05
May
Daga BELLO A. BABAJI Shugaban rukunin Kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce har yanzu matatarsu ta Dala biliyan 20 tana fuskantar ƙalubale a yayin da ta ke ƙoƙarin gudanar da harkokinta cikin salama. Ya ce, a shirye ya ke wajen faɗa da duk wani yunƙuri na kai matatar ƙasa. Shahararren Attajirin na Afrika ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da tawagar masu zuba jari a Legas, ƙarshen mako. Ɗangote ya bayyana cewa, waɗanda suka samu kuɗi wajen shigo da mai Nijeriya a tsawon lokaci, sune waɗanda ke shirya wa matatar maƙarƙashiya. Ya kuma ce, sune suka taimaka wa…
