26
Apr
Daga BELLO A. BABAJI Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi watsi da batun cewa yana halin rashin lafiya ko kuma ya yanki jiki a wani taro. Ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke ƙoƙarin kafa sharuɗɗan sulhu da abokin hamayyarsa kuma dakataccen Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara. A yayin da ya ke magana a taron taya murnar zagayowar ranar haihuwar Hon. Ken Chikere a Fatakwal, Wike ya yi tsokaci game da matsalolin siyasar jihar, inda ya ce duk da cewa ƙofarsa a buɗe ta ke na yin sulhu, sai an samu dukkan ɓangarorin siyasar da lamarin ya shafa.…
