18
May
Daga BELLO A. BABAJI Jami'an rundunar ƴan sandan farin kaya DSS, sun cafke shahararren ďan ta'adda da ake nema ruwa-a-jallo, Yahaya Zango a sansanin maniyyata a Abuja, yayin da ya yi basaja a matsayin ďaya daga cikinsu don zuwa aikin hajji a ƙasa mai tsarki. Yahaya Zango ďaya ne daga cikin jaddawalin ƴan ta'adda da hukumomin tsaro suke nema ba dare ba rana bisa hannu a ayyukan fashi da garkuwa da mutane a Arewacin Nijeriya. An kama shi ne a yayin tantance maniyyatan, a wata motar 'bus' ta maniyyata da ta nufi filin jiragen sama, ranar Lahadi. Wata majiya ta…
