Babaji

5704 Posts

Kwara: Mahara sun sake kai farmaki da garkuwa da mutane da dama

Daga BELLO A. BABAJI Wasu ƴan bindiga sun farmaki wasu motoci biyu tare da yin garkuwa da matafiya a Ƙauyen Eleyin dake Ƙaramar Hukumar Isin a Jihar Kwara. Lamarin ya auku ne kwanaki kaɗan bayan aukuwar irinsa a kusa da garin Obbo-Aiyegunle na Karamar Hukumar Ekiti a jihar, wanda ya rutsa da matafiya bakwai da suka nufi Offa daga Abuja. A ranar Juma'a ne wasu mahara suka kai wani farmakin, inda suka tare wasu motoci biyu tare da yin garkuwa da ƴan cikinsu, waɗanda zuwa lokacin kammala haɗa rahoton, ba a samu bayanin hali ko inda suke ba. Kakakin rundunar…
Read More

Legas: NDLEA ta ƙwace miyagun ƙwayoyi na biliyan N1 a otal

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA, ta yi nasarar gano maɓoyar miyagun ƙwayoyi a wani otal mai ɗakuna 80, inda ta ƙwace na kimanin sama da Naira biliyan 1, a Victoria Island dake Jihar Legas a yayin wani samame. A tsakanin ranakun 25 da 26 na watan Afrilu ne lamarin ya auku a otal ɗin mai suna The Hook Hotel, wanda kuma ake kira da Caeser Hotel ko Caeser Lounge a lamba ta 16 dake layin Waziri Ibrahim. A sanarwar da Kakakin hukumar, Femi Babafemi ya fitar, ya ce jami'ansu a yayin samamen,…
Read More

Ku daina ɗora mana laifin gazawarku – Fadar Shugaban Ƙasa ga ƴan adawa

Daga BELLO A. BABAJI Fadar Shugaban Ƙasa ta yi kira ga ƴan ɓangaren adawa da su daina ɗora laifin gazawarsu ga Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Ta kuma bayyana cewa, demokraɗiyya tana nan daram a Nijeriya, babu wani yunƙuri na hana ƴancin siyasa ko wani yunƙuri na kafa jam’iyya ɗaya tilo a ƙasar. A wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan yaɗa labarai ya fitar, gwamnatin ta ce ƙorafe-ƙorafen da wasu ƴan adawa da masu kare haƙƙin ɗan-adam ke yi na cewa ana ƙoƙarin karya demokraɗiyya, batu ne da ba shi da tushe balle makama. Sanarwar…
Read More

DSS ta kama sojan Birtaniya da wasu ɗauke da muggan makamai a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Ƴan sandan Farin kaya ta DSS, ta yi nasarar ƙwato bindigu ƙirar AK47 guda 50 da alburusai sama da 3,000 da wasu muggan makamai a yayin wani atisaye na musamman a Asaba, Babban Birnin Jihar Delta. Haka kuma ta kama wani sojan ƙasar Birtaniya mai suna Itsekiri, wanda aka yi zargin sa da sayo makaman ga wani mai suna Collins. Shaidu daga DSS sun tabbatar da cewa, jami'an hukumar sun kama Major Itsekiri ne a matsayin asalin wanda ake zargi da wasu abokan tafiyarsa da hannu a shigowa da haramtattun makaman, ranar Juma'a. An kama…
Read More

Kusancin tsohon ɗan majalisa, Farouk Lawan da ƴan APC ya fara ɗaukar hankalin jama’a

Daga BELLO A. BABAJI Watanni kaɗan bayan fitowarsa daga gidan yari, an ga yadda tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Farouk Lawan kan halarci tarukan APC a ƴan kwanakin nan, lamarin da ya sa ake raɗe-raɗen akwai yiwuwar ya zama ɗan jam'iyyar nan ba da jimawa. Farouk Lawan ya wakilci mazaɓar Ɓagwai/Shanono ta Jihar Kano a majalisar daga shekarar 1999 zuwa 2015. An sako shi ne a watan Nuwamban shekarar 2024 bayan shafe shekaru biyar a kurkuku bisa tuhumar sa da laifin hannu a cin-hanci. Bayan haka ne ya bayyana cewa, a yanzu ne za a buɗe sabon babi game da harkokin…
Read More

Borno: Zulum ya sake kokawa bayan zargin ana ɗaukar nauyin mayaƙan Boko Haram da ISWAP daga waje

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya sake bayyana damuwa game da rahoton curewar mayaƙan Boko Haram da na ISWAP a yankin Tumbus dake Tafkin Chadi da Duwatsun Mandara a Dajin Sambisa dake jihar. Ya bayyana cewa, an samu koma-baya ta fuskar nasarorin da ake samu a ayyukan sojoji, a ƙoƙarinsu da daƙile ta'addanci a jihar, lamarin da ya sa ƴan ta'addar ɓangarorin biyu suke sake kafa daba a yankunan. Ya faɗi hakan ne a lokacin da Ministan Tsaro Badaru Abubakar da Babban Hafsan Tsaron Nijeriya CDS Janar Christopher Musa da wasu manyan kwamandodin soja a ziyarar…
Read More

Kacaniyar da mu ka sha lokacin da ni da wasu gwamnoni muka naɗa Sarkin Kano – Amaechi

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana yadda Ubangiji ya tsare shi a wata tafiya daga Kano zuwa Kaduna lokacin da ya ke gyangyaɗi a yayin tuƙi. Ya ce, lamarin ya faru ne bayan da shi da wasu sun kammala ƙaddamar da naɗin wani sarki a Kano da bai bayyana sunansa ba. Tsohon gwamnan na Jihar Ribas ya kuma ce, akwai Goje da Baraje da kuma Farfesa Gambari a lokacin da ya tuƙo motar daga Kano. Amaechi ya bayyana hakan ne a yayin taron Gidauniyar Akinjide Adeosun na shekara-shekara da ya gudana a Legas karo na…
Read More

JAMB za ta biya diyya ga ɗaliban da aka sauya wa gurin jarrabawar da ba su ne suka zaɓa ba

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Haɗaka ta Bada Gurbin Karatu (JAMB), ta ce za ta biya diyya ga dukkan wanda ya bada gamsassun hujjoji game da ɗaliban da aka tura su rubuta jarrabawa a wuraren da ba nan suka zaɓa ba. A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun jami'in hulɗa da jama'arta, Fabian Benjamin, hukumar ta ce wasu ɗalibai suna yaudarar iyayensu game da gurin da aka tura su, yayin da kuma jagororin makarantu suke zargin JAMB da tura ɗalibai guraren ba nan ne garuruwan da suka zaɓa ba a lokacin rajista. Babban jami'in ya ce, kowane ɗalibin…
Read More

Gwamnan Kano ya bankaɗo rarar miliyan N28 a albashin watan Maris

Daga BELLO A. BABAJI A ƙoƙarinta na tsaftace harkokin biyan albashi ga ma'aikatan Jihar Kano, Gwmantin Abba Kabir Yusuf, ta yi nasarar bankaɗo kimanin Naira miliyan 27,824,395 na albashin watan Maris, 2025. A ƙoƙarinsa na yin kwaskwarima ga tsarin biyan, Gwamna Abba ya kafa kwamitin sanya ido game da harkokin albashin ma'aikata a jihar. Kwamitin zai yi aiki ne kafaɗa-da-kafaɗa da sauran masu-ruwa-da-tsaki da suka shafi ɓangaren don tabbatar da gaskiya da adalci. Haka kuma zai sanya ido kan yadda ake biyan ma'aikata a ƙananan hukumomin jihar gami da daƙile ayyukan rashin gaskiya a yayin aiwatar da biyan albashi ga…
Read More

Real Madrid ta bayyana ƙwarin-gwiwa kan karawarta da Barcelona duk da ƙawa-zucin alƙalin wasa

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta bada amsa cikin fushi game da hira da aka yi da alƙalin wasan da zai yi alƙalanci a wasanta da ƙungiyar Barcelona na ranar Asabar, wanda ya fashe da kuka ganin yadda gidan talabijin na ƙungiyar ke matsa wa alƙalan wasa. Ƙungiyar ta musanta rahotannin da ke cewa ta na shirin ƙaurace wa buga wasan, wanda za a yi da misalin ƙarfe 9 na dare a birnin Seville. Ricardo de Burgos Bengoetxea shi ne wanda zai yi alƙalancin wasan, wanda kuma shi ne alƙali na ƙarshe da aka tattauna…
Read More