Babaji

5704 Posts

Minista Goronyo ya jagoranci bada ba’asi kan nasarorin gwamnati a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Ma'aikatar Ayyuka ta shirya zaman nazarin ayyukan da aka aiwatar a zangon farko na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, waɗanda aka cimma ƙaddamarwa a taron Majalisar Ayyuka ta Ƙasa karo na 29. An gudanar da taron ne na kwana uku a Gidan Gwamantin Jihar Nasarawa dake Lafiya, inda aka samu halartar manyan sakatarori da sauran masu-ruwa-da-tsaki kan harkokin ayyuka da sauran ababen more rayuwa domin nazarin nasarar da aka samu a ci-gaban samar da tituna a Nijeriya. Da ya ke jawabi, Kwamishinan Ayyuka, Gine-gine da Sufuri na jihar, Mu'azu Adamu Gosho ya yaba wa dukkan masu-ruwa-da-tsaki bisa…
Read More

Badaƙalar NNPC: Ana binciken Kyari yayin da aka kama jagororin matatun Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta'annati, EFCC, ta kama daraktoci da manyan jami'an da aka tsige a kwanan nan na kamfanonin matatun Fatakwal da Warri da kuma Kaduna. An yi hakan ne bisa zargin su da hannu s laifin sauya aƙalar wasu kuɗaɗe da aka ware domin gyaran matatun, waɗanda adadinsu ya kai Dala biliyan 2.9. Jaridar 'Newspoint Nigeria' ta ruwaito cewa, bincike ya nuna yadda EFCC ta ke binciken yadda aka sarrafa $1,559,239,084.36 da aka bai wa matatar Fatakwal da $740,669,600 da aka ware wa na Kaduna da kuma $656,963,938 ga na Warri.…
Read More

FUDMA: Farfesa Raɗɗa ya kai ƙorafin Ministan Ilimi bisa zargin son kai a ɗaukar sabon VC

Daga BELLO A BABAJI Wanda ke kan gaba wajen neman muƙamin mataimakin shugaban Jami'ar Tarayya ta Dutsinma (VC) dake Jihar Katsina, Farfesa Sadiq Raɗɗa, ya shigar da ƙorafi akan Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa bisa zargin sa da ƙoƙarin kitsa yadda za a cire sunansa daga cikin masu neman kujerar. Raɗɗa, wanda Farfesa ne a Tsangayar Nazarin Zamantakewa ta Jami'ar Bayero dake Kano, ya ce duk da cewa ya cike dukkanin ƙa'idodin da ake buƙata, amma an soke da dama daga cikinsu ba tare da wasu ƙwararan dalillai ba. Ya zargi VC mai barin gado, wato Farfesa Armaya'u Bichi da…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta bada wa’adi ga ƴan ƙasar waje da bizarsu ta ƙare

Daga BELLO A. BABAJI Gwmantin Nijeriya ta bai wa ƴan ƙasar waje da bizarsu ta ƙare wa'adin watanni uku su fice daga ƙasar. Jami'in hulɗa da jama'a na Hukumar Shige-da-Fice (NIS), Akinsola Akinlabi ta faɗi hakan a wata takarda, ranar Juma'a. Hukumar ta gargaɗe su da cewa, duk wanda aka samu da laifin zama sama da wa'adin da aka ba su, zai biya tarar Dala 15 da haramta sake shiga na tsawon shekaru biyar ko kuma na dindindin, hukuncin da zai fara aiki a watan Satumban 2025. Sannan, wa'adin zai ƙare ne a ƙarshen watan Agusta. Haka kuma takardar ta…
Read More

Gwamnan Bauchi ya yi jimamin kisan tsohon ciyaman na Jama’are da umartar a yi bincike

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Jihar Bauchi da al'ummarta sun koka game da kisan tsohon shugaban Ƙaramar Hukumar Jama'are, Alhaji Isa Muhammad Wabi. Binciken ƴan sanda ya nuna cewa, wasu abokan ɗansa ne suka farmake shi ne a gidansa dake unguwar Fadaman Mada a garin Bauchi. A wata takarda da Mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Giɗaɗo ya fitar, Gwamna Bala Muhammad ya jajenta wa iyalan mamacin da al'ummar Masarautar Jama'are da sauran waɗanda alkhairansa suka kai gare su. Ya kuma bayyana kaɗuwarsa game da aukuwar lamarin tare da umartar hukumar ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro…
Read More

Bauchi: Ana zargin abokan ɗan tsohon ciyaman da hannu a kashe shi

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon Ciyaman na Ƙaramar Hukumar Jama'are dake Jihar Bauchi, Isa Muhammad Wabi ya rasa ransa a lokacin da wasu ƴan bindiga suka farmake shi a gidansa, inda ake zargin abokan ɗaya daga cikin ƴaƴansa, wato, Abdulgaffar mai shekaru 24 da hannu a kisan. Rundunar ƴan sandan jihar, sun tabbatar da aukuwar lamarin a yayin da suka samu labarin harin da wasu matasa suka kai a unguwar Fadaman Mada a garin Bauchi, kamar yadda Kakakinta, CSP Ahmed Wakil ya bayyana a wata takarda. Ya ce, sun samu tsohon Ciyaman ɗin, mai shekaru 66 a mawuyacin hali sakamakon…
Read More

Seyi Tinubu ya musanta tayin cin-hanci, garkuwa da sa a doki Shugaban NANS

Daga BELLO A. BABAJI Ɗan Shugaba Bola Tinubu, wato Seyi Tinubu, ya ƙaryata zargin da Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya (NANS), Kwamared Atiku Abubakar Isah ya yi akansa, inda ya ce an yi haka ne da nufin ɓata masa suna. Seyi Tinubu ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa ta kafar Instagram inda cikin mamaki ya ce bai taɓa tattauna wani batu da shi ba a Legas ko ko'ina a duniya. Ya kuma ce, bai taɓa haɗuwa da shi ba, kamar yadda bai taɓa zuwa wani waje da ƴan daba ba. Ya ƙara da cewa, baki ɗaya zarge-zargen…
Read More

An kashe tsohon ciyaman a Bauchi

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Alhamis ne ƴan bindiga suka farmaki gidan tsohon Ciyaman ɗin Ƙaramar Hukumar Jama'are, Hon. Isah Muhammad a Jihar Bauchi, inda da kashe shi a unguwar Fadaman Mada dake garin Bauchi. Wata majiya ta ce, maharan sun je gidan tsohon shugaban ƙaramar hukumar ne, wanda aka sani da Ɗan Galadiman Jama'are, inda suka rufe gidan sannan suka kashe shi a ciki. Haka kuma, an raunata ƴaƴansa biyu a yayin aukuwar lamarin, waɗanda a yanzu suna wani asibiti a Bauchi domin karɓar magani, kamar yadda WikkiTimes ta ruwaito daga Zamani TV. Marigayin ya kasance ɗaya ne…
Read More

NIMC ta ƙara kuɗin yin rajistirar NIN

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Alhamis ne Hukumar Samar da Katin ɗan ƙasa, NIMC ta sauya tsarin farashin gudanarwarta bayan shekaru goma, lamarin da ya shafi kuɗin rajistar samun lambar ɗan ƙasa, wato NIN. Babban jami'in hulɗa da jama'arta, Dakta Kayode Adejoke ya bayyana hakan a wata takarda, inda ya ce an yi sauyin ne don ya dace da farashin gudanarwa na wannan zamanin. Haka kuma, hukuncin zai taimaka wajen samar da kati mai nagarta ga ƴan ƙasa da tabbatar da farashi mai sauƙi a gare su. Dakta Adejoke ya ƙara da cewa, za a fara aiki da sabon…
Read More

Shugaban NANS ya zargi Seyi Tinubu da sa ƴan daba su yi masa duka bisa ƙin karɓar cin hancin miliyan N100

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya (NANS), Atiku Abubakar Isah, ya zargi ɗan Shugaba Bola Tinubu, wato Seyi Tinubu da aika wasu ƴan daba su yi masa dukan kawo-wuƙa saboda ya ƙi amincewa da karɓar cin-hancin Naira miliyan 100. Isah, wanda aka zaɓe shi a yayin taron ƙungiyar da aka yi a ranar 27 ga watan Fabrairu, ya yi zargin cewa Seyi ya zo wajen rantsar da shi a Abuja, ranar Talata, inda ya yi ƙoƙarin hargitsa wajen tare da yi wa rayuwarsa barazana. Ya kuma ce, ɗan shugaban ƙasar ya je otal ɗin da aka yi taron…
Read More