Babaji

5702 Posts

NAF ta tarwatsa maɓoyar ƴan ta’adda a Borno

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an Rundunar sojojin sama (NAF) sun yi nasarar tarwatsa maɓoyar ƴan ta'adda a Jihar Borno. NAF ta ce, harin, wanda ta kai ta sama ya yi sanadin tarwatsa wasu mafaka na ƴan ta'adda da daƙile harin da mayaƙan suka shirya kaiwa a ranar sallah a jihar. Kakakin NAF, Air Kwamado Ehimen Ejodame a wata takarda ya ce dakarun sun kai harin ne a ranakun 5 da 6 ga Yuni, 2025. Takardar ta bayyana cewa dakarun na Atisayen HAƊIN KAI sun lalata maɓoyar Boko Haram a yankin Tumbumma Baba da Chiralia dake kudancin Tumbuns a jihar. Ya…
Read More

Zamfara: ‘Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya da raunata biyu a masallaci washe-garin ranar sallah

Daga BELLO A. BABAJI Mutum ɗaya ya rasa ransa a yayin da wasu biyu suka jikkata a sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai wa masallata da ke tsaka da sallar Isha a Ƙauyen Moriki dake Gundumar Moriki a Ƙaramar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara. Bayanan sirri daga ƙwararre kan sharhin dabarun daƙile ta'addanci, Zagazola Makama, ya ce harin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Asabar a lokacin da maharan suka farmaki jama'a a ƙauyen, inda suka yi ta harbe-harbe a wani ƙaramin masallaci. Ganin hakan ne ya sa aka baza jami'an tsaro a yankin da…
Read More

Babu asarar rai a gobarar otal ɗin mahajjatan Nijeriya a Makkah, inji NAHCON

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta ce babu wanda ya mutu a yayin gobarar da ta kama wani sashi na otal ɗin da alhazan Nijeriya guda 484 suke zama a Makkah. Mataimakiyar daraktan yaɗa labaran NAHCON, Hajiya Fatima Usara ta bayyana hakan a wata takarda, ranar Lahadi. Ta ce, al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na ranar Asabar a 'Imaratus Sanan Hotel' a lokacin da mahajjatan suke gudanar da ibada a Mina. Tuni hukumomin Saudiyya da haɗin-gwiwar hukumar gudanarwar otal ɗin suka kai ɗauki na gaggawa tare da kashe gobarar, lamarin da ya dakatar…
Read More

An fusata da yafiya ga fursunoni 11 da gwamnan Neja ya yi

Daga BELLO A. BABAJI Wata ƙungiya mai suna Gaba Development Association daga Ƙaramar Hukumar Lavun a Jihar Neja, ta bayyana rashin gamsuwarta da yafiya ga fursunoni guda 11 da ke da hukuncin kisa akansu da Alƙali Maimuna A. Abubakar ta Babbar Kotun jihar ta yi musu, waɗanda aka tsare bisa laifin kisan mutane bakwai a Ƙauyen Gaba. Shugaban ƙungiyar, Mista Paul Gana a yayin taron manema labarai a Minna, ya roƙi Gwamna Umar Bago na jihar da ya janye batun yafiyar, inda ya ce hakan ya sosa wa iyalan waɗanda aka kashe zuciya. Ya ce, a shekara 2018 ne aka…
Read More

Gobara ta kama otal ɗin da mahajjatan Nijeriya 480 suke a Makkah

Daga BELLO A. BABAJI Gobara ta kama wani sashi na Otal ɗin Imaratu Sanan, wanda ke ɗauke da mahajjatan Nijeriya guda 480 a birnin Makkah. Otal ɗin yana wani yanki ne da ake kira da Sharamansur a ƙasar Mai Tsarki. Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta tabbatar da cewa baki ɗaya mahajjatan 480 suna nan cikin ƙoshin lafiya. A sanarwar da mataimakiyar daraktan yaɗa labaran hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce agajin gaggawa daga hukumomin Saudiyya da hukumar gudanarwar otal ɗin sun taimaka wajen kashe gobarar cikin ƙaramin lokacin gabannin ta mamaye sauran sassan ginin gidan. Akan haka…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Alhamis matsayin hutun Ranar Dimukraɗiyya

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Alhamis a matsayin lokacin hutu domin bikin zagayowar Ranar Demokraɗiyya na shekarar 2025. Babbar Sakatariyar Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, Magdalene Ajani ba bayyana hakan a wata takarda, ranar Lahadi. Ta ce, Ministan Ma'aikatar, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya sanar da hakan a madadin Gwamnatin, inda ya taya al'ummar Nijeriya murnar cika 26 na mulkin farar hula ba tare da samun tsaiko ba. Ya bayyana cewa, zaɓen June 12 da aka soke a ƙasar yana wakiltar tafiyar da aka ɗauko na gina ƙasa mai cike da gaskiya da adalci da wanzuwar zaman lafiya…
Read More

NiMET ta yi hasashen ruwan sama da tsawa na kwana uku daga Lahadi

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMET) ta yi hasashen samun ruwan sama da tsawa a Nijeriya daga ranar Lahadi zuwa Talata. A saƙon hasashen yanayi da ta fitar a ranar Asabar, hukumar ta ce za a samu tsawa da ruwan sama a wasu yankunan jihohin Taraba da Adamawa dake Arewacin Nijeriya. Haka kuma, a lokacin rana da dare akwai yiwuwar samuwar tsawa da ruwan sama a jihohin Katsina, Kano, Zamfara, Kaduna, Jigawa, Borno, Gombe da Bauchi. NiMET ta ce, a yammaci kuma an yi hasashen samun tsawa da ruwan sama a yankunan Abuja, Neja, Nasarawa,…
Read More

Kwastom ta ɗage haramcin tashin jirage masu zaman kansu

Daga BELLO A. BABAJI An samu sauƙi game da al'amarin jirage guda 60 na masu kansu a Nijeriya, a yayin da Hukumar Kwastom (NCS) ta dakatar da hana su tashi bisa zargin su da rashin biyan kuɗin shigowa na tsawon wata guda. Da farko NCS ta sanar da haramta wa jiragen aiki a Nijeriya kan rashin biyan kuɗaɗen izinin aiki da su a ƙasar, waɗanda a saboda haka ne aka hana su zirga-zirga daga filayen jiragen sama na Murtala Muhammed dake Lagas da kuma Nnamdi Azikwe a Abuja. Wasu muryoyi sun bayyana cewa, jiragen da aka soke musu yin aiki,…
Read More

Elon Musk ya yi asarar Dala biliyan 34 a kwana ɗaya bayan takun-saƙa da Trump

Daga BELLO A. BABAJI Matakin arziƙin shahararren Ba'amurken Attajirin nan, wato Elon Musk ya yi ƙasa da kimanin Dala biliyan 34a ranar Alhamis wanda hakan ɗaya ne daga cikin asara mafi girma da ya tafka a tarihin dukiyarsa, kamar yadda Bloomberg Billionaires Index ta bayyana. Hakan ya biyo bayan takun-saƙa da Shugaba Donald Trump a sakamakon kalaman da Musk, wanda shi ne shugaban kamfanonin Tesla da SpaceX ke wallafawa a shafin X, waɗanda ke nuna ƙiyayyarsa a fili ga Trump da gwamnatinsa. Daga cikin maganganun Musk akwai wanda ke alaƙanta Trump da Jeffrey Epstein, wanda ya ce Shugaban ƙasar ya…
Read More

Abinda ba a bayyana ba game da ƴan wasa 22 da suka rasu a hatsari da haihuwar iyalin ɗaya daga cikinsu

Daga BELLO A. BABAJI A yayin da ake tsaka da jimamin rashin Kanawan ƴan wasan, iyalin ɗaya daga cikin mamatan, wato Abubakar Yakubu Isma'il ta haifi ɗa namiji kwanaki shida bayan aukuwar hatsarin, wanda ya rutsa da ƴan wasa sama da 20 a lokacin da suke koma wa gida daga babban taron wasanni na ƙasa da aka yi a Jihar Ogun. Abubakar yana ɗaya daga cikin mutane 21 da suka rasu a yayin aukuwar lamarin, inda matarsa Ummi mai ɗauke da tsohon ciki ta samu labarin a lokacin da take tsaka da yin girki. Lamarin da ya jefa ta cikin…
Read More