13
May
Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Kula da Yanayi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WMO), ta yi gargaɗin cewa matsalolin ɗumamar yanayi da ayyukan ɗan-adam ke haifarwa, na haddasa aukuwar masifun da suka janyo ƙarancin abinci da ruwan sha, baya ga kassara tattalin arziƙin kasashe da dama a Nahiyar Afirka. A rahoton da ta wallafa a farkon makon nan, WMO ta ce masifun da ta ambata sun yi ƙamari ne a cikin shekarar 2024, inda a tsakanin watannin Maris da Mayu, ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa a dalilin saukar mamakon ruwan sama suka yi sanadin mutuwar ɗaruruwan mutane tare da wasu fiye…
