Babaji

5702 Posts

Jamhuriyar Ireland ta koro ƴan Nijeriya 35 ba tare da dalili ba

Daga BELLO A. BABAJI Kimanin ƴan Nijeriya guda 35 har da yara ƙanana ne ƙasar Jamhuriyar Ireland ta koro su dawo wa Nijeriya daga filin jiragen sama na Dublin a ranar Laraba. Irish Mirror ta ruwaito cewa, mutanen sun haɗa da maza guda 21 da mata tara da yara ƙanana biyar, waɗanda suka iso Nijeriya a ranar Alhamis. Ministan Shari'a na ƙasar, Jim O'Callaghan ya ce ya yi farin ciki da yadda dukkan su suka koma Nijeriya duk da cewa an samu tsaiko a hanya a sakamakon al'amarin lafiya da ya bijiro. Gwamnatin ƙasar ba ta bayyana haƙiƙanin dalilin koro…
Read More

Sakkwato: Shugaban sojoji ya yi bikin sallah da dakaru da ƙarfafa musu gwiwa

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban Rundunar Sojoji (COAS) Janar Olufemi Oluyede ya yi kira ga dakarun atisayen 'FANSAN YAMMA' da su daƙile ayyukan ƴan ta'adda da ke addabar al'umma a shiyyar Arewa maso Yamma. Janar Oluyede, wanda ya samu wakilcin Kwamandan dakarun yaƙi na zamani, Janar Adeleke Ayannuga, ya halarci taron cin abinci na musamman tare da jami'an a Sakkwato, ranar Juma'a. Ya ce, sojoji sun yi nasarar nakasa ƴan ta'addar, inda kuma suna cigaba da ƙoƙarin tabbatar da cin galaba akansu, yana mai nuni da muhimmancin haɗa kai tsakanin sauran hukumomin tsaro domin cimma nasara. A yayin taron ne…
Read More

Mun shiga mawuyacin hali yayin da ta’addanci ke mamaye jiharmu, inji Gwamnan Benue

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia ya bayyana cewa jihar tana kewaye da ƴan ta'adda da ƴan fashi, inda hare-haren da ake kai wa a ƙauyuka a ƴan kwanakin nan sun kere tsakanin makiyaya da manoma. An samu adadi mai yawa na hare-hare a ƴan makonnin nan a yankin Arewa ta Tsakiya, waɗanda suka jefa ƙananan hukumomi da dama cikin mawuyacin hali, lamarin da a sakamakonsa aka rasa mutane masu tarin yawa. A yayin hira da shi ta gidan talabijin na Channels a ranar Juma'a, Gwamna Alia ya ce ƴan ta'addar sun shirya hare-haren ne tare da…
Read More

Miliyoyin mahajjata sun yi jifar sheɗan yayin da aikin hajjin bana ke ƙarewa

Daga BELLO A. BABAJI A yayin da al'umma ke gudanar da hutun Babbar Sallah, mahajjata a Saudiyya sun yi jifar sheɗan a ranar Juma'a wanda ɗaya ne daga cikin wajiban ƙarshe a aikin hajjin. Kimanin sama da mutane miliyan 1.6 ne suka yi jifar a duwatsu guda uku da ke nuni da tambarin sheɗan a Mina dake wajen birnin Makkah. Tun da asubahin ranar ne mahajjata suka fara jifar domin samun sauƙi daga halin tsananin zafin rana da ƙasar ta ke da shi. Jifan, aiki ne na koyi ne da Annabi Ibrahim (AS), a lokacin da sheɗan ya yi yunƙurin…
Read More

Kano: Gobara ta kama kasuwar ‘Farm Centre’

Daga BELLO A. BABAJI Shaguna da dama sun ƙone a yayin da gobara ta kama a kasuwar waya ta Farm Centre dake Jihar Kano. Lamarin ya auku ne a safiyar ranar babbar sallah, wanda aka gano a lokacin da wani mutum ya yaɗa bidiyon a shafukan sada zumunta, inda aka ga hayaƙi na tsahi daga wani sashi na kasuwar. Duk da cewa ba a kai ga sanin haƙiƙanin aukuwar lamarin ba, wani shaida ya ce gobarar ta ƙone shagunan da ke sayar da wayoyi ne da na kayayyakinsu. Hukumar kashe gobara ta jihar ba ta fitar da wani jawabi ba…
Read More

Ba za mu bi sahun Gwamna Umo Eno ba, inji kansiloli a Akwa-Ibom

Daga BELLO A. BABAJI Biyo bayan sauya sheƙa da Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Umo Eno ya yi a ranar Juma'a, kansiloli a ƙananan hukumomin jihar sun juya masa baya da cewa ba za su bi shi zuwa APC ba domin bai shawarce su ba kafin ya ɗauki matakin a matsayinsu na zaɓaɓɓun ƴan siyasa. Wani kansila da yan emi a sakaye sunansa ya ce hakan wulaƙanci ne a gare su, saboda haka lallai sai ya neme su tare da tattaunawa da su kafin a warware matsalar. Ya kuma ce, tuni wasu daga cikinsu suka yanke shawarar sake tsayawa takara a PDP…
Read More

Daga ƙarshe Gwamnan Akwa-Ibom ya koma APC

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Umo Eno ya koma Jam'iyyar APC daga babbar jam'iyyar adawa (PDP). Ya bayyana hakan ne a gidan gwamnatin jihar dake Uyo, ranar Juma'a. Gwamnan ya ce, hakan ya biyo bayan shawarwari ne da jiga-jigan masu-ruwa-da-tsaki na tsawon watanni uku. Ya kuma yi godiya ga PDP bisa goyon bayan da ta ba shi a yayin mulkinsa, yana mai cewa lokaci ya yi da ya kamata ya sauya sheƙa domin ci-gaban siyasarsa. Haka kuma, Eno ya ce hakan da ya yi wani mataki ne na neman ƙara kusanci ga Shugaba Bola Tinubu domin jiharsa ta…
Read More

Tinubu ya taya Musulmi murnar sallah da kira a riƙa taimakon juna da jinƙai

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya al’ummar Musulmi a Nijeriya da duniya baki ɗaya murnar zagayowar bikin babbar Sallah, tare da jaddada muhimmancin sadaukarwa, biyayya ga Allah da kuma ɗorewar juriya a lokacin ƙalubale. A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, shugaban ƙasar ya ce kwanaki goma na farkon watan Zul Hijja na cikin ranaku masu albarka, waɗanda ke cike da alkairai da kuma zaburarwa zuwa yawaita ibada. Ya bayyana cewa, duk da ana gudanar da bikin Idin Sallah Babba, amma haƙiƙar tasirin ranar na koyar da mu sadaukarwa, biyayya da ƙaunar juna.…
Read More

Shettima ya ƙaddamar da asibitin African Medical Centre of Excellence a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ƙaddamar da Asibitin African Medical Centre of Excellence (AMCE) a Abuja, wanda wani katafaren cibiyar kiwon lafiya ne da aka gina ta hannun Afreximbank tare da haďin-gwiwar Kings College Hospital London. Wannan cibiya babbar nasara ce ga lafiyar al’umma a Afirka wadda kuma ta ke zama alamar ci-gaba da ƙirƙire-ƙirƙire a fannin lafiya da aka gina a Nijeriya domin amfanin Nahiyar da duniya baki ɗaya. Haka kuma Cibiyar tana da matsayi mai muhimmanci a Abuja Najeriya inda aka tanadar da ita domin bayar da kulawa ta musamman a fannonin cututtukan…
Read More

Tsohon Ministan Ilimi, Sanata Jibril Aminu ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI Babban masani a harkar likitanci kuma tsohon Ministan Ilimi da Fetur, Farfesa Jibril Aminu ya rasu. Marigayin ya rasu ne bayan ya shafe shekaru 85 a duniya, inda ya riƙe manyan muƙamai a Nijeriya. A ranar Alhamis ne farfesan ya rasu a Abuja bayan fama da wani rashin lafiya da ya ɗauki tsawon lokaci yana jinya a kai. Haka kuma ya riƙe muƙamin jakadan Nijeriya ga Amurka a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo daga shekarar 1999 zuwa 2003. Daga bisani ya zama Sanata a 2003 har zuwa 2011, inda ya wakilci mazaɓar Adamawa ta…
Read More