07
May
Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Jihar Bauchi ta yanke korar baki ɗaya jami'an da ke kula da harkokin gudanar da makarantu (SSOs) a Ƙaramar Hukumar Bauchi bisa sakaci wajen tsare ayyukansu. Shugaban Hukumar Ilimin Bai-ɗaya na jihar (SUBEB), Alhaji Adamu Muhammad Duguri ya bayyana hakan jim-kaɗan bayan gudanar da zagayen ba-zata a makarantun gwamnati dake babban birnin. Ya ce, hukuncin ya zama wajibi ne a lokacin da suka gano cewa jami'an da lamarin ya shafa ba sa gudanar da ayyukansu yadda ya dace. Ya bayyana cewa, aikin da aka ba su shine su sanya ido game da harkokin makarantun kuma…
