Babaji

5702 Posts

MOPPAN ta jajenta wa Adam A. Zango kan hatsarin da ya yi

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar masu shirya fina-finai ta Ƙasa (MOPPAN) ta jajenta wa jarumi Adam A. Zango game da iftila'in da ya same shi na hatsarin mota. A sanarwar da Sakatarenta, Dakta Ibrahim Gumel ya fitar, MOPPAN ta yi addu'ar fatan Allah ya ba shi lafiya tare da kiyaye sake aukuwar irin haka a nan gaba, da kuma fatan hakan ya zamo kaffara a gare shi. Haka kuma, ya ce a madadin abokanansa na arziƙi da na sana'a tare da masoya suna masa jaje da fatan samun sauƙi cikin ƙanƙanin lokaci. Dakta Gumel ya yi addu'ar samun nasara ga…
Read More

Maryam Abacha ta magantu akan zargin mijinta da hannu a badaƙalar kuɗaɗe

Daga BELLO A. BABAJI Matar marigayi tsohon shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha, wato Inna Maryam Abacha, ta musanta zargin batun cewa mijina ya yi almundahanar biliyoyin daloli a lokacin da ya ke shugaban ƙasa. A hira da ita ta gidan TVC a ranar Lahadi, ta bayyana zargin da aka yi wa mijin nata a matsayin rashin adalci da kuma ƙoƙarin ruɗar da al'umma. Ta yi ƙalubalen cewa, babu wata hujja ta kai-tsaye da ke tabbatar da Abacha ya yi almubazzaranci da dukiyar ƙasa, tana mai ƙalubalantar bututuwan da ke cewa an sace biliyoyi da kai su ƙasashen waje a…
Read More

Gwamnan Gombe ya yi tir da kisan Amadi Kasiran daga ɓata-gari da umarnin a farauto su

Daga BELLO A. BABAJI Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya yi alla-wadai d kisan Ahmed Aliyu mai shekaru 45, wanda aka sani da Amadi Kasiran da wasu ƴan daba suka farmaka a yankin Hammadu Kafi dake cikin garin Gombe. Lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, 8 ga watan Yuni, inda aka daɓa wa mamacin wuƙa, lamarin da ya sa aka garzaya da shi babban asibitin Specialist inda aka tabbatar da mutuwarsa, kamar yadda muryoyi daga hukumomin tsaro suka bayyana. A lokacin da ya ke magana game da al'amarin, Gwamna ya koka tare da bayyana alhininsa, yana mai…
Read More

Mataimaki ga Tinubu ya yi murabus, ya jinjina wa Ajuri Ngelale

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Litinin ne Babban Mai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu kan Harkokin Al'umma, Aliyu Audu ya ajiye aikinsa. A wani saƙon shafi ɗaya da ya fitar a ranar 8 ga watan Yuni, Audu ya bayyan cewa ya yi murabus, wanda hakan zai fara aiki ne a nan take. Sannan ya yi wa Shugaban ƙasar godiya bisa ba shi damar yi wa ƙasa hidima a ƙarƙashinsa. Ya kuma yaba wa tsohon kakakin Shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, wanda shi ne ya bada shawara aka ba shi muƙamin a watan Agustan 2023. Kazalika, ya yi addu'ar fatan alkhairi…
Read More

Tinubu ya kawo ƙarshen saɓaninsa da gwamnan Legas bayan ya yafe masa

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya shelanta cewa alaƙarsa da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu tana nan da ƙarfinta sakamakon a yanzu an samu yafiya a tsakanin su. A baya ne aka samu rahotannin da ke nuna cewa an samu tsamin dangantaka a tsakanin Shugaban Ƙasar da gwamnan, wanda yi ta yaɗawa a Soshiyal Mediya. A watan Mayu ne Shugaba Tinubu ya yi buris da gwamnan a lokacin da ya je Legas domin ƙaddamar da zangon farkon na aikin titin Legas zuwa Kalaba. A wani bidiyo da mataimaka wa Shugaban Ƙasa kan harkokin Soshiyal Mediya, Dada Olusegun ya…
Read More

Shettima ya ƙaddamar da taraktoci 375 da Hukumar NASENI ta ƙawata a Borno

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ƙaddamar da motocin tarakta guda 375 na Gwamnatin Jihar Borno waɗanda Hukumar Kula da kayayyakin Kimiyya da Fasaha ta Ƙasa (NASENI) a ƙarƙashin Ofishin aikin kula da kadarorin ƙasa, gyara su da raba su ta ƙawata. A ranar Lahadi aka gudanar da taron a ofishin hukumar kula da kayan aikin noma (BOSAMA) ta jihar a Maiduguri. Shettima ya yaba wa Gwamna Babagana Umara Zulum bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da jagoranci a jihar. Haka kuma ya jinjina wa NASENI kan aiki tuƙuru da ta ke yi wajen haɓaka harkar noma a…
Read More

Janar Buratai ya tsallake rijiya da baya harin ƴan ta’adda

Daga BELLO A. BABAJI Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya) ya tsallake rijiya da baya a lokacin da wasu mayaƙan Boko Haram suka kai wa tsohon shugaban sojojin hari, ranar Juma'a. Lamarin ya tada ƙura duba da yadda ya taimaka wa ta'azzara da ayyukan ta'addanci ke yi a shiyyar Arewa ta Gabas. Sanata Ali Ndume ya bayyana hakan a yayin hira da gidan telebijin na Channels a yammacin ranar Lahadi. Ya ce, an farmaki Buratai da wasu sojoji ne a kusa da wani babban sansanin sojoji. Duk da cewa ba samu cikakken bayani kan al'amarin ba, Sanatan ya ce…
Read More

Gwamnati ta umarci a yi binciken zargin sakaci da marasa lafiyar da suka yi hatsari a asibitin Abuja

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da bincike akan wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa, wanda ke nuna yadda aka yi sakaci da al'amarin wasu marasa lafiya da suka yi hatsari a ɗakin agajin gaggawa na Babban Asibitin Tarayya (FMC) dake Jabi a Abuja. Bidiyon ya bayyana yadda aka bar marasa lafiyar kara zube ba tare da kula su ba duk da cewa an kai su ne a mawuyacin hali daga aukuwar hatsarin. Wanda ya ɗauki bidiyon ya ce, an samu mutanen ne a hali na jikkata, inda ya ɗauke su zuwa asibitin domin ba su…
Read More

Portugal ɗin Ronaldo ta lashe UEFA Nations League akan Sifaniya

Daga BELLO A. BABAJI Ƙasar Portugal ta yi nasarar lashe kofin gasar UEFA Nations League a karo na biyu biyu bayan doke Sifaniya da ta yi a bugun fenareti a Birnin Munich. Ɗan wasa Ruben Neves ne wanda ya zura ƙwallon da ya bai wa Portugal nasara, lamarin da ya sanya Ronaldo kukan murna bayan da aka tashi wasan a 2 da 2. Ɗan wasan da Arsenal ta ke hari, Martin Zubimendi shi ya fara zura ƙwallon da ya bai wa Sifaniya dama a karon fari, kana daga bisani bayan minti biyar Nuno Mendes na Portugal ya farke. Mikel Oyarzabal,…
Read More

Trump ya sanya motarsa ta kamfanin Tesla a kasuwa kan rashin jituwa da Elon Musk

Daga BELLO A. BABAJI Donald Trump na shirin sayar da motar Fadar White House ta kamfanin Tesla a yayin da dangantakarsa da Elon Musk ta yi tsami. A watan Maris ne Trump ya sayo motar mai ƙirar 'Model S Tesla' a lokacin da Musk ya gabatar da ita a fadar. Trump ya sayi motar ne da nufin haɓaka kasuwancin Musk a lokacin da matakin raba hannun-jarin kamfanin nasa ya yi ƙasa. Saidai, wani babban jami'i ya shaida wa NewsNation cewa Trump na shirin sayar da motar ko kuma kyautar da ita duba da rashin jituwarsu, wadda aka ajiye ta White…
Read More