Babaji

5704 Posts

Yanzu-yanzu: Tinubu ya aike da kasafin tiriliyan N1.48 na Ribas ga majalisa

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Alhamis ne Shugaba Bola Tinubu ya aika kasafin Naira tiriliyan 1.48 na Gwamnatin Jihar Ribas ga majalisar dokoki domin gudanar da aiki akansa. Tinubu ya ce, hakan abu ne da ke da muhimmanci duba da hukuncin Kotun Koli na soke kasafin 2025 na jihar da kuma halin dokar ta-ɓaci da take ciki a yanzu. Ya kuma ce, ₦324bn daga ciki za a yi amfani da shi ne wajen aiwatar da ayyukan ababen more rayuwa, ₦166bn ga ɓangaren lafiya, yayin da ₦75.6bn kuma za a sanya shi a ilimi, sannan ₦31.4bn ga harkar noma. Ya…
Read More

Osun: NCoS ta sanya ladar miliyan N5 ga wanda ya taimaka aka kamo fursunonin da suka tsere

Daga BELLO A. BABAJI Al'amarin tsaro ya samu tsaiko a gidan gyaran hali na Ilesa dake Jihar Osun, sakamakon iska mai ƙarfi yayin mamakon ruwan sama da ta yi sanadin ruftawar wani sashe na gininsa, lamarin da ya taimaka wa fursunoni bakwai tserewa. Jami'an Hukumar kula da Gidajen Yari (NCoS), sun tabbatar da aukuwar lamarin. Waɗanda suka tseren sun haɗa da John Michael mai shekaru 34; Tobi Akin ɗan shekara 19; Eze Nweze ɗan shekara 40; Olalekan Ajofoyinbo mai shekaru 45; Ninalowo Yusuf, shekaru 28; Matthew Ogunjimi mai shekaru 20 da kuma Kabiru Oyedun mai shekaru 39. An sanya ladar…
Read More

Tottenham ta lashe kofin Europa bayan doke Manchester United

Daga BELLO A. BABAJI A daren ranar Laraba ne Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur dake Arewacin London, ta yi nasara akan Manchester United da ci 1 da nema, wanda hakan ya ba ta damar lashe kofin Europa League na kakar 2024/2025. Ɗan wasa Brennan Johnson ne wanda ya zura kwallon a minti na 42 bayan kuskure da aka samu daga Luke Shaw na Manchester, lamarin da ya ba ta nasara a Filin wasa dake Birnin Bilbao na ƙasar Sifaniya. Nasarar ta nuna cewa, Tottenham ta samu gurbi a gasar zakarun Nahiyar Turai, wato UEFA Champions League na kakar 2025/2026.…
Read More

‘Yan sanda sun kama mutane 25 bisa casa DPO a Gombe

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sandan jihar Gombe, ta tabbatar da kama mutane 25 da ake tuhumar su da hannu a kai farmaki ga CSP Adamu Alhaji Idi, wanda ke aiki a babban ofishin hukumar na yankin Kwadon a Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba dake jihar. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya bayyana hakan a wata sanarwa, ranar Laraba. Ya ce, wasu gungun ƴan daba da ake kira da ƴan Kalare ne suka lakaɗa wa jami'in duka a lokacin da ya ke tsaka da gudanar da aikinsa na ɗan sanda a cikin garin Kwadon, ranar Talata. Ya kuma yi tir da…
Read More

Majalisar Wakilai ta nemi Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da ƙarin fanshon da aka amince da shi

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Wakilai ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta aiwatar da dukkanin ƙarin da aka yi na kuɗaɗen fansho ba tare da jinkiri ba. Ta yanke hakan ne bayan gabatar da batu kan kalubalen da ƴan fansho suke fuskanta a sakamakon rashin biyan su da ƙarin gami da riƙe musu sauran haƙƙoƙinsu na tsofaffin ma'aikata. A yayin karanta batun ne a zaman majalisar na ranar Laraba, ɗan majalisa Ibrahim Ayokunle ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu ya amince da ba su albashin tallafi na N25,000 da kuma ƙarin N32,000 ga kuďin fansho da tsofaffin…
Read More

‘Yan siyasa da jami’an sojoji na daga cikin ƴan tsegumi ga Boko Haram, inji Zulum

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya zargi wasu daga cikin jami'an sojoji da ƴan siyasa da yin tsegumi tare da taimaka wa mayaƙan Boko Haram. A wata hira da 'News Central's Breakfast Central' a ranar Laraba, gwamnan ya ce "Mu na da masu tsegumi da masu yin zamba-cikin-aminci acikin jami'an sojojin Nijeriya, ƴan siyasa da cikin garuruwan." Zulumi ya ci alwashin hukunta dukkan wanda aka samu da hannu a yi wa ƙoƙarin gwamnatinsa na daƙile ayyukan ta'addanci zagon-ƙasa a jihar. Ya kuma ce, gwamnatinsa za ta ƙarfafa matakan tsaro na sirri domin magance matsalolin…
Read More

Majalisar Dattawa na neman rage ƙarfin EFCC da ICPC don kafa hukumar ƙwato kadarori

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Talata ne Majalisar Dattawa ta yi karatu na biyu ga ķudirin da ke neman yin kwaskwarima ga dokokin manyan laifuka (sashen kwatowa da gudanarwa) na 2022 da gabatar da bukatar samar da sabuwar hukuma da za ta ɗauki alhakin kula da ķwato haramtattun kadadori. Sanata Idiat Oluranti Adelabu (Lagas ta Yamma) ta ɗauki nauyin ķudirin, wanda ke neman a inganta tabbatar da gaskiya da adalci wajen kula da kadadorin da aka ķwato ta yadda za a sauke nauyin hakan daga kan hukumomi 18 da ke kula da ɓangaren a dokar da ake aiki da…
Read More

Fursunoni bakwai sun tsere bayan ruftawar ginin gidan yari a Osun

Daga BELLO A. BABAJI Wani mamakon ruwan sama da aka yi a ranar Talata ya yi sanadin tserewar fursunoni bakwai daga gidan gyaran hali na Ilesa dake Jihar Osun sakamakon ruftawar da wani sashe na gininsa ya yi. Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa, NCoS ta ce lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 2:00 na dare a dalilin iska da tsawa yayin mamakon ruwan. Kakakin hukumar, Umar Abubakar a wata sanarwa, ya ce tuni hukumomi suka ƙaddamar da aikin farauto waɗanda suka tsere domin dawo da su gidan gyaran halin. Ya ce, Kwantirola Janar na hukumar, Sylvester…
Read More

Oyo: ‘Yan sanda sun harbe ɗalibin WAEC yayin farautar ƴan yahoo

Daga BELLO A. BABAJI Wani ɗalibi da ke rubuta jarrabawar WAEC mai suna Taiwo, ya rasa ransa a lokacin da ƴan sanda suka yi harbi yayin wani atisaye a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo. Lamarin ya auku ne a kusa da kasuwar Gbagi dake yankin Soka a birnin, ranar Litinin. Wani shaida ya ce, jami'an ƴan sandan suna farautar ƴan damfara ta yanar gizo ne da aka fi sani da ƴan yahoo a lokacin da abin ya faru, inda ɗaya daga cikinsu ya yi harbin da ya samu ďalibin, wanda ke cikin motar mahaifinsa a hanyarsa ta zuwa rubuta jarrabawa.…
Read More

Tsarin Tinubu na cinikin ɗanyen mai da Naira ne ya karya farashin fetur – Ɗangote

Daga BELLO A. BABAJI Matatar Man Fetur ta Ɗangote ta ce tsarin cinikayyar ɗanyen mai da Naira na Shugaba Bola Tinubu ya taimaka musu wajen rage farashin fetur, lamarin da ya kai ga samun sauƙinsa a gidajen mai. Kamfanin man ya ce, duk da hauhawar farashin mai a kasuwar mai a mataki na duniya, yana samun damar yin ragi akai-akai don tabbatar da samar da sauƙi ga al'umma. A sanarwar da babban jami'in yaɗa labaran kamfanin, Anthony Chiejina ya fitar, ya ce hakan na samuwa ne a ƙoƙarinsu na tallafa wa Tattalin arziƙin Nijeriya da rage raďaďi ga kwastomomi duk…
Read More