Babaji

5704 Posts

Gwamnonin Arewa maso Gabas za su kafa ofisoshin almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnonin jihohin Arewa maso Gabas da suka haɗa da na Adamawa, Gombe, Taraba, Yobe, Bauchi da Borno, sun amince da haɗa hannu da Hukumar Kula da Harkokin Almajirai da Ilimin yaran da ba sa zuwa Makaranta (NCAOOSCE) don samar da ofisoshi a kowacce jiha. An cimma matsayar hakan ne a yayin zaman gwamnonin a Damaturu, Babban Birnin Jihar Yobe, ranar Alhamis. Haka kuma sun amince da sanya almajirai da yaran a makarantun boko don su shiga sahun sauran yaran da ke zuwa makaranta. Ƙungiyar gwamnonin za ta yi hakan ne da haɗin-gwiwar NCAOOSCE ta yadda za…
Read More

Mu na buƙatar wata uku kafin bada rahoton binciken Tinubu – Hukumomin binciken Amurka ga kotu

Daga BELLO A. BABAJI Yayin da ake dakon fitar da sakamakon bincike na rahoton zargin Shugaba Bola Tinubu da ta'ammali da ƙwayoyi a shekarun 1990s, Cibiyar Bincike da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, wato FBI da DEA a Amurka, sun bayyana wa reshen Kotun Shiyya ta ƙasar Colombia dake Amurka cewa suna buƙatar a ƙara masu watanni uku domin kammala haɗa takardun rahoton. Hukumomi biyun sun bayyana hakan ne a wani saƙon haɗaka zuwa ga kotun tare da wanda ya shigar da ƙarar, wato Aaron Greenspan. Saidai, Greenspan ya ƙi amincewa da buƙatar, inda a madadin haka ya…
Read More

Hajjin 2025: Sahun farko zai tashi a ranar 9 ga Mayu, inji Shugaban NAHCON

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh, ya ce hukumar ta shirye tsaf wajen fara jigilar zangon farko na alhazan shekarar 2025. Za a fara ɗibar alhazan ne zuwa ƙasa mai tsarki a ranar 9 ga watan Mayu, 2025. Farfesa Saleh ya bayyana hakan ne a yayin wani zama da masu-ruwa-da-tsaki kan harkokin da suka shafi kula da tsare-tsaren kuɗaɗen mahajjatan da gudanarwasu. A gudanar da zaman ne, wanda NAHCON da Cibiyar kula da harkokin aikin hajjin Nijeriya da HIN gami da haɗin-gwiwar bankin Ja'iz suka shirya. Ya ce, Gwamnatin Tarayya ta zaɓi kamfanonin…
Read More

Gwamnatin Birtaniya ta barranta daga sojan da aka kama bisa safarar makamai a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Laraba ne Babbar Hukumar ƙasar Ingila ta ƙaryata rahoton da ke zargin wani jami'in soja daga cikin jami'an rundunar sojojinta ya na da hannu a sayen haramtattun makamai a Nijeriya. A wani saƙo da Kakakin hukumar ya fitar, ya ce mutumin da aka kama, ba ya aiki tare da rundunar sojojin ƙasar a halin yanzu. Rahotanni sun bayyana cewa, a baya ya kasance ya na aiki da reshe na biyu na rundunar a matsayin ƙaramin soja, kana daga bisani aka sallame shi. Sanarwar ta kuma ce, hukumar ba za ta bada ƙarin bayani game…
Read More

FBI da wasu hukumomi za su saki rahoton zargin ta’ammali da ƙwayoyi akan Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a, 2 ga watan Mayu, 2025 ne ake sa ran hukumomin gwamnatin Amurka da suka haɗa da Cibiyar Bincike ta FBI da DS da wasu za su fitar da rahoton zargin ta'ammali da ƙwayoyi akan Shugaba Bola Tinubu tun a shekarun 1990s. A farkon watan Afrilu ne kotun Amurka ta 'District' a madadin takwararta ta ƙasar Colombia ta umarci sauran hukumomin da ke da hannu a batun, ban da CIA, da su shirya baki ɗaya bayanan da ke da alaƙa da batun tare da fitar da rahotonsu a ranar 2 ga watan Mayu. Hakan…
Read More

Wulaƙanta Naira: E-Money ya magantu bayan EFCC ta sako shi

Daga BELLO A. BABAJI A yammacin ranar Talata ne Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta'annati, EFCC, ta sako shahararren tauraron nan na Legas, wato Emeka Okonkwo, wanda aka fi sani da E-Money, kwana ɗaya bayan kama shi. E-Money, wanda shahararren ɗan kasuwa ne, EFCC ta kama shi ne a gidansa dake yankin Omole na Jihar Legas a yammacin ranar Litinin sakamakon zarginsa da laifin wulaƙanta takardar Naira da wasu kuɗaɗen ƙasashen waje. Bayan sako shi ne ya sanar da al'umma ta kafar Instagram a daren Talata. Ya bayyana cewa, ya na cikin ƙoshin lafiya tare da miƙa godiyarsa…
Read More

Zargin badaƙala: EFCC ta gurfanar da Aisha Achimugu a kotu

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta'annati, EFCC, ta gurfanar da ƴar kasuwa A'isha Achimugu aka kotu, kamar yadda kotun ta umarta, ranar Laraba. Jami'ai mata biyu na hukumar ne suka shiga da ita kotun da misalin ƙarfe 11:35 na safe. Alƙali Iyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ya umarci matar, wadda ta fice daga Nijeriya da ta amsar gayyatar EFCC zuwa ƙarfe 12:00 na ranar Talata. Haka kuma ya umarci EFCC ta gurfanar da ita a ranar Laraba. Da asubahin ranar Talata ne jami'an EFCC suka kama Attajirar bayan isowarta Nijeriya.
Read More

NiMeT ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a faɗin Nijeriya ranar Laraba zuwa Juma’a

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa, NiMeT, ta yi hasashen samun hasken rana da hadari mai ɗauke da tsawa daga ranar Laraba zuwa Juma'a a sassan Nijeriya. A hasashen nata na ranar Talata, NiMeT ta yi nuni da cewa, za a samu hasken rana a ranar Laraba a yankin Arewa. Haka kuma, za a samu hadari da tsawa a lokutan rana da yamma a yankunan Jihohin Kaduna, Adamawa, Sakkwato, Kebbi, Zamfara da Taraba. A Jihohin Abuja, Benue, Kwara, Neja, Filato da Kogi kuwa, za a samu hadari da yiwuwar tsawa a lokacin rana da kuma yammaci.…
Read More

Yadda Aisha Achimugu ta ƙi cin abinci a hannun EFCC

Daga BELLO A. BABAJI Shahararriyar Attajira, A'isha Achimugu, ta ƙi amincewa da cin abinci a yayin da ta ke hannun jami'an Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta'annati, EFCC. A ranar Talata ne tawagar shari'arta ƙarƙarshin jagorancin Chikaosolu Ojukwu (SAN), ta sanar da cewa an kama Attajira Aisha ne da misalin ƙarfe 5 na asuba a Filin Jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja. Tun a watan Maris ne EFCC ta sanar da neman Attajirar ruwa-a-jallo sakamakon zargin ta da hannun a aikata manyan laifuka da suka haɗa da badaƙalar wasu kuɗaɗe. Haka kuma, Babbar Kotun Tarayya ta umarci…
Read More

NNPCL ya sallami manyan jami’an da suka yi aiki ƙarƙashin Mele Kyari

Daga BELLO A. BABAJI Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPCL ya sallami manyan jami'an da suka yi aiki tare da tsohon shugabansa, Mele Kyari. Daga cikin su akwai tsohon shugaban Hukumar Kula da zuba Hannun-jari a Man Fetur ta Ƙasa (NAPIMS) Bala Sunyi da Ibrahim Onoja, daraktan Matatar Kaduna da Lawal Sade. Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, aƙalla ma'aikata 200 lamarin ya shafa, wanda ke nuna yadda kamfanin ya yi gagarumin garambawul. Hakan ya kuma nuna yadda aka samu ƙarin adadi na mata da suka samu manyan muƙamai a kamfanin, waɗanda daga ciki akwai Maryam Idrisu a matsayin Darakta…
Read More