Babaji

5704 Posts

Tinubu ya ƙarfafa gwiwar jagororin rundunonin tsaro wajen kawo ķarshen ta’addanci

Daga BELLO A.BABAJI A cigaba da nuna kishin ƙasa da jajircewar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa, Shugaba Tinubu ya gana da shuwagabannin tsaro na ƙasar inda ya ƙarfafe su wajen kawo ƙarshen ta’addanci a Najeriya. Babban hafsan tsaro na ƙasa, Janar Christopher Gwabin Musa, ya bayyana cikakken rahoto bayan taron gaggawa da Shugaban Ƙasa ya jagoranta, inda manyan hafsoshin tsaro da sauran jami’an tsaro suka halarta. Janar Musa ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa na matuƙar damuwa da yadda barazanar tsaro ke ƙara ƙarfi, musamman sakamakon…
Read More

Gwamnatocin Tarayya da na jihohi da ķananan hukumomi sun raba tiriliyan N1.681 a Afrilu

Daga BELLO A.BABAJI Jimillar Naira tiriliyan 1.681 daga kudaden Harajin Asusun Tarayya na watan Afrilu ne aka raba a tsakanin Gwamnatin Tarayya, na jihohi da na ķananan hukumomi. An gudanar da rabon ne a taron watan Mayu na Kwamitin Asusun Tarayya (FAAC) a Abuja, ranar Juma'a. A sanarwar da Kakakin Kwamitin, Bawa Mokwa ya fitar, ya ce kuďin ya ķunshi wanda aka tattara daga harajin aiki (na ķa'ida) - biliyan N962.882 da na harajin VAT - biliyan N598.077 sai na harajin hadada, EMTL - biliyan N38,862 da kuma na banbance-banbancen kasuwanni (Exchange Difference) - biliyan N81.407. A wata takarda da…
Read More

Shugaba Tinubu ya gana da jagororin tsaro

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya yi ganawar sirri da jagororin sojoji da sufeton ƴan sanda a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja. Waɗanda suka halarci zaman sun haďa da Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa; Shugaban Sojojin ƙasa, Laftanal Janar Olufemi Oluyede; Shugaban Sojojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar; Shugaban Sojojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla; da Kayode Egbetokun, sufeton ƴan sanda. Ana ganin zaman ba zai rasa nasaba da sake farfaďowar ayyukan ta'addanci a wasu sassan Nijeriya musamman a shiyyar Arewa. An gudanar da zaman ne gabannin ziyarar Shugaba Tinubu zuwa taron kaddamar da sabon Fafaroma,…
Read More

Kano: An kama awakai bisa lalata bishiyoyi

Daga BELLO A. BABAJI Faruwar wani al'amari ya jefa al'umma cikin al'ajabi a Kano yayin da Ma'aikatar Kula da Muhalli da Sauyin Yanayi ta fara kamen awakan da ke lalata bishiyoyi, wanda hakan ke haifar da koma-baya ga ayyukan raya birane a jihar. Kwamishinan Ma'aikatar, Dakta Dahir M. Hashim ya tabbatar da hakan a wata takarda, ranar Juma'a, inda ya ce tuni aka kai wasu awakai ofishin rundunar ƴan sanda bayan sun lalata wasu bishiyoyi da aka shuka a wasu manyan tituna. Ya ce, a kokarinsu na raya birane, sun shuka bishiyoyi a manyan titunan ne domin rage matakin zafi…
Read More

Abinda ya sa ba za a soke TETFUND ba – Ministan Ilimi

Daga BELLO A.BABAJI Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana Asusun Tallafa wa Ilimin Manyan Makaratu (TETFUND), a matsayin babban ginshikin ci-gaban manyan makarantun Nijeriya, yana mai cewa ba za a soke shi ba daga cikin kudirin gyaran haraji. Ya bayyana hakan ne a Legas, yayin taron kwana ďaya na ganawa da jagororin makaratun, wanda TETFUND ta shirya, ranar Juma'a. Ministan ya kawar da fargabar da masu-ruwa-da-tsaki da dama ke yi na tunanin rushe TETFUND, inda ya ce Shugaba Bola Tinubu ya amince da karin kuďi ga asusun wanda daga ciki akwai harajin kaso 50. Ya ƙara da cewa, kokarin da…
Read More

Tinubu ya ƙaddamar da jiragen yaƙi biyu ga sojoji

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da jirage biyu masu tashin angulu na kai farmaki domin karfafa ayyukan dakile matsalolin rashin tsaro a Nijeriya. Taron kaddamarwar ya kuma yi daidai da cikar rundunar sojojin sama shekaru 61 da kafuwa, wanda aka gudanar a Abuja, inda Shugaban ƙasar ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima. An kaddamar da sabbin jiragen ne ga dakarun sojojin sama tare da sanya musu lambobin NAF544 da NAF545, waɗanda aka samar domin karfafa ayyukan sojojin a yaki da ta'addanci. Hakan wani bangare ne na habaka ayyukan sojoji da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen samar…
Read More

Filato: Sojoji sun kashe ƴan bindiga biyu a Wase

Daga BELLO A. BABAJI Dakarun atisayen Operation Safe Haven (OPSH) a Jihar Filato, sun halaka wasu mutun biyu da ake zargin ƴan bindiga ne a Gundumar Gimbi dake Karamar Hukumar Wase. Jami'in Hulďa da Jama'a na tawagar, Manjo Samson Zhakom ya faďi hakan a wata takarda da ya fitar a Jos, ranar Juma'a. Ya ce, an kashe mutane biyun ne bayan samun rahoton ayyukan ƴan bindiga a yankin. Manjo Zhakom ya kuma ce sojojin sun yi nasarar kwato wata bindiga kirar AK-47 a yayin atisayen. Ya kirayi al'ummar jihar da su cigaba da ba su goyon a kokarinsu na dakile…
Read More

‘Yan sanda sun kama barayin dabbobi da kwato shanu 273 a iyakar Kaduna da Neja

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sanda a Jihar Kaduna, ta yi nasarar kama barayin dabbobi guda biyu da kwato shanu 273 da ake zargin na wasu sanannun jagororin ƴan bindiga ne da ke ayyukansu a Kudancin jihar. Lamarin ya biyo bayan atisayen haďaka da aka gudanar tsakanin ƴan sanda da sojoji da ƴan bijilante, sakamakon samun bayanan sirri na sace dabbobi a Kananan Hukumomin Kauru, Kaura da Kachia a jihar. Bayanan sun nuna cewa, bayan sace dabbobin ne sai aka tafi da su yankin gabashin Akilibu da Dajin Rijana. A ranar 11 ga watan Mayu ne aka kama wani…
Read More

Kar ku damu da hare-haren ƴan ta’adda, mu na kula da al’amarin, inji Babban Hafsan Tsaron Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya ce sojoji da sauran hukumomin tsaro suna aiki tukuru wajen kawo karshen ta'addanci a Arewa maso Gabas sakamakon sake farfaďowar ayyukan tada kayar baya a shiyyar. Janar Musa ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno, ranar Alhamis. Ya ce, duk da cewa shi da ministan tsaro da sauran jagororin tsaro sun halarci Borno makonni kaďan da suka gabata, hakan bai sa ya yi ƙasa a gwiwa ba wajen sake dawowa da nufin duba matakin hare-haren da kokarin kawo…
Read More

JAMB: Majalisar Wakilai za ta binciki tsaikon da aka samu a jarrabawar 2025

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Laraba ne Majalisar Wakilai ta umarci a gudanar da bincike game da tsaikon da ya haifar da matsaloli a jarrabawar UTME ta shekarar 2025, wanda Hukumar JAMB ta gudanar. Majalisar ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa cibiyoyin rubuta jarrabawar (CBTs) a baki ďaya kananan hukumomin Nijeriya 774 don saukake hanyoyin jarrabawar ga ďalibai. A ranar Alhamis ne majalisar ta cimma matsayar a yayin zamanta, bayan da Hon. Adewale Adebayo (Osun) ya gabatar da kudirin. A ranar 9 ga watan Mayu ne JAMB ta fitar da sakamakon jarrabawar, wanda ya nuna…
Read More