Gwamnatin Bauchi ta bada miliyan N95 ga iyalan waďanda harin ƴan bindiga ya shafa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Alhamis ne Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bada tallafin Naira miliyan 95 ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a yayin harin ƴan bindiga.

A kwanakin baya ne wasu ƴan bindiga suka kai hare-hare a kauyukan Duguri da Gwana dake Karamar Hukumar Alkaleri ta jihar, inda suka kashe wasu ƴan bijilante da fararen hula.

Gwmnan ya sanar da bata tallafin ne a lokacin ya je ziyarar ta’aziyya a yankunan, inda ya ce ƴan bijilante 13 da fararen hula 10 ne suka rasu a yayin farmakin.

Ya bayyana cewa, za a bai wa kowane ahali na ƴan bijilante da abin ya shafa miliyan N5 domin rage musu raďaďin rashin da suka same su, yayin da na sauran mutane goman kuma za a bai wa kowannensu miliyan N3.

Gwamnan ya ƙara da cewa, sama da ƴan ta’adda 60 ne suka rasa rayukansu a yayin fafatawa da jami’an tsaro da ƴan bijilante, yana mai yaba wa jajircewarsu wajen dakile ta’addancin maharan.

Bugu da kari, ya ce kungiyar ƴan bijilante za ta ďauki mutum 2,100 aiki kafin karshe shekerar nan, inda za a fara da mutum 300 zuwa 500.

Har’ilyau, gwamnan ya yi kira ga al’umma da su kasance a ankare da masu tsegumi ga bata-gari, waɗanda sun ma fi ƴan ta’addar haďari, ya na mai cewa wajibi ne a zakulo su domin su fuskanci hukuncin doka.

By Babaji