatar da al'umma haramta hawan salla da ta yi a lokacin ƙaramar sallah…
Read More

Trump ya haramta wa ƴan ƙasashe 12 shiga Amurka

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Laraba ne Shugaba Donald Trump na Amurka ya amince da hana ƴan ƙasashe guda 12 zuwa ƙasar. Ƙasashen sune Afghanistan, Myanmar, Chadi, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libiya, Somaliya, Sudan, da Yemen. Dokar, ta nuna cewa mutane daga ƙasashen da aka lissafo ba za a bari su shiga ƙasar ba bisa kowane irin dalili. A ranar 9 wata Yuni, 2025 ne dokar za ta fara aiki, wanda zai yi daidai da ƙarfe 5:01 na safe a Nijeriya. Hakan wani ɓangare ne na ƙarfafa dokokin shige da fice na zangon mulkinsa na biyu. Haka…
Read More

Masu jiragen kansu sun yi magiya ga gwamnati bayan ta hana 60 tashi

Daga BELLO A. BABAJI A ƙoƙarinta na ƙwato kuɗaɗen izinin shigowa daga masu jiragen sama na kansu, Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Kwastom (NCS), ta hana aƙalla guda 60 aiki a manyan filayen jiragen sama na Nijeriya. An ruwaito cewa, an rufe tashoshin ajiyar ire-iren jiragen a filayen jiragen sama na Legas da Abuja. Saidai masu jiragen, waɗanda suka hada jagororin bankuna da masu kamfanonin mai da sauransu sun fara magiya ga Fadar Shugaban Ƙasa domin a sake musu jiragen nasu. Wasu daga cikin jiragen da aka dakatar da su aiki kamar yadda jami'an Kwastom da na Ma'aikatar Sufurin Jiragen…
Read More

Ambaliyar Mokwa: Tinubu ya amince da ware biliyan N2 da tirelolin shinkafa 20 ga waɗanda iftila’in ya shafa

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 2 domin sake gina baki ɗaya gidajen da ambaliyar Mokwa a Jihar Neja ta lalata. Mataimakinsa, Kashim Shettima ne ya faɗi hakan a yayin ziyarasa a garin Mokwa a yau Laraba, biyo bayan ambaliyar da ta yi sanadin rasa rayuka da dukiyoyi dama tare da ɗaiɗaita ɗaruruwan mutane. Shettima ya kuma ce, Shugaban ƙasar ya umarci a gaggauta kai tireloli 20 na shinkafa ga mutanen da iftila'in ya afka wa a ƙoƙarin gwamnatinsa na rage musu raďaďi. Ya tabbatar musu da cewa, Shugaba Tinubu na tare da…
Read More

Arsenal za ta yi adabo da ƴan wasa 20 ciki har da Jorginho

Daga BELLO A. BABAJI Ƴan wasa Jorginho da Kieran Tierney za su bar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, bayan da kwantiraginsu ya ƙare a ranar 30 ga watan Yuni, 2025, waɗanda ta sanyaa jaddawalin waɗanda ba ta buƙatar su. Jorginho, wanda ɗan wasan tawagar Italiya ne da ke dab da rattaɓa hannu a Flamengo ta Brazil, ya koma Emirates ne daga Chelsea a Janairun 2023, inda ya yi mata wasa 79. Shi kuwa Tierney, ɗan tawagar Scotland, ya koma Arsenal daga Celtic ne kaka shida da suka gabata, inda ya buga wasa 170, kana daga baya ya je aro a…
Read More

Abinda ya sa muka fifita yaƙi da miyagun ƙwayoyi – Ribaɗu

Daga BELLO A. BABAJI Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu, ya ce Gwamnatin Tarayya tana fifita yaƙi da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi ne saboda tasirinsa mai girma akan harkar tsaron ƙasa da zaman lafiyar al'umma. Ya alaƙanta amfani da sinadarai masu cutarwa musamman akan matasa da ta'azzara da rashin tsaro ke yi a Nijeriya ganin cewa ƴan ta'adda da dama suna mu'amala da su, lamarin da ke taimaka wa yawaitar manyan laifuka da tada zaune-tsaye. Ribaɗu ya kuma ce, gwamnati ta duƙufa wajen tallafa wa ayyukan yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da gurɓatattun…
Read More

Ba na taƙaddama da yara – Martanin Amaechi ga Wike

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana dalilan da suka sanya shi naɗa Ministan Abuja, Nyesom Wike a matsayin shugaban ma'aikata a lokacin da ya ke gwamna a Jihar Ribas. Ya ce, ya naɗa shi a muƙamin ne a madadin ba shi kwamishinan kuɗi saboda ya sanya ido akansa. Da fari, Wike ya yi alla-wadai da kalaman Ameachi na cewa "Dukkan mu mu na jin yunwa", waɗanda ya yi su a lokacin bikin cikarsa shekaru 60 a duniya, makon da ya gabata, inda Wiken ya ba shi amsa da cewa yunwarsa ta mulki ce ba ta…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Shettima ya ziyarci Mokwa don jajenta wa waɗanda ambaliya ta rutsa da su

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya isa garin Mokwa dake Jihar Neja sakamakon ambaliyar ruwan sama da ta ɗaiɗaita al'umma da sanadin rasa rayukan mutane sama da guda 200. Haka kuma ta raba ɗaruruwan mutane da muhallansu daga ƙaramar hukumar, waɗanda a halin yanzu suke sansanonin ƴan hijira a wurare mabanbanta da suka haɗa da makarantu da sauran su. Sauran bayani zai zo daga baya...
Read More

Gwamnan Neja ya yafe wa fursunoni 11 da ke da hukuncin kisa akansu

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Talata ne Gwamna Umar Bago na Jihar Neja ya yi afuwa ga wasu fursunoni guda 11 da aka yanke wa hukuncin kisa a jihar. Babbar Kotun Minna ta yanke musu hukuncin bisa bisa hannu a laifin kashe-kashen da aka yi a faɗan ƙabilanci a Ƙaramar Hukumar Lavun ta jihar. A yayin ganawa da manema labarai a Minna, Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari'a na jihar, Nasiru Muhammad Mu'azu ya sanar da hakan, inda ya ce gwamnan ya yi amfani da ikonsa ne da dokar ƙasa gyaran 1999 sashe na 212 (1) ta ba shi dama…
Read More

Ondo: Yadda sarki ya ciji takwaransa a kunne

Daga BELLO A. BABAJI Rahotanni daga Jihar Ondo sun bayyana cewa an samu fargaba a garin Igbokoda dake Ƙaramar Hukumar Ilaje ta jihar biyo bayan farmakin da wani babban sarki (Oba Oladimeji) ya kai wa sarkin ƙauyen. Daily Post ta ruwaito cewa, an farmaki sarkin ne gabannin buɗe titin Igbokoda-Okitipupa mai tsawon kilomita 27.5 a garin sarkin, wanda wani babban sarki daga cikin sarakunan yankunan jihar zai ƙaddamar. Zuwa lokacin kammala rahoton, ba a bayyana sunan sarkin da ya ciji kunnen sarkin gargajiyar ba, inda a ranar Talata ne mata a garin suka yi zanga-zanga da bayyana rabin jikkunansu a…
Read More