20
May
Daga BELLO A. BABAJI Jami'an tsaro a Saudiyya sun kama mata biyu da ake kyautata zaton mata da mahaifiya ne ga Ado Aliero, wanda ɗaya ne daga cikin fitattun jagororin ƴan bindiga a Nijeriya, a lokacin da suke tsaka da gudanar da aikin hajji. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, shaidu sun ce an kama mutane biyun ne sakamakon atisayen sirri da aka alakanta da jami'an tsaron da ke ƙoƙarin daƙile ayyukan ta'addanci a Arewa maso Yamma. An kama su ne a Madina a wani yanayi na basaja suna gudanar da harkokinsu. A wani faifan bidiyo da ya karaďe kafafen…
