29
Apr
Daga BELLO A. BABAJI Kimanin mutane 15 ne ƴan ta'adda suka kashe a yayin wani zaman makoki da garkuwa da wasu a Ƙauyen Kwaple dake kusa da Ƙaramar Hukumar Chibok a Jihar Borno. Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar Litinin, a lokacin da ƴan zaman makokin suke jimamin rashin ɗaya daga cikin ƴan ƙauyen. A yayin tabbatar da lamarin, Ciyaman ɗin ƙaramar hukumar, Modu Mustapha ya ce maharan sun farmaki al'umma ne a lokacin zaman makokin inda suka kashe mutane da dama. Wani shaida da ya nemi a sakaye sunansa ya ce, aƙalla mutane 15…
