16
May
Daga BELLO A. BABAJI Kotun Adalci ta ECOWAS, ta yanke hukuncin bada Naira miliyan 20 a matsayin kuďin dameji ga Mista Moses Abiodun, bayan tsare shi da aka yi na tsawon shekaru 16 ba tare da an gurfanar da shi ba. Mutumin ya maka Gwamnatin Tarayya ne a Kotun bisa zargin tauye hakki na ƴancin walwala da gurfanarwa da aka yi masa na tsawon lokacin. Mista Abiodun, ta hannun lauyansa, Chigozie Uzodinma, ya ce jami'ai na musamman kan lamuran fashi da makami (SARS), sun kama shi ne a watan Nuwamban 2008, inda suka tsare shi na tsawon watanni da dama.…
